Tag: yadda ake

  • Tatsuniyar Dawi Mai Turmi

    Tatsuniyar Dawi Mai Turmi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can wata ’yar unguwa da ke dab da wani tsauni, an yi wasu’yan biyu, Awa da Dawi. Tun suna yara mahaifiyarsu ta rasu, suka ci gaba da taimakon juna. To, amma shi Dawi hatsabibin yaro ne, kuma duk sanda ’yar’uwarsa Awa ta dafa abinci, sai ya cinye. Kullum ana haka har ta kai sai da ta tona rami domin ta riƙa ɓoye rabonta na abincin a ciki, amma sai ya tono ya cinye.

    Wata rana Dawi ya ce da Awa: “Ni fa na gaji da zaman garin nan. Ina so ki goya ni mu yi ƙaura mu je mu zauna a wani gari inda za mu sami kwanciyar rai.” Bayan Awa ta yi ɗan tunani, sai ta amince, ta goya shi, kuma ta ɗauki ’yan tarkarcensu a ka, suka kama hanya.

    Suna cikin tafiya sai Awa ta ce: “Na ga inda za mu tafi yana da nisa kuma ga shi ina jin yunwa.” Can sai Dawi ya hango wani ɗaki a gefen hanya, ya ce su shiga ciki. Da suka shiga, sai suka tarar da abinci a ciki. Dawi ya ce: “To ga shi Ubangiji ya ji kukanmu, ai sai mu ci.”

    Ba da wata-wata ba sai Awa ta yarda. Suka cinye abincin nan duka, duk da yake ba su san mai shi ba. Suka sha ruwa, suka sake kama hanya. Suna tafiya har suka isa wani
    gari. Dawi ya ce: “Albishirinki, ni fa ina da wata dabara.” Awa ta ce: “Kawo ta mu gani.” Sai kawai Dawi ya tara yaran garin nan ya ce shi fa ɗan dabo ne, kuma zai yi wasanni iri-iri domin ya ɗebe musu kewa.

    Daga nan sai ya ce a kawo turmi, domin ya yi musu wasan daka mutum irin yadda ake yi a garinsu. Dawi ya fara shiga turmi, yara suka daka shi, kuma ya fito jiki lafiya lau. Wani daga cikin yaran ma ya shiga, aka daka shi, amma sai ya fito da jikinsa jina-jina. Da yaran suka ga haka, sai wasu daga cikinsu suka tsere.

    Sauran da suka tsaya kuwa, sai suka riƙa shiga turmi ɗaya bayan ɗaya ana laƙada su, suna fita jiki a kumbure. Da mutanen garin suka ga abin da yake faruwa da yaransu, haushi ya kama su, suka yi ca a kan Awa da Dawi. Dawi ya ce da su: “Don Allah ku dakata.

    Idan kun yi haƙuri, za ku ga abin mamaki.” Mutanen suka tsaya, suna jira su ga abin da Dawi zai yi. Sai ya yi wani irin siddabaru na hatsabiban yara, nan take duk yaran da aka yi wa rauni a turmi suka warke sarai. Mamaki ya kama jama’a, suka ce sai shi da Awa su zauna a garin nan tun da suna da abin mamaki da asiri haka.

    Suka yarda. Suka zauna a garin. Dawi da Awa suka girma, ya zama sadaukin matashi. Awa kuma ta zama kyakkyawar mace, son kowa. Dawi ya kama noma da farauta. Ya tara dukiya mai yawa kamar ba maraya ba. Ita kuma ta zauna da shi suna cin duniyarsu.

    Mutanen gari suka yi wa Dawi laƙani: “Dawi Mai Turmi.” Shi kuma yakan ce: “In da mai son mu daka shi ya zo.” Duk sanda ya faɗi haka sai a bushe da dariya, labarinsa ya bazu a duniya. Shi yasa ma kuke jin duriyarsa a taskar tatsuniyoyi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai.
    • Tausasa wa ɗan’uwa shi ma wani jari ne.
    • Kar a yi saurin yanke hukunci ga abin da ba a san haƙiƙaninsa ba.
    • Arziƙi a ƙafa yake.
    • Motsi ya fi zama

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wani mutum ne yana zaune da matarsa a cikin talauci a wani ɗan ƙauye, babu cin yau balle na gobe. Wata rana sai ya je gona ya ga wata busasshiyar bishiya, ya hau ya fara sara da gatarinsa domin neman abin zaman gari. To akwai wani dutse mai kogo kusa da gonar.

    Sai kwatsam, ga wasu mutane su goma sha biyu riƙe da kwari da baka sun fito daga ciki. Da fitowarsu sai suka zauna suka ci abinci, suka tafi. Amma kafin su bar wurin sai da suka faɗi wani abu kamar haka: “Kalja sum sum, Kalja sum sum, Kalja sum sum.” Da faɗin haka sai mutumin ya ga ƙofar kogon dutsen ta rufe.

    Sai dai ya ga kamar ɗaya daga cikinsu ya manta da wani abu sai yace: “Buɗe sum sum, Buɗe sum sum, Buɗe sum sum.” Sai ƙofar kogon ta buɗe, ya shiga ya ɗauko wata batta daga ciki; ya fita, suka kama hanyarsu. Bayan sun tafi, sai mutumin ya matsa kusa da dutsen domin ya kashe kwarkwatar idonsa.

    To, tun da ya ji abin da suka faɗa, sai shi ma ya faɗa, ƙofar kogon kuma ta buɗe, sai ga ruwa. Ya sake cewa: “Kalja sum sum,” wata ƙofar ta buɗe, sai ga wuta. Bai fasa ba dai, ya sake faɗa, wata ƙofar ta buɗe, amma a wannan wuri sai kawai ya ga ƙyalƙyali irin na zinariya. Ga kuma tarin zinariyar mai ɗinbin yawa, abin gwanin ban mamaki, har ma da tsoro.

    Can gefe kuma tarin azurfa ne kamar ba iyaka, ga kuma kuɗi a wani ɓangaren kamar duk kuɗin duniya baki ɗaya aka tara a can saboda yawansu. Mutumin nan ya shiga ya ɗebi dukiya iya yadda zai iya ɗauka, ya ɗora a ka, yana riƙe da gatarinsa ya kama hanyar gida, amma fa duk sai da ya tabbata ya rufe duk ƙofofin kogon nan da ya buɗe.

    Yana isa gida matarsa ta tarye shi da murna kamar dai yadda takan yi kullum idan ya je neman abinci ya dawo. Mutumin da gaggawa kuma a cikin murna ya nuna wa matarsa zinare da kuɗi da azurfar da ya samo. Matar kuma a guje ta je ta aro ma’auni a wajen maƙwabta suka auna zinaren.

    Ba da saninsu ba ashe akwai ɗan guntun zinaren ya maƙale a ma’aunin da suka mayar masu. Masu ma’auni suka ajiye, har dare ya yi. Sai ga wani abu ya haske musu ɗaki, suka yi ta mamaki. Da gari ya waye suka shiga bincike, suka gano ashe zinare ne a jikin ma’auni da maƙwabta suka ara da maraice.

    Daga nan suka aiki ɗayansu ya je ya tambayi mutumin inda ya samo zinariya. Ya dai matsawa mutumin sai ya nuna masa inda ya samo domin shi ma ya je ya ɗebo. A kan tilas mutumin nan ya tasa ƙeyarsa suka tafi. Da suka isa, sai mutumin ya gaya wa maƙwabcinsa abinda ake cewa ƙofofin kogon dutsen nan su buɗe.

    Daga nan fa sai ya tafi gida abinsa. Maƙwabci ya faɗi abin da mutumin ya gaya masa, sai nan da nan ƙofofin suka buɗe. Sai ga dukiya, kamar ta fi wadda mutumin farko ya fara gani jiya. Maƙwabci ya lafci dukiya iyakar son ransa, to amma da ya zo fita sai ya rikice, ya rasa abinda zai faɗa ƙofar kogo ta buɗe.

    Jim kaɗan sai mutanen nan goma sha biyu suka dawo daga inda suka je. Suka shiga kogon, sai kawai suka tarar da maƙwabci. Ganin ya kwashi dukiya ba tare da izininsu ba, sai suka kama shi suka yanka, suka ajiye gawarsa a gefe. Washe-gari da mutumin ya ji ana cewa maƙwabcinsa bai dawo gida ba, sai ya koma dajin nan, ya jira sai da mutanen nan suka fito suka tafi, ya je ya buɗe kogo, ya shiga.

    Da shigarsa sai ya tarar da gawar maƙwabcinsa a gefe, mutanen nan sun yanka ta gunduwa-gunduwa. Ya tattara gaɓobin, ya zuba a mangala, ya kama hanyar gida. Sai ya ɗebi zinariya, ya je wurin shugaban dogarai ya ce da shi ɓarayi sun tare su, har suka kashe mishi ɗan’uwa, saboda haka ya ce masa: “Don Allah ga ladan zinariya nan ka sake haɗe min shi, domin a rufe shi a haɗe.”

    Sarkin Dogarai ya haɗa mutum, amma tun kafin a ɗauke shi a tafi da shi wurin binnewa ra, sai mutanen kogo suka je gidan Mai Gari suka ce wani mutum ya sayi saniyarsu bai biya ba, amma ya mutu an kawo gawarsa gidan Sarkin Dogarai. Sarki ya bincika aka tabbatar da haka; aka kawo gawar, suka ce a ba su.

