An haife shi a garin Kudan, sunan mahaifinsa shi ne malam Bala, mahaifiyar sa kuma Hassana, ya shahara wajen iya harbi, wanda waɗansu mutane suka ce tun da suke, ba su taɓa ganin ya auna ko ya saita wani abu ba.
Amma kuma ya ƙasa bugo abin, wanda hatta ma maganin bindiga an sha kawo su wajen sa, amma da ya saita, sai kawai ka ji bindigar ta tashi, kamar yadda muka tattauna da ‘ya’yansa (Suleman da Shitu mai aski) suka ce ba a taɓa kawo masa maganin bindiga ya harba ta ƙi tashi ba a iya tsawon rayuwar sa.
Saboda haka ne ma yasa ake yi masa laƙabi da Nuhu mai bindiga, duk da yake an yi wasu a can baya, amma kuma su da kwari da baka suke yi kamar wata mace wacce ake iya kira da suna Madidi mace mai kamar maza, wadda ta kashe ɓarawo a daji ita kaɗai, ga sarkin Kudan Sambo, ga Mika na sari, ga Garba na Ode da sauran su.
Bugu da ƙari kuma, ya iya sana’ar wanzanci da ƙira da mafarauci da allura da ɗori da ba da magungunan gargajiya da gyaran keke da kuma harbi. Saboda a harkar faruta mafi yawanci shi kaɗai yake fita daji, ya tafi ya yi farautarsa a cikin dare ya dawo da safe, haka kuma wani lokacin ma yakan yi kwanaki uku ko sama da haka a daji bai ya dawo gida ba, sai dai kawai abin da ya farauto ya aiko da shi gari a siyar.
Shahararsa
Ya shahara wajen iya sarrafa bindiga ta yadda yake so kuma a lokacin da yake so, misali idan yana ɗaki a kwance a kan gadonsa, sai ya hango wata tsuntsuwa a kan wata bishiya, to zai iya auna ta daga nan inda yake zaune ya kuma harbo ta. Haka kuma akwai wani lokaci da ya tafi barikin sojoji na Fatakwal, wanda yake a Ohode ya dawo gida da wata adda, wanda wannan addar duk ƙafar da aka sara da ita ,sai dai kawai mutum ya ga ƙarfan ta gutsire ko ya noƙe ko ya lauye.
Sannan kuma ya tafi Nassarawa wajen wani gari wanda ake kira da suna Toto ya yi kwana da kwanaki a can, ya kuma tafi jihar Sokoto wajen garin Moriki, ya tafi jihar Taraba wajen garin Zink, waɗannan su ne kaɗan daga cikin dajujjukan da ya halarta daga cikin ƙasar nan banda su irin Katsina da Jigawa da dai sauran su.
Bugu da ƙari kuma, akwai wata rana ya tafi daji akan ɗan wani gajeren mashin ɗin sa, bayan ya tafi dajin sai ya samu wani waje ya ajiye shi, can sai wani mutum ya lallaɓo ya taho zai ɗauke masa mashin ɗin nasa, ai ko yana zuwa kusa da inda mashin ɗin yake, sai kawai ya ga mashin ɗin ya koma kamar Gada, sai ko ya tsaya ya ciro bakar sa wai zai harbe shi.
Can sai ga Nuhu Baushe nan ya taho ya dafa mashin ɗin sa ya hau ya kara gaba, kawai abin nan ya ba shi mamaki, kamar yadda duk wanda yake garin Kudan ko ƙaramar hukumar Kudan, ya san wane ne Lado, wanda shi Lado ɗa ne ga Nuhu Baushe, sannan kuma shi Lado idan mutane sun kai guda ɗari ko sama da haka, to ba su isa su hana shi ya wuce ba ko da ko sun kewaye shi baki ɗayansu.
A lokacin da yake ganiyarsa, da zarar ya yi wani yunƙuri, sai dai kawai a ga ya wuce, kamar yadda an sha samun waɗansu zuga a garin Kudan, sun taho domin su yi masa lahani, amma kuma da zarar ya yi wani yunƙurin, sai kawai a ga ya fice.
Saboda haka idan mutum ya yi nazari sosai, zai ga abin mamaki sosai akan sha’anin, domin kuwa kowane mutum a wannan zamanin zai iya shaidawa cewa masana na ɓangaran lafiya ne kaɗai suke yin allura ko kuma wanda ya yi ilimin zamani (boko) mai zurfi su ne kaɗai ne suke yi allura, amma kuma shi sai ga shi almajiri ne, wanda ya yi karatun allo, amma kuma sai ga shi yana yi wa mutane allura, wanda har ma ni kai na mai wannan rubutun na shaida ya yi min allura.
Haka kuma akwai mutane da yawa waɗanda suka koyi allura, saboda yawan zama da suke yi da shi misali kamar ɗansa Nuhu mai aski a kuka, wanda ya shaida mana cewa dukkanin ‘ya’yan sa da shi kan sa, idan ba shi da lafiya, to da kansa yake yin allura, amma kuma almajiri ne.
(Mun samu wannan jawaban ne ta hannun ‘ya’yan sa wato Suleman da Shittu a ranar lahadi 16/03/1442 Hijira=01/11/2020 da misalin ƙarfe goma na dare a shagon Shitu mai aski wanda yake Kuka Kudan).
Danna nan don karanta tarihin hakimin Kudan
Edita; Rumasa’u M. kallamu