Taƙaitaccen Bayani A kan Nijeriya

0
626

Nijeriya ƙasar tarayya ce da take da jihohi 36 da Babban birni tarayya guda (1). Kowace jiha rukuni ce ta siyasa mai cin gashin kanta, wanda take raba iko tare da Gwamnatin Tarayya kamar yadda aka lissafta a cikin Tsarin Mulkin Tarayyar na Nijeriya.

Babban birnin tarayya, wanda aka sani da Federal Capital Terittory (FCT), shi ne babban birnin tarayyar Nijeriya, kuma yana cikin garin Abuja.

FCT ba jiha ba ce, amma ana gudanar da ita ne ta hanyar zababbun jami’an da ke Kula da Gwamnatin Tarayya.

Kowane yanki ya kasu kashi-kashi zuwa ƙananan hukumomi (LGAs). A halin yanzu akwai jimilar ƙananan hukumomi 774 a Nijeriya. A ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki. Jihohi 36 suna da daidaituwa amma ba maɗaukakiya ba, saboda ikon mallaka, yana tare da Gwamnatin Tarayya.

Majalisar ƙasa za ta iya yin gyara ga kundin tsarin mulki, amma dole a kawo sauyi kowane kashi biyu bisa uku na jihohi 36 na tarayya.

Domin sanin cikekken bayani a kan Nijeriya danna nan

labarin da ya wuceTarihin Nijeriya Kashi Na Ɗaya(1)
Labarin na GabaTarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD)
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.