    To, dama suna so a ba su gawar ne domin su cinye, Sarki ya hana. Yasa Sarkin Dogarai ya ba mutumin nan gawar maƙwabcinsa, aka binne ta bisa al’adar garinsu. Mutanen kogo suka haƙura, shi kuwa matalaucin nan da ya sami dukiya a dare ɗaya, ya yi ta cin
    duniyarsa shi da matarsa. Amma kuma duk sanda ya ga matalauta yakan taimake su da kuɗi da abinci da jari domin su yi sana’a. Sai mutan ƙauyen suka sa masa suna Mai sa’a. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mahaƙurci mawadaci.
    • Wanda ya daka rawar wani zai rasa turmin daka tasa.
    • Kuɗi masu gidan rana.
    • Duk wanda ya haƙura da kaɗan Allah zai wadata shi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Jika Da Kaka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Jika Da Kaka

    Tatsuniyar Jika Da Kaka

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can wani ɗan ƙauye da ke kusa da Gulbin Tattabaru, an yi wata yarinya da ke zaune tare da kakarta. Rannan yarinyar tana shara sai ta tsinci kurkunu ta bai wa kakarta ta ajiye mata. Da ta gama sharar sai ta je wurin kakar ta tambaye ta: “Kaka, ina kurkununa?” Kakar ta dubi jikarta ta mayar da jawabi: “Ai na cinye, jikalle.”

    Da jin wannan amsa sai yarinya ta fusata; ta ƙura wa kakar ido tace: “A gaskiya kaka ban yarda ba.” Daga nan ta ɗauki buta, ta cika ta da ruwa; ta kama wata kuka ta haye; ta yi zamanta ba niyyar saukowa. Da kakarta ta ga ya kamata ta sauko ta ci abinci, sai ta je kiran ta.

    Yarinya abu kamar da wasa, sai ta ƙi saukowa kakar ta kira maƙwabta da ƙawayen jikarta domin su sa ta ta sauko, ammaina, abu ya faskara. Sai ta ce da wasu samari: “Don Allah ku taimaka ku sare mini kukar nan tun da jikata ta ƙi saukowa.” Samari suka yarda suka debo gatura daga gidajensu.

    Kowa ya yi ɗamara suka fara saran kuka. Suna waƙar gayya, wannan ya sara idan ya gaji wannan ya karɓa, da haka da haka har suka ci ƙarfin kaurin bishiyar. Can da kuka ta nuna layin faɗuwa, sai kawai aka ga yarinyar ta fara rikiɗa, har ta zama kurkunu. A halin haka sai ta haifi ’ya’ya da yawa.

    Kuma nan take ta sake rikiɗa, ta koma mutum a kan bishiyar. Kowa ya buɗe baki sai kallon abin al’ajabi yake yi. Sai ta ce da kakarta da sauran mutanen: “Ga kurkunu nan da yawa ku ci ku ƙoshi, amma ki rage mini guda ɗaya kawai; daga nan sai ki koma gida, zan sauko.”

    Da kowa ya bar wurin, sai yarinya ta sauko ta kama hanyar gida. Tana isa gida sai ta yi wa kakarta bayani cewa: “Ai aljanun da ke zaune a kukar nan ne suka hana a sare ta, saboda haka ne ma suka rikiɗar da ni har na haifi kurkunu domin ki dawo min da shi a ƙyale musu gidansu.

    Kuma sun ce in gaya miki ki gaya wa Mai Gari kada a sake ƙoƙarin sare wannan kukar.” Kakar yarinya ta yi mamakin wannan bayani, kuma ba ta yi nawa ba ta je ta sanar da Mai Gari saƙon da aljanu suka aiko ta hannun jikarta. Shi kuma Mai Gari ya sa aka sanar da jama’arsa cewa kada wani ya kuskura ya sare kukar nan domin gidan mutanen ɓoye ne, abokan zaman lafiyarsu. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wasa tsakanin jika da kaka ba abu ne mai kawo ɓacin rai ba.
    • Wasu mutan ɓoye abokan zama ne ba abokan faɗa ba.
    • Komai za ka yi ka yi tunani kafin ka aikata shi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Yan Matan Fangama

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken: Hoton Waibuwar Hausawa a Cikin Waƙoƙin Mamman Shata

    Maƙala Mai Taken: Hoton Waibuwar Hausawa a Cikin Waƙoƙin Mamman Shata

    Hoton Waibuwar Hausawa a Cikin Waƙoƙin Mamman Shata

     Yakubu Aliyu GOBIR

    Department of Nigerian Languages

    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

     &

    Abu-Ubaida SANI

    Department of Languages and Cultures

    Federal University Gusau, Zamfara

    Article Citation: Gobir, Y. A. & Sani, A-U. (2018). Hoton waibuwar Hausawa a cikin waƙoƙin Mamman Shata. Studies in the Songs of Dr. Mamman Shata Katsina. Katsina: Umaru Musa ‘Yar’adua University, 189-203. ISBN: 978-978-5588-2-4.

     Tsakure:

    Masana da manazarta sun tafi kan cewa, daga cikin adabin al’umma (na baka ko rubutacce), mutum na iya fahimtar salon rayuwar al’ummar na gaba ɗaya. Wannan ya haɗa da tunaninsu da imaninsu da fahimtarsu da al’adunsu da tsarin zamantakewa da sauransu. Mawaƙa na taka muhimmiyar rawa wurin fito da tunanin al’umma.

    A bisa wannan zaren tunani ne wannan takardar ta ginu, inda take ƙoƙarin hango waibuwar Hausawa daga bakin Mamman Shata. Shata yakan danganta mutum da aljani ko kuma ya ba shi wata siffa ko ɗabi’a ta aljani domin nuna shahara da buwayar mutumin. Haka ma yakan danganta magani da aljani a wasu daga cikin waƙoƙinsa.

    Wannan takarda ta bibiyi irin waɗannan waƙoƙi da suka haɗa da ‘Malam Babba na Ƙofar Gabas,’ da ‘Hassan Sarkin Dogarai,’ da ‘Mamman Sakkwato Kyaftin,’ da kuma ‘Waƙar Sarkin Bori Sule.’ Daga ƙarshe takardar ta fahimci cewa, Bahaushe ya yarda da wanzuwar aljani har ma ya ɗauke shi a matsayin halitta mai matuƙar hatsabibanci. A taƙaice, Bahaushe ya tafi kan cewa, ƙololuwar buwaya kan samu ga ɗan’adam yayin da ya yi cuɗanya da aljani.

    Muhimman Kalmomi: Hausaswa, Waibuwa, Aljani, Mamman Shata

     1.0 Gabatarwa

    Waƙa ba sabuwar aba ba ce da ake da buƙatar dogon bayani game da ma’anarta. Masana da manazarta da dama sun bayyana ma’anar waƙa a rubuce-rubuce da suka gabatar a matakan ilimi daban-daban. Daga cikin masana da marubuta da suka yi tsokaci kan ma’anar waƙa sun haɗa da: Gusau (1993) da Ƙaura (1994) da Bunza (1988) da Yahya (1996) da Habibu (2001) da Zurmi (2006) da Abdullahi (2017) da makamantansu.

    Kasancewar waƙa zance tsararre da ake rerawa cikin salo da raujin murya ta musamman tare da zaɓen kalmomi da jera su cikin tsari mai jan hankali, hakan ya sa waƙa ta kasance mai matuƙar tasiri ga zukatan al’umma. Masana da marubuta irin su: Furniss (1996) da Gusau (2009, 2014); Sani (2016) da Sani da Tsaure (2016) sun tabbatar da cewa, waƙa ta kasance aba mai matuƙar tasiri ga zukatan al’umma tun zamani mai tsawo da ya wuce.

    A taƙaice za a iya cewa, waƙa ta fara tasiri tare da samar da sauyi ga rayuwar Hausawa tun lokacin da suka fara ta’ammuli da ita. A wani ra’ayi mai kama da wannan, A’azamiyyun, 1962 da CNRS a cikin Science Daily, 2014 da Sani, 2016; duk sun tafi kan cewa, tasirin waƙa ba zai taɓa gushewa ba daga zukatan al’umma. Wannan ne ma ya sa, waƙa ta kasance babbar hanyar isar da saƙonni ga al’umma, kuma saƙonnin na yin tasiri ga rayuwarsu.

    Ƙudurin wannan takarda shi ne tsakuro ɗiyan waƙa da Dr. Mamman Shata ya kawo hoton waibuwar Hausawa cikin waƙoƙinsa.

    2.0 Taƙaitaccen Tsokaci Game Da Dakta Mamman Shata

    Dakta Mamman Shata ba ɓoyayyen mawaƙi ba ne. Yana ɗaya daga cikin makaɗan da suka fi kowa suna da ɗaukaka a duniyar waƙa a ƙasar Hausa. Waƙoƙinsa sun shiga duk lungu-lungu da saƙo-saƙo na ƙasar Hausa, haka ma sunansa. Wannan ya samo asali ne a dalilin zunzurutun fasaha da ke cikin waƙoƙinsa tare kuma da farin jini da yake da shi, wanda hakan ya zamar da shi wani zakara tsakanin mawaƙan lokacinsa.

