Allahu Wahabu mai komai, Mai sa zaki ya kar birrai, Mai sa kuturu ya hau jakai, Mai bai wa mutum sanin ilimai, Karimu, Wahabu mai komai.
-
Sa’a na rika a tun farko,
- Ka ban ilimin mutan farko,
- A waka kar na zam soko,
- Ka ban hikima na sa saƙo,
- A gari, birni da duk loko.
- ————————-
- Ku biyo ni ki ji ni baitoci,
- Na tsara batu na lakcoci,
- A Gadau ta Jiharmu can Bauci,
- Garin da na je a motoci,
- ————————
- Na je ni Shira na je Zaki,
- Na je ni Gaɗau da ba gunki,
- A nan na zamo ya ɗan zaki,
- Jama’are na je cikin tuƙi,
- Na kwan Azare cikin ɗaki.
- —————————-
- Mu ɗan koma batun na Shira,
- Garin dutse garin Gora, kara;
- Rumfa, Dutsen Gabas a Shira,
- Ruwan ƙirci akwai a Shira,
- Kare, Margi, Habe a Shira.
- —————————–
- Wata ran a Guru na tasowa,
- Na je ni Bade garin Gashuwa
- A Potiskum ban yi hutawa,
- Sai ga ni Bagauda yan mowa,
- Bulkachuwa ma na gotawa.
- ——————————
- Tafiya daɗi cikin mota,
- Bulkacuwa nan na dan gota,
- Damban na wuce ina mota,
- Zan je ni Gaɗau garin tsafta,
- Na shige Azare a kan kwalta.
- ——————————
- Na je ni Gamawa yan barka,
- Garin Shehin da bai shirka,
- Ɗan Sa’idu Ali na gaishe ka,
- Sakwa a garin da babu
- Allah ya saka ku kere haka.
- ——————————
- Na gode wahabu mai khairi,
- Da ya ban ilmin da ba sharri,
- Abun ga uku cikin jeri,
- Na yi su ku ji su ba kuri,
- Certificate two abin fahari.
- ——————————-
- Masters kuwa gefe can na shiga,
- Tinƙis-tinƙis ina ta buga,
- Karatu babu yin burga,
- Ga aiki ga yawan sabga,
- Allah ya nufa na kere duga.
domin samun karanta cikkakken littafin danna koren rubutu.