Wuraren Da Ake Zaton Damakwaraɗiyya Ta Yi Kama Da Musulunci

0
18

Akwai wurare uku a cikin damakwaraɗiyya waɗanda suka sa wasu suke kamanta ta da Musulunci, amma a haƙiƙanin lamari sun sha bamban.

  1. Majalisun Dokoki Ba Shura Ba Ne: 

A siyasar Musulunci akwai abinda ake kira Majalisar shura wadda wasu suke daidaita tada majalisar dokoki. To a gaskiyar lamari ita Damakwaraɗiyya babu tsarin Shura a cikinta, (Democracy is NOT Shura). Saboda: 

  1. a) A tsarin Shura ba a tattauna abin da Allah ya yanke hukunci a kansa. 
  2. b) A tsarin Shura shawarar da majalisa ta yanke ba ta zama dole ga shugaba ya yi aiki da ita. Domin Shawara aka ba shi. Ba doka ba. 
  3. c) A tsarin Shura ana naɗa mutane ne masu suffofi kamar haka: (i) Musulmi 

(ii) Masu cikakken hankali 

(iii) Masu ilimin addini 

(iv) Ko masu ƙwarewa a wata harka ta rayuwa 

(v) Masu kyawawan halaye. Watau su zamo adalai ba fasiƙai ba. 2. Jefa Kuri”a Ba Mubaya’a Ba Ne: 

Domin karanta bayani akan Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauki Danna nan

A siyasar Musulunci akwai abinda ake kira mubaya’a, shi ne bayan nagartattun mutane sun zaɓi shugaba sai sauran mutane su dinga zuwa suna nuna yardarsu gare shi. Don haka Jefa ƙuri’a ba daidai yake da “mubaya`a ba, ta fuskoki kamar haka: 

  1. a) A zaɓen jefa ƙuri’a mutum fiye da ɗaya ne suke tsayawa. Ita kuwa mubaya’a shugaba ake yi wa, bayan an zaɓe shi. 
  2. b) Shi zaɓe hanya ce ta ɗarewa muƙamai daban-daban. Ita kuwa mubaya’a sai shugaban al’uma gaba ɗaya ake yi wa. 
  3. c) Shi zaɓen jefa ƙuri’a na kowa da kowa ne, ita kuwa nagartattu ake neman su yi, ba kowa da kowa ba. Sai sun yi, san nan sauran jama’a su yi mubaya’a.
  4. d) A tsarin jefa ƙuri’a mutum fiye da ɗaya suna iya cin zaɓ Ita kuwa ‘mubaya’ a da ma mutum ɗaya ake yi wa. 

Yadda mutane fiye da ɗaya za su ci zaɓe da ƙuri’a ɗaya a tsarin damakwarɗdiyya shi ne, a zaɓen ‘yan majalisar dattijai a Najeriya, kowa ƙuri’a ɗaya zai jefa, amma a zaɓi dukkanin yan majalisar dattijai da ita. 

  1. Yancin Damakwaraɗiyya Ba Yanci Ba Ne: 

Damakwaraɗiyya tana bai wa ɗan Adam ‘yanci na ƙarya, mai mummunar manufa (Wrong Meaning in the Use of Freedom). 

A Musulunci akwai ‘yanci. Mutum yana da ‘yancin ya rayu. Yana da ‘yancin a kare masa dukiyarsa. Yana da ‘yancin a kare masa mutuncinsa, da sauransu. Amma shi ‘yancin damakwaraɗiyya manufarsa, a mafi yawan lokuta shi ne, nuna wa ɗan Adam yana da `yancin ya saɓa wa dokokin Allah (Subahanahu Wata’ala). Misali: 

Domin karanta tarihin damokuraɗiyya a Najeriya danna nan

Yancin tunani. Watau mutum zai iya zaɓar tunani wanda zai bauta wa, komai ƙasƙancinsa. Ko da kuwa kare ne ko jaki ko ƙabarin wani, kai ko da najasar wani ya zaɓi ya bauta wa, za a ba shi wannan ‘yancin. 

Yancin zaɓin dokar da mutane suka ga dama. Za su iya cewa, ba za a yanke hannun ɓarawo ba. Zina ba laifi ba ce, sai in ta zama fyaɗe. Auren jinsi halal ne, da sauransu. 

Mu sani cewa tunanin ɗan’dam yana da iyaka. Ba zai gano masa komai da Komai ba. Allah (SubahanahuWata’ala) yana nuna mana cewa ‘yancinmu yana da iyaka. Don haka kada mu wuce dokokin Allah. Inda yake cewa: 

“Waɗannan dokokin Allah ne, kada ku ƙetare su. Wanda duk ya ƙetare iyakokin Allah waɗannan su ne azzalumai (Suratul Baƙarah, aya ta: 229). 

Watau sun zalunci kansu. Kuma idan muka duba za mu ga a can inda damakwaraɗiyyar ta fito, ‘yancin ba a sake yake ba a wajen su. Misali: 

Mutum ba zai yi tusa a cikin jama’a ba, saboda da’awar ‘yanci. Ba su yarda

yana da wannan ‘yancin ba. 

  • Mutum bai isa ya tuƙa abin hawansa ta inda wasu suke tawowa ba, domin taƙamar ‘yanci. Da yake ita wannan dokarsu ce, ba ta Allah ba. Kuma sun gane za su cutu. 
  • Mutum bai isa ya yi gini a gidansa ba tare da ya nemi izini ba, idan aka tambaye shi ya ce yana da ‘yanci. 
  • Duk da cewa mace tana da ‘yancin ta sa kayan da take so, waɗanda suka saɓa wa dokokin Allah, amma ba ta isa ta sa kayan yin wanka a bakin ruwa, ta je gidan makoki da su ba. 

Ashe ke nan ma’anar yancin shi ne a saɓa wa dokokin Allah. Auren mace fiye da ɗaya haramun ne, amma yin zina da mace fiye da ɗaya halal ne. Yin fyaɗe haramun ne, amma yın zina da mace ko guda nawa ce ya halatta, in dai da yardarta. Da sauransu. 

Domin karanta cikekken littafin  Danna nan 
labarin da ya wuceShin Damakwaraɗiyya Musulunci Ce?
Labarin na GabaAibukan Damakwaraɗiyya Guda Ashirin Da Ɗaya (21) A Mahangar Musulunci