    Hakan ne ma ya sa, har a yau mawaƙa da dama (cikinsu har da na zamani) suke ƙoƙarin danganta kansu da Shata. A taƙaice ke nan, inkiyar Shata da za a yi wa mawaƙi a yau na nuna ficen mawaƙin a fagen waƙa. Duniyar mawaƙan Hausa sun yi ittafaƙin Shata a matsayin sarkin waƙa. Nura M. Inuwa (Mawaƙin zamani) ya ambaci Shata a matsayin sarkin waƙa, inda yake cewa:

    Mai sautina kunno,

    Wani zance zan tono,

    Yaro na mawaƙa ne ni ba Shata ne ba,

    Matsayi ban kai a kira ni da sarkin waƙa ba.

    Daga baitin da ke sama, lallai mawaƙin yana nuna matsayinsa bai kai a kwatanta shi da Shata ba. Dalili kuwa shi ne, shi (mawaƙin) yaro ne kawai a cikin mawaƙa, amma bai kai matsayin sarkin waƙa ba. A taƙaice ke nan, Shata sarkin waƙa ne.

    Saboda fice da Shata ya yi a duniyar waƙa, ƙoƙarin kawo tarihinsa zai zama maimaici ne kawai na aikin da masana da marubuta suka daɗe da baje guminsu a kai. Saboda haka, a wannan gaɓa takardar za ta waiwaiyi irin ayyukan da aka yi ne game da Shata, wanda kuma ke ɗauke da tarihin rayuwarsa.

    Abdulƙadir (1975) shi ne aiki na farko na ilimi da aka yi a kan Mamman Shata da waƙoƙinsa. Sai Sheme da wasu (2000) sun kawo cikakken tarihin Shata a cikin littafinsu mai suna: Shata Ikon Allah. Haka kuma, Kankara, (2013) ya yi matuƙar ƙoƙari wurin tattaro cikakken tarihin Shata da kuma aikace-aikacensa masu tarin yawa.

    Ya tattara wannan tarihi cikin littafinsa mai suna: Mahadi Mai Dogon Zamani: Shata da Kundin Waƙoƙinsa. Wannan littafi yana ɗauke da tarihin rayuwar shata tun daga kan iyaye da kakanninsa. Sannan littafin ya kalato irin abubuwan mamaki da al’ajabi da Shata ya riƙa nunawa a lokacin rayuwarsa. Bayan waɗannan, akwai kuma wasu ayyuka da aka gudanar a kan Shata, da suka haɗa da Ɗangambo (1973) da Gusau (1996) da kuma Gusau (edita) (2003).

    3.0 Waibuwar Hausawa A Waƙoƙin Shata

    Mamman Shata ya kawo ire-iren waibuwar Hausawa a wasu daga cikin waƙoƙinsa. Ko bayan Shata ma, akwai mawaƙa da dama da suka nuna hoton waibuwar Hausawa cikin waƙoƙinsu. Wasu daga cikin waɗannan mawaƙa su ne: Gambo, (a cikin waƙarsa ta Tsoho Tudu) da Ɗan’anace (a cikin waƙarsa taShago) da Bage Ɗansala (a cikin waƙar ‘Yarkala) da Garba Ɗanwasa (a cikin waƙar Gojirgo) da kuma Sani Ɗanbalɗo (a cikin waƙarsa ta Ciran Rogo) da ma wasu mawaƙan na daban. Mawaƙan Hausa na fito da waibuwa bisa wasu tubalai cikin wasu gurabu na ɗiyan waƙoƙinsu. Sukan yi hakan ta amfani da wasu tubalai kamar:

    Kambamar zulaƙe

    Jarumta

    Tsafi

    Magani

    3.1 Tubalin Kambamar Zulaƙe

    Kambamar zulaƙe ta ƙunshi kurarawa da rurutawa tare da zuzutawa da kuma ɗaukaka abu sama da yadda yake a haƙiƙa. Ahmad (2010) da Fitri (2010) na da ra’ayin cewa, kambamar zulaƙe na samuwa ne yayin da aka yi amfani da wasu kalmomin da za su ɗaukaka wani mutum ko wani abu sama sosai da yadda ya kasance a haƙiƙa.

    Manazarta irin su Omosowone da Nelson (2003) da kuma Amaechi (2010) na da irin wannan fahimta, inda suka ƙara da cewa; kambamar zulaƙe ta ƙunshi ɗaukaka wani abu zuwa wani matsayin da bai kai wurin ba. Sai dai mai kambamar zulaƙe yakan yi ne dumin barkwanci ko dai gyaran zance ko kuma jan hankali zuwa ga abin da yake magana a kai.

    Bunza (2015) yana ganin cewa, kambamar zulaƙe shi ne mafi ƙololuwar salo da mawaƙi zai iya amfani da shi, domin ƙawata waƙarsa tare da jan hankalin mai sauraro da kuma ɗebe wa masu sauraro tantama dangane da wani abu da dai makamantansu.[1] Shata yakan danganta faruwar wasu abubuwa da waibuwa yayin da yake kambamar zulaƙe, domin fito da girman wani abu ko wani mutum. A cikin waƙar Sarkin Bori Sule, Shata ya yi amfani da kambamar zulaƙe wurin da yake cewa:

    Jagora: Shi ke kwana bakwai,

    Ba ci ba sha Sule,

    Kullum bori yake.

    ‘Yan Amshi:    Sarkin bori Sule.

    Binciken kimiyya ya tabbatar da ɗan’adam ba zai iya sama da kwana huɗu a raye ba tare da ruwa ba, balle har a ce yana aikata wani aiki, kuma mai wahala da buƙatar jijjiga jiki.

    A nan kuwa, sai ga shi Shata yana cewa, ai shi Sule na shafe har tsawon kwanaki bakwai ba tare da ci ko sha ba, sai dai zunzurutun bori. Haƙiƙa a nan kambamar zulaƙe ce Shata ya yi game da borin Sule.

    A cikin waƙar Hassan Sarkin Dogarai, Shata ya kawo kambamar zulaƙe dangane da girman shi Hassan.[2] Yayin da yake siffanta girman Hassan a cikin waƙar, sai yake cewa:

    Jagora: Mutuum huɗu da rabin mutum,

    ‘Yan Amshi: Hassan Sarkin Dogarai.

    Jagora: Mutuum huɗu da rabin mutum,

    ‘Yan Amshi: Hassan Sarkin Dogarai.

    Haƙiƙa wannan kambawa ce Shata ya yi dangane da girman Hassan Sarkin dogarai. Domin kuwa, ko kusa Hassan bai kai wannan girma da ake kwatanta shi da shi ba.

    Ko bayan Shata, akwai mawaƙan Hausa da ke amfani da hoton waibuwar Bahaushe wajen gina kambamar zulaƙe. Misali Gambu ya yi amfani da kambamar zulaƙe wajen bayyana yadda Tsoho Tudu ke da tsananin waibuwa. Ya yi hakan ne a cikin waƙarsa mai suna Tsoho Tudu. A cikin waƙar yake nuna cewa, saboda tsantsar ƙuƙuwa ta Tsoho Tudu, ko da furarsa ce ta zube ƙasa, to hatta ƙwaro ba ya iya taɓinta.[3]

    Jagora: “Don duk mai ku]i a Arewa

    Ko wa ya haihwai ɗan gaton’uwa

    Babu kamar guda mai ƙuƙuwat Tudu

    Sai dai a gwada mai tara jalli

    Duk da hura tai tat tuɗe ƙasa

    Tabbata ƙwaro bai taɓin ta

    Saboda mugunyar ƙuƙuwa tai”.

    3.2 Tubalin Jarumta

    Jarumta ta ƙunshi jajircewa da dagewa cikin zage damtse da taƙarƙarewa a kan duk wani abu da aka sanya a gaba. Wannan ya haɗa da fitar da tsoro da fargabar abin da aka tunkara tare da dakakkiyar zuciya da ƙarfin guiwar hangen nasara. Wannan ne ma ya sa, masana irin su: Becker da Eagly (2004) da kuma Blau da Zimbardo (2011) ke da ra’ayin cewa, jarumta ta ƙunshi aikata ayyuka da ke da matuƙar hatsari ga rayuwa.

    Wato dai, sau da dama jarumi kan cusa kansa ga halaka. Shi ya sa Bahaushe ke cewa: “Uwar rago ake yi wa barka, ta jarumi sai jaje.” Ke nan dai, rago ne ke tsira saboda karaya kan sa shi guje wa bacin rana. Shi ko jarumi, a koyaushe dagewa yake yi, “sai ya ga abin da ya ture wa Buzu naɗi.”

    Akan samu jarumai cikin al’umma, inda jarumtar ta danganta ga sana’o’i ko zamantakewa da dai sauransu. Misali, akan samu jarumai cikin manoma ko mafarauta ko sarkawa ko maharba da sauran sana’o’i da ke buƙatar jajircewa da nuna bajinta. Sai dai kuma, nuna jarumta bai tsaya ne ga kyawawan ayyuka ba kawai.

    Akan nuna jarumta har ga ɗabi’u da ayyuka da suka kasance ababan ƙi cikin al’umma. Sun haɗa da sata da fashi da sane da makamantansu. Douglas da Mathew (2012) na da wannan ra’ayi, inda suka nuna cewa, duk wata jajircewa da nuna bajinta akan iya kiran ta jarumta, ba wai sai ga abin ƙwarai ba.

