A daren tarewa abubuwa guda goma sha ɗaya (11) ya kamata ma’aurata masu addini da wayewa su aikata:
- Addu’ar shiga gida
- Sallama
- Shigowa da abincin da ya dace
- Sallatar nafila raka’a biyu tare
- Karanta wannan addu’o’in
“Allahumma baarik liy fiy ahliy wa baarik lahum fiyya. Allahummaj ma’a bainana ma jama’ata bi khairin wa farriq bainana iza farraqta ila khairin” ko kuma “Allahumma baarik liy fiy ahliy wa baarik li ahli fiyya, Allahummar zuqhum minni warzuqni minhum, Allahummaj ma’a bainana ma jama’ata fi khairin wa farriq bainana iza farraqta fi khairin’’
6. Sannan ango ya kama goshin amaryarsa ya karanta
“Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi wa a’azu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi’’
7. Taƙaitacciyar hirar ɗebe kewa da soyayya
8. Su yi wanka da brush
9. Idan ba ta jinin al’ada a yi mu’amalar aure su karanta ‘Bismillahi, Allahumma jannabinas shaidan wa jannaibis shaidana ma razaqtana’’
10. Kiyaye ladubban mu’amalar aure
11. Bayan an gama a yi wanka ko alwalla kafin kwanciya.
Washegarin tarewa, ma’aurata suna zaunawa dogon lokaci domin meeting, su tattauna a kan yadda za su rayu har ƙarshen rayuwa cikin ƙauna da haɗin kai, a tsara gida da yadda zamantakewa za ta kasance, domin rayuwa ta ilmi, ƙauna da tausayawa, su fahimci manufofin juna da tsare-tsaren juna, tafiya a kan tsari shi ne asasin saurin isa ga manufa. Masu hikima na cewa “Zo mu zauna zo mu tsara”
RUFEWA
Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon, shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba, wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar ya na cewa: “Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida. Idan miji da mata suka sami hada kansu bisa turba ta musulunci to sai ka samu yayansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba akan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.
Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.
Subhanakallahumma wa bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.
karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki ko domin sauki cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu