Zamani ya yi matuƙar tasiri a wasan ƙunshi. Idan muka dubi shi kansa wannan wasa, za mu ga a ɓangaren da ake amfani da Tufafin da suke amfani da su a lokacin wasan akwai; atamfofi da shaddodi da leshe-leshe da boyal-boyal da wagambari da (material) da yaduka kala-kala da dogayen riguna da hijabai da niƙabai da mayafai da kayan ƙyale-ƙyale.
Ana yin ɗinkuna iri daban-daban, waɗanda masu aiwatar da wasan ƙunshi suke amfani da su a lokacin aiwatar da wasan. Masu aiwatar da wasan ƙunshi, a yau sukan yi ado da kwalliya a ranakun wasan, ba kamar yadda ake gudanar da shi a baya ba, tun daga ranar farko har zuwa ranar ƙarshe, daga kan sarƙoƙi da ‘yankunnaye da roses da awarwaraye da zobuna da barima, da agogo da ribas da jakankuna, har ma da tabarau.
Bugu da ƙari, suna amfani da kayayyakin irin su; mayukan shafawa iri daban-daban, da turare, da jambaki, da hoda barbaɗa-kumatu, fiƙe-hanci, da ataciman da yin ƙunshi, na zamani wato fulawoyi, kala-kala, a hannu da ƙafa.
Haka wasan ƙunshi a wannan lokaci ya tasirantu musamman masu aiwatar da wasan suna yin amfani kayan kaɗe-kaɗe da waƙoƙin na zamani, inda suke amfani da mp da bluetoot da rikoda da sauransu, wajen sanya waƙoƙi iri daban da daban. Suna amfani da su ne musamman wajen ƙara armashin wasan haɗi da nishaɗantarwa.
A yau, an samu wadatuwar wasu hanyoyin fasahar sadarwa na zamani, wasu daga cikin su sun haɗa da wayoyin tafi da gidanka ko kuma wasu suce wayoyin hannu da computer suna taimakawa matuƙa gaya wajen aiwatar da wasan, a na ɗaukar hotuna da turawa saƙonnin kar ta kwana ta amfani da fasahar sadarwa da suka haɗa da instgram da facebook da tiktok da sauransu.
Ana tura yadda wasan ke gudanar wasu kai tsaye ga ‘yan uwa da abokanan arziƙi zuwa ga waɗanda basu sami damar halartar wasan ba,ta hanyar tura musu saƙonnin ciki da wajen ƙasar nan, kamar Ghana da Kamaru da Saudi Arabiya da Mali da sauran sassan ƙasahen duniya. Sannan kuma sukan ɗauki yadda ake gudanar da wasan kai tsaye tare da yin jawabi wasan yake kasancewa tamkar kamar yadda ake aiwatar a nan take.
Haƙiƙa a yau, an samu sauye-sauye, musamman a ɓangaren addini a domin yaran da ba sa cika azumi ko kuma basa yin sa, da yin sallah a lokacin da ya dace da sauran abubuwan da suka shafi addini. A yau abin ba haka yake ba. Masu aiwatar da wasan suna tafiyar da harkokin addinisu kamar yadda shari’ar musulunci ta sharaɗanta kamar yin azuminsu ba tare da ƙin yi ba ko kuma karya shi, haka ma suna aiwatar da sallah a lokacin da ake gudanar da ita, da sauran abubuwan da suka shafi addini. Sai dai idan da (akwai dalili na rashin yin hakan musamman mai lalura (‘yan mata).
Sannan kuma wasan a yau, yana kan hanyar dusashewa, saboda sauye-sauyen zamani, kamar ta fuskar addinin musulunci, karatun boko da sauransu. Wasu a waɗannan ranaku suna zuwa dai ranar da ake karatun makarantar allo da makarantar islamiya da kuma makarantar boko, wanda sun taimaka wajen rage kaifin aiwatar da wasan kamar yadda ake aiwatarwa a baya.
Sannan kuma a sakamakon a yau babu wadatattun filayen wasanni, wannan shi ma ya taimaka gaya wajen koma bayan aiwatar da wasan ƙunshi. A yau filaye sun yi ƙaranci babu wadatattu wasu an yi gine ginen gidaje, yayin da wasu kuma gwamnati ta yi wasu abubuwan na ci gaban al’umma.
Haka nan, ta fuskar tsaro a wannan lokaci ba iya samun damar wasan ya kai wani lokaci mai tsaho ana gudanarwa kamar a baya, wannan yana faruwa a ‘yan shekarun nan sakamakon rashin wadataccen tsaro, wanda a yau ƙasar Hausa a wannan lokaci take fuskanta. Wannan ya taimaka a yau iyayen yara basa barin ‘ya’yansu sukai wani dogon lokaci suna aiwatar da wasan kamar yadda ya kamata.
Wanan bayanin an ciro shine daga maƙala mai taken Nazarin Wasan Ƙunshi Jiya Da Yau A Ƙasar Gaya wadda Magaji Ahmad Gaya Ph.D Sashen koyar da Hausa Jami’ar Northwest, Kano ya wallafa.
Emai: magaya@nwu.edu.ng
08066009039
Danna nan don karanta Yadda ake Gudanar da Wasan Ƙunshi
Edita@rumasau-kallamu