    Waƙar Sarkin Bori Sule kyakkyawan misali ne na yadda Shata ke nuna dangantakar jarumta da waibuwa. Misali a cikin waƙar, Shata na nuna cewa, idan Sule ya faɗi magana bayan ya yi duba, to kuwa sai ta tabbata. Ke nan dai ya ƙware a kan sana’ar duba, wanda hakan ne ya zamar da shi jarumi da ya yi fice. Waibuwa ce ta zamar da Sarkin Bori Sule jarumi ga tunanin Shata. Ya ce:

    Jagora: Bugi ƙasa ka duba musu,

    Shidda shidda ka ɗauke uku,

    Ka ga idan ka haɗa su sun zama tara,

    Kowa aka gani cikin tara ɗin nan,

    Yai sha’ani nai shi ta rufa …

    Ka je Baba ya duba maka.

    Idan ya zana ƙasa ya duba maka,

    Ya ɗaga kai ya shaida maka,

    Ka ga kamar da shi ne a kai.

    ‘Yan Amshi: Malam Babba na Ƙofag Gabas.

    A wani baitin na daban, Shata ya nuna ficen Sarkin Bori Sule da cewa, nan take marar lafiya ke samun sauƙi idan dai har aka kai shi ga Sule. Shata yake cewa:

    Jagora: Yau wannan zamani,

    Wannan lokaci,

    Ko wani ke zazzaɓi,

    Ka ga ana gai da shi,

    Yana amsawa jika-jika,

    Ku kai mai borin Sule,

    Sarkin Bori Sule.

    Yan Amshi: Sarkin bori Sule.

    Jagora: Yanzu sai ka ga sun warware,

    Suna yawon duniya.

    ‘Yan Amshi: Sarkin bori Sule.

    Baya ga haka Shata ya nuna cewa, Sule ya yi matuƙar sanuwa a garuruwa daban-daban na ƙasar Hausa. Duk kuwa a dalilin bori ne. Ya bayyana hakan inda yake cewa:

    Jagora: Wurin rangadi Sule,

    Ya zo birnin Kano,

    Na Kazaure sun sani,

    Katsinawa sun sani,

    Ya je Kukar Bauɗe Shiɗe,

    Ya nemo bori duka.

    ‘Yan Amshi:    Sarkin bori Sule.

    A wani baiti makamancin wannan, Shata ya kawo wasu muhimman mutane masu manyan matsayi da muƙamai a cikin Hausawa tare da cewa su ma sun san Sule a dalilin bori. Daga cikinsu har da sarki da alƙali da magajin gari da kantoma da DPO da razdan har ma da gwamna. Shatan yake cewa:

    Jagora: Sarki ya sani,

    Alƙali ya sani,

    Magajin gari ya sani,

    Kantoma ya sani,

    D.P.O. ya sani,

    Kuma Razdan ya sani,

    Kuma gwamna sun sani,

    Duka sun san borin Sule.

    ‘Yan Amshi:  Sarkin bori Sule.

    aƙiƙa baitukan da ke sama, suna nuna mana yadda Shata ke danganta waibuwa da shahara. Ya nuna yadda Sule ya shahara a sanadiyyar bori. Sai dai yana da kyau a tuna ba Shata ba ne kaɗai ke da irin wannan ra’ayi a cikin mawaƙan Hausa. Misali, Ɗan’anace ya danganta shahara da buwayar Shago[4] da hulɗa da aljani. Ya kawo hakan ne cikin waƙarsa mai suna: Shago Mai Hagun Mai Dama, inda yake faɗin:

    Jagora: Ɗan Audu duk da idanunka ba awa na mutum ba,

    Ɗan Audu ya hau bori, borin da ba shi da girka,

    … ba a gyara maka iskoki ba.

    ‘Yan Amshi:    Arne ba a gyara maka iskoki ba.

    A nan yana nuna cewa, hatta siffar Shago na jirkicewa yayin fafatawa. Wato dai yakan koma tamkar ba mutum ba. A nan ya ƙara da kwatanta wannan yanayi da hawan bori, wanda kuma ba a yi wa girka ba. Ma’ana dai, tamkar mutum da ke ta’ammuli da aljanu alhali ba a yi masa girka domin daidaita su a kansa ba.

     3.3 Tubalin Tsafi

    Tsafi ya shafi hulɗa da aljani tare da biya masa wasu buƙatunsa domin shi kuma aljanin ya riƙa taimaka wa mai hulɗa da shi wajen yin abubuwan ban mamaki, da kuma biya masa wasu buƙatun da zai iya buƙata yau da gobe. Za a iya kallon tsafi a matsayin mafi ƙoluluwar mataki da mutum zai taka a matsayin hanyar waibuwa. Matsafi kan yi abubuwan ban mamaki waɗanda ga al’ada, ɗan’adam ba shi da damar gudanar da su ba tare da taimakon iskoki ba. Wannan ya haɗa da:

    1. Rikiɗa zuwa wasu halittu
    2. Ci ko shan wani abu da ya saɓa hankalin al’ada kamar allurai ko ƙaya ko wani ƙarfe ko fasasshiyar kwalba da makamantansu.
    3. Ɓacewa nan take
    4. Sanya wani abu marar motsi motsawa, kamar zabira ko garma/galma da makamantansu.
    5. Bayyanar da wani abu nan take wanda a farko matsafi ba ya tare da shi

    Sai dai yana da kyau a lura da cewa, akwai abubuwan bammamaki makamantan waɗannan da ɗaiɗaikun jama’a ke yi, wanda ya shafi siddabaru ne ba tsafi ba.[5] Matsafa kuwa na amfani da ƙarfin tsafinsu domin kare kai, ko nuna bajinta ko ma cutarwa a wasu lokuta.

    A cikin waƙar Shata ta Hassan Sarkin Dogorai, an ga yadda Shata ya nuna Hassan a matsayin mai waibuwa, inda yake cewa:

    Jagora: Nan na ga al’ajabi, Ranar tafiya Ɗorayi.

    ‘Yan Amshi: Hassan Sarkin Dogarai.

    Jagora: Ran hawa zuwa Ɗorayi.

    Yan Amshi: Hassan Sarkin Dogarai.

     

    Jagora: Ranar hawan Ɗorayi,

    In sarki yah hawo,

    Hassan kuwa ya yo hawa,

    Ko hadari ya taho,

    Ana ta ruwa yaf-da-yaf,

    Hassan ya ja yai gaba,

    Yai gaba sai yats tsaya,

    Na ɗauko doki guje,

    Na zo ciki na rakuɓe,

    Zatona rumfa a kai,

    Wanda sarki zai shiga,

    A ƙasa sai na ga kofatai,

    Kuma na ga idon mutum,

    Sai na ruga guje.

    Nai zaton ifiritu ne,

    Na kwalba

    ‘Yan Amshi: Hassan Sarkin Dogarai.

    Kamar yadda yake cikin ɗiyoyin waƙar da ke sama, tsananin waibuwar Hassan, ruwan sama da ake yi ba ya zuba a daidai wurin da yake tsaye tare da sarki. Wannan ne ma ya sa har Shata yake tunanin ko rumfa ce aka yi a wurin, domin a tare wa sarki ruwan saman, gudun kada ya jiƙe. Sai dai kuma yayin da Shata ya je wurin, sai ya ga kofatai, sannan da idanun mutum a ƙasa. A nan ma za a ga cewa, Shata ya danganta waibuwar Hassan da cuɗanya da aljani. Da ma dai a tunanin Bahaushe, kofoto na ɗaya daga cikin siffofin aljannu.

    A waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas, Shata ya sake bayyana waibuwar Malam Babba, inda yake nuna cewa, yayin da shi Malam Babba ya yi duba, sannan ya faɗi sakamakon; to kuwa abin zai kasance tamkar yana wurin aka shirya. Ke nan dai Shata na nufin cewa, Malam Babba yana iya faɗin abin da zai faru. Ya ce:

    Jagora: Malam na ga kana yin yaushi,

    Je ka Babba ya duba maka.

    Ya zana ƙasa ya duba maka…

    Ya ɗaga kai ya shaida maka,

    Ka ga kamar da shi ne akai.

    ‘Yan Amshi:    Malam Babba na Ƙofar Gabas.

    A wata waƙa mai suna: Mamman Sakkwato Kyaftin, Shata ya nuna yadda Kyaftin Mamman ke da waibuwa, musamman a daji. Waibuwar tasa har ta kai matsayin da, ko da mutum ya san shi, to idan ya kalle shi a daji, zai ga ya zama wani abin tsoro, wanda ba siffar mutane ba. Irin wannan waibuwa ta filin daga kuwa, ba sabon al’amari ba ne ga tunanin Bahaushe. Ma’ana, yana ɗaya daga cikin abin da Bahaushe ya yi amanna da su. Shata ya ce:

    Jagora: Ko ka san shi mutum kauce mashi,

    Kiyayi Mamman Sakkwato daji …

    Ya ce min, Shata mai waƙa,

    Sarkin waƙa,

    Lallai a daji Sakkwato Kyaftin,

    Wannan abin tsoro ya koma.

    ‘Yan Amshi: Sannu Mamman Sakwkato Kyaftin.

