Waƙar Yabon Manzon Allah(S.A.W).

0
1020

Domin  shiga gasar mawaƙa wadda ƙungiyar gamayyar marubuta da yadda manazarta waƙoƙin Hausa ta ƙasa, ta saka a ƙarshen shekarar  2018 zuwa farkon  2019.

 

 • Allah na roƘa cikin ɗa’a,
 • A baitukan nan da babu ba’a,
 • Allah na ɗaro daɗin sa’a,
 • A baitukan nan da ba bidi’a,
 • Albarka sa min na ɗau ƙuri’a.
 • —————————–
 • Na yo salati ga Manzona,
 • Na Khadija, Hafsat, Uban Nana,
 • Na Sadiƙu, Umar, Usumana,
 • Na Aliyu zaki kisan arna,
 • Na Mu’awiyya sahihin ƙima
 • ————————–
 • Zuma farar gani farar saƙa,
 • Na ƙulla baiti cikin waƙa,
 • Na tsara ɗango cikin sarƙa,
 • Domin yabon Ɗaha kun ji haka,
 • In ka bi Manzonmu ka fi haka.
 • ——————————-
 • Kyawun ɗabi’unsa sun fi ɗari,
 • Kufurun, musulmanmu sun nazari,
 • Zama da Manzon fa ba haɗari,
 • Rayuwa a tsarinsa ba garari,
 • In ka bi Manzonmu ka ci gari.
 • ——————————–
 • An haifi Manzo a Makkiya,
 • Ran Litinin sha biyun ku jiya,
 • Auwal Rabiyun na ɗan juya,
 • Shekara ta giwa a Habshiyya,
 • Islam kalanda ta Hijriyya.
 • —————————-
 • Nasabar Mahaifinsa Abdallah,
 • Abdulmuɗallib cikin jumla,
 • Haashim fa Kaka ga Abdallah,
 • Abdulmanaf ɗan Ƙusai Allah,
 • Ya sa Kilab don cikar falala.
 • ——————————
 • Umminsa Babba Aminattu,
 • Yar Wahab, Manafi, Zuhuratu,
 • Sun haɗe a Kaka taƙaita batu,
 • Na biyar Kilab sai ku gane batu,
 • Sirarsa Manzon da bai shantu.
 • ———————————
 • Matansa sha ɗai na lobayya,
 • Khadija farkonsu kun ji ɗaya,
 • Assha da Hafsat suna baya,
 • Ummu Habiba da Salmayya,
 • Hindattu, Saudat ba sa ƙarya
 • —————————-
 • Sai Zai nabu bintu Jahshiyya,
 • Maimunatu bintu Harisiyya,
 • Zainab Khuzaima na jerayya,
 • Sai kam ta ƙarshe Juwairiyya,
 • Matansa cif-cif da sha ɗay
 • —————————-
 • ‘Ya’yanSa bakkwai cikar sunna,
 • Ibrahim a farko mai suna,
 • Abdallah, Ƙasim da ba su tsana,
 • Fatima, Kulsum cikar ƙauna,
 • Ruƙay da Zainab cikon juna.
 • ——————————
 • Manzo yana nan da mu’ujiziyya,
 • Ƙur’an da ba wasa ba ƙarya,
 • Tatsuniyar nan ta yan zolaya,
 • Ba shirme danniyar nan ku jiya,
 • Halinsa ne kun ji khairiyya.
 • ——————————
 • Halinsa Manzo cikar kunya,
 • Nutsuwarsa Manzo a taffiya,
 • Maganarsa ƙamshi yake zirya,
 • Dattijo ne mai halin manya,
 • Ƙur’an dalilinsa baki ɗaya
 • —————————
 • Dini na Manzo da ba ƙarya,
 • Ba yaudara ko kisan hanya,
 • Shi gaskiya ce zancensa ɗaya,
 • Dinin da Shaiɗan yake baya,
 • Ba ya kusantarsa don kariya.
 • ——————————-
 • Islam ya kawo a Makkiya,
 • Ya ƙira Ƙuraishi su bar ƙarya,
 • Sata da shirka da camfiyya,
 • Da kisa na juna da shirya tsiya,
 • Su riƙe ƙiran nan na kimtsiyya.
 • ——————————-
 • Rukunai shida ne na Addini,
 • Zan ambato su ku ɗan ji ni,
 • Kalma ta farko shahadataini,
 • Sallah, Azum, Zakka ba raini,
 • Hajji a ƙarshe ga mai sukuni.
 • ——————————-
 • Iman ku gane ajinsa shida,
 • Iman da Allah, Mala’iku da;
 • Littattafan nan na aƙida,
 • Manzanni, Lahira kui shaida,
 • Ƙaddar fa wajib cikon na shida.
 • ——————————-
 • Ya yaƙi arna cikin sa’a,
 • Ya rusa daular da ba ɗa’a,
 • Ya ce gumaka mu yo bara’a,
 • Kisa na juna mu bar bidi’a,
 • Kushe da juna mu bar ta ba’a.
 • ——————————
 • Yaƙi talatin na yo nazari,
 • Ya yo su ba ɗai Ya buɗe gari,
 • Islam ya zamto cikin fahari,
 • Kufurun suna can suna garari,
 • Aljanna ce duk cikar guzuri.
 • ——————————-
 • Daula ta zamto ta Islama,
 • Kowa ya zamto cikin hidima,
 • So, taimakon juna ba ƙyama,
 • Ba soke-soke da yin gulma,
 • Cab! Kun ji hanyar mutan ƙ
 • —————————–
 • Zan dakata zana sa birki,
 • Tamkar fa mota a kan tuƙi,
 • Nayaya ƙanin Bilki,
 • Yobe gari na da ba raki,
 • Tammat salamun na yo birki.

 

              domin samun karanta cikakkiyar waƙar danna koren rubutu

 

 

labarin da ya wuceWaƙar Hamdala .
Labarin na GabaWaƙar Yabon Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo