An haifi Gwani Saleh ɗan Abdullahi jikan Abdullahi a Ƙasar Jahun. Mahaifin sa ya rasu yana ƙaramin yaro, don haka sai mahaifiyar sa ta koma da shi garin Zarga ta kuma kyautata tarbiyar sa.
Gwani Saleh ya taso da kaifin basira da son Alƙur’ani. Don haka ya lazimci makarantan garin Zarga irinsu Malam Abdullahi har Ubangiji Ya hore masa Alƙur’ani ya haddace shi yana ɗan shekara tara (9). Gwanin Alƙur’ani ma’abocin ƙan-ƙan da kai da gaskiya da riƙon amana. An ce tun yana ɗan shekara sha biyu ya sha fari.
Gwani Saleh ya yi tafiye-tafiye na neman karatu a inda yazo Kano ya sauka a tsangayar Gwani Nadudu. Daga bisani kuma ya lazimci mashahurin malami Malam Aliyu Basakkwace ya karanci Fiƙhu da Hadisi da tafsiri Shaharar da tsangayarsa ta yi ya sanya makaranta daga nisan duniya yin takakkiya don ɗosana daga haskenta. Manyan abokanen karatun Gwani Saleh sun haɗa da:-
- Gwani ɗan Kwandarai
- Gwani Ɗan birni
- Gwani Daudu
Game da yawan almajiran da suka samu Alƙur’ani a hannun sa kuwa, wannan ɗan littafi ba zai ɗauke ambaton su ba, sai dai mu yi ishara ga waɗansun su:
- Malam Muktari Abdullahi
- Yayan sa Gwani Yahuza da Gwani Lawi
- Malam Husaini Rijiyar Lemo
- Malam Sham’unu
- Malam Ibrahim Maidarasu
Gwani ya rayu cikin karamci da girmamawa daga maƙwabtan sa, musamman ma Alhaji Sunusi Ɗantata da al’umar Unguwar ƙoƙi da kewayenta. A halin yanzu wannan tsangaya tana ƙarƙashin kulawar ɗan sa Gwani Yahuza inda ta ƙara bunƙasa ta hanyar shigo da tsarin ilmin zamani, ɓangaren firamare da sakandare. A lokaci guda kuma, ga tsohon tsarin tsangaya na gudana da makaranta da mahaddata.
Gwani Yahuza ya samu gogayya da wayewa ta zamani a inda ya dangana da ƙasar Masar don karatun sa na digirin farko. A halin yanzu Gwani Yahuza ɗaya ne daga manyan alƙalai na musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa. Gwani Yahuza shi ne ɗan Najeriya na farko da ya karɓi kyautar girmama mahaddata Alƙur’ani daga ƙasar Saudi Arebiya. Baya ga wannan rassa na makarantar akwai majalisai a unguwannin Gwammaja da Kurnar Asabe da Ƙoƙi.
Ita wannan makaranta ta Gwammaja, Gwani Lawi ne ya kafa ta mai suna Ma’ahad Gwani Lawi Litahfizil Ƙur’anil Karim.
Gwani Lawi ya yi babbar Diflomarsa a Jami’atul Ƙur’anil Karim da ke Sudan, kuma shi ne wan da ya kafa ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani ta farko a Najeriya, mai suna Rabiɗatul Huffazil Ƙur’ani, Nigeriya. Gwani Sale Ɗanzarga ya bar ‘ya’ya goma sha biyu, maza da mata.
Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Ɗankwandarai danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD) danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.