    4.4 Tubalin Magani

    Magani dai na nufin duk wani abin da ake amfani da shi domin samun waraka daga wata cuta. Bunza, (1995) ya nuna cewa, magani ga Bahaushen tunani na iya kasancewa sassaƙe ne ko saiwa ko ruwa ko allura ko ma wasu hanyoyin riga-kafi na daban. Tarihin Hausawa na ƙunshe da wasu hanyoyin waraka da Hausawan suka yi amfani da su, waɗanda suka haɗa da bori da ma sauran hanyoyin hulɗa da aljannu domin samun magani.

    Sai dai kuma yana da kyau a tuna, dalilan da kan sa Bahaushe ya nemi magani ba ciwon jiki ba ne kawai, har ma da na zuciya. Bahaushe kan nemi magani domin neman waraka ko kariya ko ɗaukaka da buwaya ko ma domin cutar da abokin gaba (Bunza, 1995; Sarkin Sudan, 2008; Gobir, 2012). Ke nan dai kalmar ‘magani’ na da faffaɗar ma’ana ga Bahaushen tunani.

    A cikin waƙar Mamman Sakkwato Kyaftin, Shata ya bayyana Mamman a matsayin mai waibuwar magani a filin daga. Waibuwarsa ta sanya, ko da ana musayar wuta, harsashe na zirya, to shi ba ya kwantawa ko ya duƙa domin gudun kada harsashi ya same shi. A maimakon haka, zai ci gaba da kutsawa ne kawai riƙe da sandarsa. Ke nan dai Shata na nuna Mamman a matsayin wanda yake da maganin harsashi. Ya ce:

    Jagora: In dai an ce bakin daga,

    Muddin an je bakin fama,

    Ga harsashi na warici,

    Ga harsashi na yawo nai,

    Malam Mamman Sakkwato Kyaftin,

    Bai kwantawa,

    Bai duƙawa,

    Ya riƙe sanda,

    Kui gaba yaran Sakkwato Mamman.

    ‘Yan Amshi:    Sannu Mamman Sakwkato Kyaftin.

    Akwai mawaƙa da dama da suka kawo irin wannan yanayi inda mutum ke amfani da waibuwar magani. Misali Gambu mai waƙar ɓarayi ya kawo irin wannan waibuwa cikin waƙar Jibril Mugun Tsoho inda yake cewa:

    Jagora: Sai ga Hausawa irinmu,

    Ihu ɓarawo,

    Nic ce, an yi ɓarna,

    Wanga bawa ba kaiwa zai ba,

    Tun wada na hanga hakan ga,

    Sai yana tahiya tai yanga-yanga,

    Ba mai jiha ko bugawa,

    Sai dai nuni sai a ɓatai.

    A nan Gambo ya kawo labarin inda aka yi wa ɓarawo ihu domin a kama shi. Sai dai saboda tsabar waibuwar ɓarawon (magani), sai kowa ya kasa kaiwa gare shi, ballantana har a samu wanda zai doke shi. A maimakon haka, sai shi ɓarawon ya ci gaba da tafiyarsa cikin yanga. Duk dai wannan na nuni ga waibuwar Bahaushe a ɓangaren magani.

    4.0 Kammalawa

    Nazarin ya lura da cewa, a lokuta da dama Bahaushe na danganta ɗaukaka da buwaya da kuma cuɗanya da aljani. A tunaninsa, hulɗa da aljani hanya ce mafi sauƙi na samun buwaya. Wannan ne ma ya sanya, mawaƙa da dama ke amfani da waibuwa a matsayin tubalin ginin saƙonnin waƙoƙinsu. Kamar dai yadda Shata ya yi amfani da waibuwa a matsayin dalilin samuwar jarumta da magani.

    Mawaƙa na ba wa mutum wata ɗabi’ar aljani domin ɗaukaka buwayarsa da kambama shi da fito da shahara da gagararsa a fili. Lura da misalan da suka gabata daga cikin waƙoƙin Shata inda ya yi amfani da waibuwa a matsayin manyan tubalan ginin kambamar zulaƙe da jarumta da ma magani; za a iya cewa a tunanin Shata, ƙololuwar buwaya da za a iya ba wa mutum shi ne a danganta shi da aljani. Wannan bai rasa nasaba da yanda aljani yake a tunanin Bahaushe, wanda hatsabibanci da buwaya na samuwa ta hanyar ta’ammuli da shi. 

    Manazarta

    A’azamiyun, W. (1962). Sha’irul Islami: Hassan Bin Sabit Al’ansari. Alkahira: Madaniyyun.

    Abdlƙadir, D. (1975). The Role of an Oral Suɓey in Hausa/Fulani Society. Unpublished Ph. D. Thesis Bloonimgton, Indiana Uniɓiɓersity, USA.

    Abdullahi, I.S.S. (2008). “Jiya ba Yau ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto.

    Abdullahi, S. M. (2017). “Kuɗi A Idan Mawaƙan Hausa Na Baka Da Rubutattu, Waƙar Kuɗi Ta Alhaji Audu Wazirin Ɗanduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja” Kundin digiri na farko da aka gabatar a Sashen Harunan Nijeriya, Jami’ar Usamnu Ɗanfodiyo Sakkwato

    Ahmad, A. (2010). Figure of speech and idiomatic eɗpressions. In Mastering the Basics of English Language. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press Limited.

    Amaechi, M. I. (2010). Comprehensiɓe Literature in English for senior secondary schools. Lagos: A. Johnson Publishers LTD.

    Becker, S. W. & Eagly, A. H. (2004). The heroism of women and men. In American Psychologist Ɓol. 59. Pp 163-178.

    Bello, S. da wasu (eds) (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press Limited.

    Birnin-Tudu, S. Y. (2002). Jigon salon rubutattun waƙoƙin fura’u an ƙarni na ashirin. A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto.

    Bunza, A. M. (1988). “Nason Kirari Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na 20.” Maƙalar da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Bunza, A. M. (1995). Magungunan Hausa a rubuce: Nazarin gudummuwar ayyukan malaman tsibbu. A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity, Kano.

    Bunza, A. M. (2015). Hyperbole as the Peak of Stylistic Adornment in the Hausa Oral Songs. Being a lead paper presented at the 3rd Annual Conference and 12th NFS Congress organized by Nigerian Folkloric Society, Center for Research in Nigerian Languages and Folklore, Bayero Uniɓersity, Kano, with the theme: Oral Poetry In Nigeria: Prospects And Challenges In The 21st Century, Monday, October 26th – 27th, 2015 at Musa Abdullahi Auditorium, Bayero Uniɓersity, Kano.

    Dangambo, A. (1973). “Shata da waƙoƙinsa. An undergraduate project submitted to the Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity, Kano.

    Douglas, M. S. & Mathew, C. (2012). Heroism and risk of harm. In Psychology Ɓol. 13, No. 12S, pp. 1080-1090

    Fitry, I. (2010). A figuratiɓe language analysis on Sylɓia Plath poems. Retrieɓed on 30th June 2017, from: repository.uinjkt.ac.id/dspace

    Franco, Z. E., Blau, K. & Zimbardo, P. G. (2011). Heroism: A conceptual analysis and differentiation between heroic action and altruism. In Reɓiew of General Psychology. Doi: 10.1037/90022672, pp. 99-113.

    Furnish, G. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. London: Edinburgh Uniɓersity Press.

    Gobir, Y. A. (2009). Tasirin Iskoki a Cikin Waƙoƙin Sata: Nazari Daga Waƙoƙin Gambo Mai Waƙar Ɓarayi. Takardar da aka gabatar a taron }ara wa juna sani a kan “Tubar Gambo daga Wa}o}in Sata”, wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato ta shirya, Asabar, 28 ga Fabrairu, 2009.

    Gobir, Y. A. (2012). Tasirin iskoki ga cututtuka da magungunan Hausawa. A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto.

    Gusau, S. M. (1996). Makaɗ a da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

    Gusau, S. M. (2003). Jagora Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers.

    Gusau, S. M. (2003). Waƙoƙin Alhaji Mamman Shata, Diwani na Ɗaya (ed). Bugawar Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu ta Katsina. Katsina: Goɓernment Printing Press.

    Habibu, L. (2001). “Bunƙasar Rubutattun Waƙoƙin Hausa a Ƙarni na Ashirin (20).” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

    Habibu, L. (2001). Gudummuwar finafinan Hausa a ƙarni na ashirin (20). An undergraduate project submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto.

    Kankara, A. I. (2013). Mahadi mai Dogon Zamani: Shata da kundin waƙoƙinsa. Kaduna: Labson Prorduction.

    Maiyama, U. H. (2008). Sata a zamantakewar Hausawa: Nazarin waƙoƙin ɓarayi na Muhammadu Gambo Faraga. Kundin digiri na uku wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Marriam Webster, (2017). Sorcery. Retrieɓed on 8th July 2017 from; www.marriam-webster.com/dictionary/sorcery

    Melony, A. (1999). Preference ratings of images representing archetypal themes: An empirical study of the concepts of archetypes. In Journal of Analytical Psychology, Ɓol. 44. Pp 101-116.

    Omosowane, J. O. & Nelson, A. A. (2003). Comprehensiɓe English language for senior secondary schools. Lagos: A. Johnson Publishers LTD.

