Waƙa A Matsayin Sana’a

0
447

Mawaƙa da dama sun dogara da yin waƙa wanda rayuwarsu ta dogara a kai; wannan tunani kuwa tun daga mawaƙan jiya har zuwa na yau waɗanda ake kiransu da Mawaƙan Situdiyo.

Misali, Marigayi Alhaji (Dk.) Mamman Shata Katsina ya faɗi haka, a inda ya ce:

Jagora: Ko ni Alhaji Sarkin waƙa,
In nai waƙa kyakkyawa,
Na samu kuɗi mai kauri,
Na tara har sun kauri,
Ba ashararu ba sakarci,
Sai in kashe su ta hanya mai kyau.
(Waƙar Kuɗi a kashe su ta hanya mai kyau).

Kamilu Almajirin Maiwaƙa ma, ya bayyana haka a wata waƙarsa da yake cewa:
Jagora: Waƙa nake yi domin na samu abin miya.
(Waƙar Baba na Mashina).

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki: Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan

labarin da ya wuceYabo Daga Waƙar Aminu Alan Waƙa
Labarin na GabaTaƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa