An karɓo daga Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu); ya ce da ‘yar uwarsa Zainab lokacin da ya ga tana marin kumatunta za ta yaga tufafinta ta faɗi za ta suma, sai ya ce:
“Ya ke ‘yar uwata, kiji tsoron Allah, kiyi haƙuri, ki sani halittun ƙasa za su mutu; na sama ba za su wanzu ba, babu abinda zai saura sai Allah; wanda shi ne ya halicci halittu da Ikonsa; shi ne makaɗaici sani mahaifina ya fi daraja, haka Kuma mahaifiyata, haka ɗan uwa na (Hassan); kuma ni da duk wani musulmi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne abin koyin mu”.
Sannan ya ci gaba da cewa: “ya ke ‘yar uwata na yi rantsuwa kada ki karya min rantsuwa ta, idan na mutu, kada ki yaga tufafinki, kada ki yakushe fuskarki, kada kiyimin kururuwa!“
To ɗan uwa ka ji da kansa abinda ya yi umarni, kuma har da rantsuwa kamar ya san a rina…; to don Allah waɗannan koke-koke da dukan jiki har ma da kisan kai a wasu lokuta; daga ina aka samo su?
Domin karanta cikakken bayani a kan Matsayin Koke-Koke Da Kururuwa danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Kukan Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.