    Ƙaura, H. I. (1994). “Ƙawancen Salo a Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa.” Kundin kammala digiri na biyu (M.A.) wanda a aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

    Samaram, G. (2008). Witchcraft and sorcery: Social and medical perspectiɓe. Retriɓed on 8th July 2017 from http.atheistcenter.in/pdfs

    Sani, A-U. & Tsaure, M. B. (2016). An Image of Northern Nigeria’s Marital and Gender-based Controɓersies: A Surɓey of Abubakar Gimba’s Sacred Apples. Being a paper presented at the 13th International Conference on Ethnic Nationalities, Cultural Memory and the Challenges of Nationhood in 21st Century Literature, held at The Uniɓersity Auditorium, IBB Uniɓersity, Lapai, from 30th August to 2nd September 2016.

    Sani, A-U. (2016). Hausa Literature Beckons National Integration: An Insight Into Waƙar Haɗin Kan Afirka by Abubakar Ladan Zariya. Being a paper presented at the 1st National Conference of Faculty of Arts and Islamic Studies on the Role of Language, History and Religion, in the Deɓelopment, Integration and Security in Nigeria, held at Uniɓersity Auditorium Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto, between 1st to 3rd March, 2016

    Science Daily, (2014). Culture Influences Young People’s Self-esteem: Fulfillment of ɓalue priorities of other indiɓiduals important to Youth. Retrieɓed on 21st June, 2017 from www.sciencedaily.com

    Sheme, I., Ƙanƙara, A. I., Albasu, T. Y., Kano, A. M. (2000).  Shata Ikon Allah. Kaduna: Espee Publications

    Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Serɓice.

    ‘Yar’aduwa, T. M. (2010). Jagoran Nazarin Rubutaccen Adabin Hausa. Ibadan: HEBN publishers PLC.

    Zurmi, A. D. (2006). “Tsoratarwa a Cikin Waƙoƙin Wa’azi na Nana Asma’u.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

    [1] A ƙoƙarinsa na ba da misalin kambamar zulaƙe, Bunza, (2015) ya rawaito Muhammadu Sani Ɗanbolɗo a waƙarsa ta Zaura, inda yake kambamar zulaƙe yayin yaba siffar wata mace. Yana cewa:

    Farar fatat ta ka ruɗa ni

    Dun nar rice

    Tsawon hancinta misali nai

    Ya kai mil goma misalin dogon hanci.

    (Muhammad Sani Ɗanbloɗo: Waƙar Zaura)

    Da ma dai, Bahaushe ya ɗauki dogon hanci a matsayin babban abu wajen nuna kyawun mace. Domin fito da tsawon hancin matar da Sani yake yi wa waƙa fili, sai ya yi amfani da kambamar zulaƙe, inda yake nuna ai tsawon nasa ya kai har mil goma (Da a magana ce ta yau da kullum, sai a ce zuge ta malle!).

    [2] Hasan Sarkin Dogarai wani dogari ne da aka taɓa yi a fadar Kano, wanda ya yi zamani da Sarkin Kano Mai Martaba Ado Bayero. Al’umma ta tafi kan cewa, Hasan yana da tsananin waibuwa sosai. Saboda haka, kambamar zulaƙe da Shata ya yi masa, bai rasa nasaba da wannan fahimtar mutane game da Hasan, wato waibuwar da yake da shi.

    [3] Gambu ya yi haka ne domin ya nuna yadda Tsoho Tudu yake da zunzurutun waibuwa, wanda babu wani ɓarawo da ya isa ya masa sata.

    [4] Shago ɗan dambe ne da ya yi matuƙar shahara a ƙasar Hausa. An tabbatar da cewa, sau da dama Shago na kai abokin karawarsa ƙasa da bugu guda kawai.

    [5] Siddabaru dai shi ne amfani da dabara da hikima maɗaukakiya domin aikata wani aikin da zai ɗaure kan masu kallo ko saurare. Sau da dama idan aka yi siddabaru, masu kallo (musamman waɗanda ba su gane dawar garin ba) kan samu wasu-wasi tare da ɗaukar mai siddabaru a matsayin wanda yake da waibuwa ta musamman.

    Danna nan don karanta Maƙala Mai Taken: “Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto”

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ’Yan Matan Fangama

    Tatsuniyar ’Yan Matan Fangama

     Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana ’yan matan Fangama suka shirya za su biki a wani gari da ke kusa da su. Dabarar zuwan ita ce ko za su yi dace kowaccensu ta sami manemi, wata rana a yi nata bikin. Kowacce dai ta ci ado, abin gwanin ban sha’awa. Amma kafin su tafi sai da suka fita bayan gari domin kowacce ta tsinko wa mahaifiyarta goriba.

    Dukkanninsu sun samo goriba, in ban da ɗaya daga cikinsu. Ita ta nema, ta rasa. Shi ne bayan sun koma gida, sai mahaifiyarta ta ce lallai ta koma sai ta samo, in ba haka ba kuwa, ita babu tafiya biki. Ta rasa yadda za ta yi don ƙawayenta sun shirya za su tafi su bar ta.

    Haka dai ta jure ta koma wurin bishiyar goriba, ta roƙe ta. Da bishiyar ta ji bayaninta, sai ta tambaye ta: “Me za ki yi da goribar idan na ba ki?” Yarinya ta ce: “Zan kai wa mahaifiyata saboda ta ba ni kayan da zan sa mu je wani biki aure tare da ƙawayena.” Da jin haka bishiyar ta ce: “Ba zan iya taimakon ki ba, sai in kin roƙi girgije ya sako ruwa in sha.

    Idan na sha sai in zuba ’ya’yan da zan ba ki.” Yarinya ta durƙusa ta roƙi Ubangiji ya sauko da ruwa. Bayan wani ɗan lokaci kuwa sai aka kece da ruwa mai ɗimbin yawa. Goriba ta yi ’ya’ya, yarinya ta tsinka ta kai wa gyatumarta. Nan da nan uwar ta kawo kayan kwalliya da na alatu, masu kyan gaske ta ba ’yarta.

    Amma kuma tuni ƙawayenta cikin gaggawa sun tafi, sun bar ta a baya.Da yake tana cikin ɗoki, ba tare da kasala ba ta kama hanya ita kaɗai, har ta isa wurin bikin. Ta tarar ƙawayen ba su jima da zuwa ba. Samari kuwa sun cika wurin, saboda iyayen ma’auratan sun gayyato mutane da yawa.

    Aka yi ta shagali, suka ɗirki rawa, har suka gaji. Can a lokacin tsarince, sai wani saurayi kyakkyawa wanda ke tashen samu ya kira ta. Suka yi taɗi, ya yaba hankalinta. Daga nan suka shirya aure, da ta koma gida ta sanar da iyayenta, shi maya tura magabatansa gidansu.

    A takaice dai, aka ba shi ita, suka yi aure. Sauran ƙawayenta ma daga baya Allah ya ji kukansu, ɗaya bayan ɗaya suka sami maza, kowacce ta shiga ɗakin miji. Yanzu haka suna can har sun fara hayayyafa, kowacce na zaune lafiya da mijinta. Kuma wani abin ban sha’awa shi ne, har yanzu suna ƙawance da junansu. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai nema yana tare da samu.
    • Ka so wa ɗan’uwanka abin da kake so ga kanka.
    • Biyayya ga iyaye takan kawo wa mutum buɗi da cimma burinsa na rayuwa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Garin Da Ba Maza Sai Mata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Garin Da Ba Maza Sai Mata

    Tatsuniyar Garin Da Ba Maza Sai Mata

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani gari da duk mazaunansa mata ne zalla, watau ba wani namiji ko ɗaya a cikinsu. Su matan a kullum sukan tafi rafi su yi wanka, su kuma ɗauko ruwa. Sai wani mutum daga wani gari mai nisa ya ji labarin wannan ƙauye. Ya ɗaura ɗamara, ya kama hanya da nufin sai ya je wannan gari mai ban mamaki.

    Ya yi tafiya mai nisa a cikin ƙungurmin daji kafin ya isa. Da zuwansa sai ya hangi wasu mata kyawawa suna wanka a rafi. Ya matsa har ya isa kusa da su, ya gama kallon su sarai, ba tare da sun sani ba. Da ya ga ba su gan shi ba, sai ya kwashe tufafinsu da ke dab da bakin kogin nan; ya hau bishiya, ya ɓuya.

    Can da matan suka gama wanka suka fito sai suka ga ba suturarsu. Suka duba nan suka duba can ba su ga kowa ba, suna ta mamakin abin da ya faru. Wasu suna ce ko aikin aljanu ne. Can sai wata daga cikinsu ta leƙa saman wata bishiya sai ta ga mutumin. Ita ce kuma ta fi duk sauran kyau.

    Shi kuma mutumin ɗan saurayi ne mai kyan gaske. Daga nan sai matan suka kama waƙa, suna cewa:

    “Kai saurayin nan, Kai saurayin nan,

    Don Allah ka maido mana da kayanmu nan.

    Kai saurayin nan, Kai saurayin nan,

    Ka ji kunyar mu, Ka dawo mana da kayanmu.”

    Nan da nan ya mayar musu da kayansu, amma banda na waccan mata da ta fi sauran kyau. Ya ce zai ba ta kayanta ne kurum idan ta yi masa waƙa mai daɗi, kuma ta ambaci sunansa. Sai ta yarda. Ta rera waƙar mai daɗi, sai dai ba ta ambaci sunansa ba, saboda ba ta sani ba.

