Ɗalibi a matakin digiri na biyu, Sashen Harsuna, Jami’ar Jihar Bauchi. Malami mai aikin Hidimar Ƙasa, Sashen Nazarin Harshen Hausa, Kwalejin Addinin Musulunci da Sharia ta Aminu Kano, Jihar Kano.
Wadda aka gabatar a taron bikin taya Farfesa Abdulƙadir ɗangambo murnar samun Emiratus farfesa a ranar Lahadi 14/07/2019, A Ɗakin Taro na American Corner dake Laburaren Jihar Kano
- Sallama gare ku karin fari,
- Godiya ga Allah mai khairi,
- Allah ban basira nai ƙudiri,
- Nai yabon ƙwararren mai nazari,
- Ɗangambo Baban nan nagari.
- —————————
- Gaisuwa ga Ɗaha miji nagari,
- Shugaba a duniya har kabari,
- Bin Sa babu zancen bin garari,
- In ka gane son sa fa ka ci gari,
- Lalle fa ni kam nai katari.
- ————————–
- Manzo na Allah ɗa nagari,
- Sahibansa, matayen khairi,
- Har da ‘ya’ya masu gudun garari,
- Sanya tabi’an nan masu gari,
- Ka daɗo aminci mai sukari.
- —————————–
- Gani nan da waƙa ba fahari,
- Har na tsara baiti ku yo nazari,
- Babu batsa ko zancen sharri,
- Don yabon Ubanmu da bai kuri,
- Wanda bai wa al’umma sharri.
- ———————————
- Ana na gaishe ku tun da wuri,
- Taron da kun shirya don fahari,
- Na tayo Ubanmu Uba nagari,
- Murnar Emiratus mun fahari,
- A Kano muna nan muna zikiri.
- ———————————
- Duk garin da babu sani da ɓari,
- Ilimi fa gyara ne na gari,
- In akwai gidanku fa kun ci gari,
- In ka ba da ka zarce sukari,
- Kai batun ga sai mai kyan ƙuduri
- —————————-
- Rayuwar karatu ba garari,
- Mai biɗarsa shi ne ɗa nagari,
- Malami ko shi ne uba nagari,
- Samuwarsa dole a yo fahari.
- Ɗangambo lalle ka ci gari.
- —————————–
- Rikicin Fulani ƙona gari,
- Rigimar fatake ce gagari,
- Rigar mutunci ce fahari,
- Riƙi gaskiya ka zamo nagari,
- Riƙi ɗa na Gambo ka zarce gari.
- ——————————–
- In ka nemi maciji ka je shuri,
- Shi Ɓarawo sa shi cikin fa mari,
- Kankana tana kayan marari,
- Ɗangamo sa shi cikin nagari.
- Ni ko sai ka je layin nazari.
- —————————
- Malami jakadan alheri,
- Rayuwarsa bai ƙullo sharri,
- Mutuwarsa ke sa ai garari,
- Wanzuwar sa ke kawo sarari
- Ɗangambo kanka mu yo fahari.
- —————————–
- In ka kalli B.U.K nazari,
- Ɗalibanta duk sun yo katari,
- Sun naƙalci harshe ba fahari,
- Lugatan da Turanci a gari,
- Ga biyayya gunsu cikar fahari.
- ——————————–
- Ɗangambo fannunu ne nazari,
- Ɗalibansa sun zamto ƙwari,
- Fannukansu sun san duk lamari,
- Ba su birki balle a yo turi,
- Ba su yi wa kowa alfahari.
- ——————————
- In ka je gari aka ma fahari,
- Kar ka damu lura ka yo nazari,
- Ƙila babu Malam a wanga gari,
- Je ka sashikan Hausar nazari,
- Ba rabo da kai ba shiga haɗari
- ——————————–
- Ɗangambo ka zarce zuma maɗari,
- Wane farin can wai sukari,
- Ka yi taka kai ta rago a gari,
- Ka faranta rayin masu gari,
- Zuciyarsu ta zamto fa fari.
- ——————————-
- Baban Samira uwar nazari,
- Na gaida Dakta da ba ta ɓari,
- Ma’ana Halima dake nazari,
- Harshe na Hausa yana fahari
- Da ke da Abbanmu masu gari.
- ——————————-
- Manyan furofesa sun nazari,
- Sun koyi Adab da kyau da wuri,
- Dakta da masters sun yo nazari,
- Sun zarce hamsin wane fa ɗari,
- Lalle gwanin namu ka ci gari.
- ——————————-
- Na san ka tun kan na zo ni gari,
- Sanadin karatunka nai nazari,
- A rubutukanka na yo nazari,
- Na nazarci waƙa, adab da kari,
- Har ma da ƙage na labari.
- ——————————-
- Ni Nayaya na yo alfahari,
- Na zamo cikin ‘ya’ya tari,
- Wanda sun ka yo wannan katari,
- Sun ka yo rubutu mai fahari,
- Don na waƙe Ɗangambo a gari.
- ——————————-
- Zan taƙaita kan waƙar sukari,
- Kai! Maɗi fa zance ba kuri,
- G. Nayaya uban nazari,
- Suna gare ni a wanga gari,
- Nguru a ce tammat khairi.
domin samun karanta waƙar gargajiya danna koren rubutu