Waƙar Hamdala .

0
1016

Allahu Wahabu mai komai, Mai sa zaki ya kar birrai, Mai sa kuturu ya hau jakai, Mai bai wa mutum sanin ilimai, Karimu, Wahabu mai komai.

  • Sa’a na rika a tun farko,
  • Ka ban ilimin mutan farko,
  • A waka kar na zam soko,
  • Ka ban hikima na sa saƙo,
  • A gari, birni da duk loko.
  • ————————-
  • Ku biyo ni ki ji ni baitoci,
  • Na tsara batu na lakcoci,
  • A Gadau ta Jiharmu can Bauci,
  • Garin da na je a motoci,
  • ————————
  • Na je ni Shira na je Zaki,
  • Na je ni Gaɗau da ba gunki,
  • A nan na zamo ya ɗan zaki,
  • Jama’are na je cikin tuƙi,
  • Na kwan Azare cikin ɗaki.
  • —————————-
  • Mu ɗan koma batun na Shira,
  • Garin dutse garin Gora, kara;
  • Rumfa, Dutsen Gabas a Shira,
  • Ruwan ƙirci akwai a Shira,
  • Kare, Margi, Habe a Shira.
  • —————————–
  • Wata ran a Guru na tasowa,
  • Na je ni Bade garin Gashuwa
  • A Potiskum ban yi hutawa,
  • Sai ga ni Bagauda yan mowa,
  • Bulkachuwa ma na gotawa.
  • ——————————
  • Tafiya daɗi cikin mota,
  • Bulkacuwa nan na dan gota,
  • Damban na wuce ina mota,
  • Zan je ni Gaɗau garin tsafta,
  • Na shige Azare a kan kwalta.
  • ——————————
  • Na je ni Gamawa yan barka,
  • Garin Shehin da bai shirka,
  • Ɗan Sa’idu Ali na gaishe ka,
  • Sakwa a garin da babu
  • Allah ya saka ku kere haka.
  • ——————————
  • Na gode wahabu mai khairi,
  • Da ya ban ilmin da ba sharri,
  • Abun ga uku cikin jeri,
  • Na yi su ku ji su ba kuri,
  • Certificate two abin fahari.
  • ——————————-
  • Masters kuwa gefe can na shiga,
  • Tinƙis-tinƙis ina ta buga,
  • Karatu babu yin burga,
  • Ga aiki ga yawan sabga,
  • Allah ya nufa na kere duga.

 

domin samun karanta cikkakken littafin danna koren  rubutu.

labarin da ya wuceWaƙar Gulma .
Labarin na GabaWaƙar Yabon Manzon Allah(S.A.W).