    Shi kuwa ya ƙi ba ta kayan. Yana ta ja mata rai, har rana ta kusa faɗuwa. Da mahaifiyarta ta ga shiru ba ta koma gida ba, sai ta aiki ƙanwarta nemanta. Kanwar na zuwa bakin ruwa sai ta tarar da yayarta zindir, haihuwar uwarta. Tana ganin ƙanwar sai ta ce:

    “Akwai wani kyakkyawan saurayi a wurin nan wanda ya riƙe kayana; ya ce ba zai
    ba ni ba sai na ambaci sunansa.” To da man kanwar hatsabibiyace, sai ta yi wani siddabaru irin nata, ta ji kurum kamar daga sama an gaya mata sunan saurayin nan. Nan take ta sanar da yayarta, tace kuma ta yi wakar ta faɗi sunan ta ga abin mamaki.

    Da ta yi haka sai saurayi ya mayar mata da kayanta; ya sauko daga kan bishiyar;
    ya ɗora ta tare da ƙanwar a kan doki; ya karya linzami, ba su zame ko’ina ba sai a ƙofar gidan su yarinyar. Gyatumarsu da maƙwabta suka yi ta mamakin ganin namiji a garin saboda duk tsawon rayuwarsu ba wadda ta taɓa ganin namiji.

    Ba tare da ɓata lokaci ba mutumin ya nemi yarinyar da aure, aka ba shi. Aka yi aure da babban biki mai ƙayatarwa. Bayan can ya sami wuri ya gina gida mai ƙayatarwa a garin, shi da matarsa suka zama abin kallo, ba a zancen komai sai nasu. Bayan ’yan shekaru suka haifi ’ya’ya maza biyu.

    Wata rana mutumin ya ce zai je ganin gida, amma tare da ɗaya daga cikin ’ya’yan. Uwar ta ce su dawo lafiya. Suka je, suka komo. Bayan an kwana biyu mutumin ya ce zai sake ziyartar garinsu, amma a wannan karo yana so ya je tare da ’ya’yan duka, domin ya nuna wa danginsa su baki ɗaya.

    Wannan buƙata ta mutumin ta tayar da hankalin duk matan garin. Amma mahaifiyarsu, ta dage a kan cewa a bar mijin ya yi haka. Da mutumin ya je garinsu, sai ya yi zamansa, bai koma ba. Matar ta yi ta kuka saboda rashin ganin ’ya’yanta. Bugu da ƙari mutumin ya aiko da saƙo cewa ya saki matar.

    Bayan wani lokaci Ubangiji ya share mata hawaye. Wani ɗan Sarki daga wata ƙasa ya je garin, ya neme ta da aure, ta yarda aka ɗaura musu aure aka yi babban biki. Suna nan zaune, har ɗan Sarki ya gaji sarautar gidansu. Ba a jima ba shi ma ya rasu, ɗan da suka haifa da matar ya gaje shi.

    Ita kuma Allah ya ba ta tsawon rai, ta zauna tare da ɗanta cikin ni’ima. Waɗancan ’ya’yan nata na farko su ma sun zo sun girma suka matsa wa mahaifinsu ya bar su suna zuwa a kai a kai suna gaishe su ana musu alfarma. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wani hani ga Allah baiwa ne.
    • Soyayya gamon jini.
    • Mai haƙuri yakan dafa dutse.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Kanta Da Mugayen Abokananta

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kanta Da Mugayen Abokananta

    Tatsuniyar Kanta Da Mugayen Abokananta

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wasu ’yan mata su goma sha biyu ƙawaye. A cikinsu har da wata ’yar Sarki mai suna Kanta. Ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta. Ita ce kuma ta fi kyau a tsakanin duk ’yan matan garin. Kowane saurayi a garin yana so ya aure ta, amma ta ƙi. A cikin waɗanda suke son ta har da wani maciji wanda ke zaune a cikin kogin da ke kusa da ƙauyen.

    Sauran ’yan matan suna kishin Kanta saboda farin jininta da kyauta. Saboda haka suka haɗa baki cewa za su ja ta zuwa kogin nan domin su kashe ta. Mahaifiyar Kanta ta gane duk ƙulle-ƙullen da ’yan matan suke yi game da ’yarta, saboda haka ta yi ta ƙoƙari ta kare ta.

    Duk lokacin da ’yan matan suka zo neman Kanta, sai ta ce da su ba ta nan. Wata rana sai uwar Kanta ta tafi wata unguwa ziyara. Ganin haka ’yan matan nan suka je har cikin gidan Sarki suka ja hankalin Kanta har ta amince za ta bi su kogin nan. Ta bi su da sunan kamun kifi za su.

    Da suka isa kogin, sai suka ga wani mangwaro mai ’ya’ya, kuma suka yanke shawara za su hau domin su tsinki na sha. Kanta ta ƙi hawa, amma suka matsa mata, har dai ta hau. Kowaccensu ta roƙi Kanta da ta tsinko mata mangwaro. Macijin da ke kogin nan ya ji hayaniya ta yi yawa, sai ya fito.

    Ya nufi inda ’yan matan nan suke. Da suka gan shi suka gudu, suka bar Kanta a sama. Macijin ya hau itacen ya same ta. Can daga baya ’yan matan suka koma wajenta, suka ga halin da take ciki. Da suka iso sai suka kama waƙa, suna cewa:

    “Kai macijin nan don Allah,

    Ka sassauta wa Kanta ta sauko,

    Kai macijin nan don Allah,

    Ka sassauta wa ƙawarmu Kanta ta sauko.”

    Kanta kuwa sai hankalinta ya tashi. Da mahaifiyarta ta dawo ba ta gan ta a gida ba, sai ta shiga nemanta. Ta shiga nan ta shiga can har dare ya yi ba ta gan ta ba. Ƙawayen Kanta kuwa suka koma gida dab da almuru, suka baro ta a kan mangwaron nan na bakin kogi.

    Allah da ikonsa sai ga wani ɗan tsuntsu fari ya zo ya sauka kusa da Kanta; sai ta roƙe shi, ta ce: “Kai ɗan farin tsuntsun nan, don Allah ka taimake ni ka kai saƙona ga iyayena. Babana shi ne Sarkin garin. Ka gaya musu cewa ina cikin matsala. Ƙawayena duk sun gudu sun bar ni da wani maciji wanda yake so ya haɗiye ni.

    Ina nema su kawo mini gudunmawa da wuri don su kuɓutar da ni daga wannan matsala.” Ɗan tsuntsu ya yarda; ya tashi sai fadar Sarki. Da ya isa gaban Sarki sai ya ce: “Mai martaba, na zo ne in ba ka saƙo daga ’yarka.” Da jin haka sai mamaki ya kama Sarki da matarsa.

    A gigice Sarki ya ce da ɗan tsuntsu: “Yi maza ka gaya mana saƙon.” Ɗan tsuntsu ya ce: “Mai martaba, ’yarka ce tana can dogon daji; tana kan wata babbar bishiyar mangwaro, kuma wani babban maciji ya kusa ya haɗiye ta.” Da jin haka, ba tare da ɓata lokaci ba Sarki ya tattara dogarawansa suka tafi ɗan tsuntsu na nuna musu hanya.

    Da suka isa sai suka tarar macijin ya fara barci. Ba tare da yin wani motsi da zai farkar da maciji ba, suka ce ɗan tsuntsu ya yi ƙoƙari ya goyo Kanta, ya sauko da ita. Ɗantsuntsu ya je wajen Kanta ya gaya mata zai goye ta. Ya juya baya ta ɗare, ya tashi fir, yana nishi, da ƙyar ya kai ta fada.

    Dogarai suka sulale, suka bar maciji na barci, suka isa fada lafiya. Washe-gari Sarki ya sa a kirawo duk ƙawayen ’yarsa. Suka zo fada. Da aka bayyana duk abubuwan da suka faru, sai ƙawayen Kanta suka tuba, tare da yin alƙawari ba za su sake yin irin wannan abu ba har abada.

    Suka roƙi Sarki ya yafe musu. Sarki ya yarda, ya yi musu afuwa. Ya kuma sa wasu samari su auri ’yan matan. Aka yi babban biki a fadar Sarki. Har yanzu waɗanda suka san an yi wannan biki sukan ce ba su taɓa ganin biki mai armashi da ƙayatarwa kamarsa ba.

    Amma fa wani abu shi ne, duk da shagalin da aka yi lokacin bikin nan cikin farin ciki, Sarki bai huce baƙi ɗaya ba; sai da yasa aka je aka kashe macijin nan. Zaratan da suka kashe macijin suka ɗauko mushensa suka kai fada. Maciji ne mai tsawon gaske, kuma ba wanda ya taɓa ganin irinsa a ƙauyen.

    An ce ya halaka wasu daga cikin zaratan da Sarki ya tura suka kashe shi. Sarki ya yi wa waɗanda suka mutu wajen kashe macijin alheri, wanda aka ba iyalansu, kuma waɗanda suka dawo lafiya daga cikinsu ya yi wa kowannensu aure. Mutanen garin kan yi bikin tunawa da waɗanda suka rasu saboda bajintar da suka yi. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Ba a rama kirki da mugunta.
    • Kowa ya ci amana sai amana ta ci shi.
    • Wayo ya kada sarkinsa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta tatsuniyar Tatsuniyar Dila Da Zomo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken: “Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto”

    Maƙala Mai Taken: “Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto”

    “Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto”: Taliyon Dangantakar Adabi da Al’ada

     Abu-Ubaida Sani

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng

    WhatsApp: +2348133529736

                                                             And

     Dr. Adamu rabi’u bakura

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: arbakura62@gmail.com

    Phone: 08064893336

     Article Citation: Sani, A-U. & Bakura, A.R. (2024). Zamo mini tubali in zam miki hoto: Taliyon dangantakar adabi da al’ada. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 319-327. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.040.

     Tsakure

    Manufar wannan bincike shi ne gano nau’in alaƙar da ke tsakanin adabi da al’ada. An zaɓi yin amfani da tsararren salon zaɓar samfuri na wa-ta-gangano (stratified random sampling) domin tabbatar da cewa ba a ɗauki samfurin al’adu da ake kallo ko aka san da zamansu cikin adabi ba kawai. An ɗora aikin kan falsafar Hausawa da ke tunanin cewa hulɗa na kasancewa ne cikin tsarin cuɗe ni in cuɗe ka.

    A bisa wannan ne binciken ke hasashen cewa, adabi na da bazar takawa wajen bayyana hoton al’adu kamar yadda al’ada ke da rawar takawa wajen kasancewa tubalan gina adabi. Sakamakon binciken ya tabbatar da wannan hasashe inda ya kasance an samu dukkannin samfuran al’adu da aka ɗauka a cikin ɓangarorin adabin baka. Ta la’akari da wannan ne daga ƙarshe binciken ya ba da shawarar ƙara faɗaɗa bincike kan tasirin adabi a kan al’ada da kuma na al’ada a kan adabi.

    Fitilun Kalmomi: al’ada, adabi, matakan rayuwa, bayyanannun al’adu, ɓoyayyun al’adu

    1.0 Gabatarwa

    “Al’ada” ba baƙuwar kalma ba ce ga kunnuwa da bakunan Hausawa. A kullum Hausawa na amfani da kalmar a bagire mabambanta bisa ma’anoni masu kama da juna waɗanda ba a rabe su da sababben al’amari ko sananniyar hanyar gudanar da lamura. Rubuce-rubuce masu tarin yawa da masana suka gudanar game da al’adun Hausawa na ƙara nuni ga kasancewar kalmar fitacciya da ba ta buƙatar wani dogon sharhi.

    Kalmar al’ada ta ratsa ayyukan masana da manazarta irin su Mustapha, (2003) da Najahu, (2018) da Bunza, (2019) da Abdullahi, (2021). Yayin da aka nazarci waɗannan rubuce-rubuce da makamantansu, za a tarar da cewa al’ada na nufin tsarin rayuwa ta gaba ɗaya wadda ta haɗa da sanannun sababbun al’amuran da ke gudana yau da kullu bisa wasu tsararrun ƙa’idoji da matakai da kuma waɗanda aka saba da wanzuwarsu kara zube ba tare da ƙa’ida ta musamman ba.

    A ɓangare guda kuwa, ayyukan da aka yi game da adabi sun fi shurin masaƙi. Wani abin burgewa shi ne, ba a samu saɓanin ra’ayi ba game da bayanin adabi a matsayin madubi ko hoton da ke bayyana rayuwar al’umma.[1] A farfajiyar Hausa da Hausawa, ana iya cewa adabi na nufin fasahohi da hikimomi na ƙirƙira da zalaƙa da ƙwarewar sarrafa harshe da luguden kalmomin fasaha da ke kasancewa cikin salo-salo da siga-siga na labartawa ko rerawa ko ambatawa ko samar da sautin da ke isar da manufa da ba da ma’ana ta musamman, waɗanda ke nuna hoton zuci na rayuwar al’umma na gaba ɗaya, ciki har da bayyanannu da ɓoyayyun al’adunsu.

    Wannan takarda ba ta kasance ta farko ba a wannan bagire na nazartar dangantakar al’ada da adabi. Sai dai mafi yawan ayyukan da aka gudanar a baya game da wannan batu suna da taƙaitattun kadada. Yawanci sukan ɗauki waɗansu keɓantattun al’adu ne domin nazartar yadda hotunansu suka bayyana cikin adabi, ko su ɗauki keɓantattun fannonin adabi domin nazarin wata al’ada ko wasu al’adun da suka ratsa cikinsu.

    Za a tarar da misalan hakan cikin ayyukan Yahya, (2001) da Mustapha, (2003) da Yahya, (2013) da  Sarkin Gulbi, (2014) da Buba, (2016) da Najahu, (2018) da Bunza, (2019) da Abdullahi, (2021) da makamantansu. Maƙasudin wannan bincike kuwa shi ne (i) gudanar da nazarin ƙwaƙƙwafi don gano ko al’adu ne tubalan gina kowane nau’in adabi, da (ii) gudanar da nazarin ƙwaƙƙafi don gano ko ana iya ƙyallaro dukkannin nau’ukan al’adu daga cikin madubin adabi?

    1.1 Dabarun gudanar da bincike

    Wannan bincike ya shafi al’adun Hausawa ne a kadadar adabin baka. An bar kadadar wannan bincike a buɗe. Ba a taƙaita ta ta fuskar ayyana taƙamaimai nau’ukan al’adu ko fannonin adabin baka da za a nazarta ba. Rashin taƙaita kadadar ne zai tabbatar da nazarin ya binciko abin aka ƙudurta tare da tabbatarwa, ko kuma kore hasashen da binciken ya yi.

    A ƙoƙarin cimma maƙasudin wannan bincike, an duba samfurin al’adun Hausawa a cikin adabin bakansu. Wannan ya shafi (i) bayyanannun al’adu da (ii) ɓoyayyun al’adu da (iii) matakan rayuwa.[2] Kasancewar al’adun Hausawa suna da matuƙar yawa, an ware samfurin da ya wakilci saura.

    An yi amfani da tsararren salon zaɓar samfuri na wa-ta-gangano (stratified random sampling). An bi abajadi a matsayin ma’aunin rukunonin (strata) samfurin, inda aka ɗauki ɗaya daga (1) cikin kowane rukunin abajadi biyu (2), na farko da na ƙarshe. Bisa bin waɗannan matakai da alƙaluma ne aka samu samfuri kamar haka:

    Jad. na 1: Samfurin bincike

    Matakan Rayuwa   Zaɓaɓɓen Samfuri
    Lamba Matakan Rayuwa   Rukuni Bayyanannun Al’adu Ɓoyayyun Al’adu
    1 Aure A Abinci Amana
    2 Haihuwa Z Zani Zumunci
    3 Mutuwa

    Madogara: Tsararren salon zaɓar samfuri na wa-ta-gangano

    Domin cimma hasashen binciken, ba a keɓance waɗansu rukunonin adabin baka ba domin gudanar da nazarin.[3] An yi ƙoƙarin taƙaita nazarin ta hanyar ɗaukar abubuwan da suka zo ƙarƙashin Jadawali na 1 da ke ƙasan 1.1 domin duba misalansu daga cikin fannonin adabin baka da hannu ya fara kaiwa gare su.

    1.2 Ra’in bincike

    Wannan nazari ya shafi adabi da al’adun Hausawa ne tsurarsu. Hakan ya sa ba a tafi neman na dawa ba alhali na hannu bai kai gida ba, kamar yadda Bunza, (2019 p. 721) ya yi wannan jan hankali. Ko ba komai, mai ɗaki shi ya san inda ke masa yoyo. Hakan ya sa aka sakar wa waɗannan manyan fagage na adabi da al’ada mara domin su yi tuwona-maina ta fuskar zaƙulo hanyar ɗora aiki da ta dace da tunanin Hausawa kan batun da ake magana a kai.

    An ɗora wannan nazari kan fahimtar Hausawa cewa “lamarin zaman duniya cuɗe ni ne, in cuɗe ka.” A bisa wannan tunani, ana sa ran duk wani abu ko wani lamari da ya cuɗanya da wani abu na daban, to wancan abin shi ma ya cuɗanya da shi ta waɗansu fuskoki, ko dai kai tsaye ko a kaikaice. A fahimtar wannan ra’ayi, binciken yana da hasashen cewa al’adu su ne tubalen ginin kowane nau’in adabi. A ɓangare guda kuwa, adabi madubi ne da cikinsa za a iya hango dukkannin nau’ukan al’adu.

    2.0 Bitar Dangantakar Adabi Da Al’ada

    Al’ada da adabi ɓangarorin rayuwa ne guda biyu da ke tafiya hannu da hannu. Suna zama ne irin na cuɗe ni, in cuɗe ka, ko na ba ni gishiri, in ba ka manda. Za a iya tabbatar da hakan cikin ayyuka daban-daban da suka gabata da ke nuna cuɗeɗeniyar waɗansu al’adu da ɓangarorin adabi. Daga ciki akwai ayyukan Abdullahi, (2000) da Muhammad, (2008) da Atuwo, (2009), Giwa, (2012), Bunza, (2013), da Musa, (2019) da Abdullahi, (2021) da waɗansu masu tarin yawa.

    Babu wani nau’in adabi da al’adu ba su kasance tubalan gidan shi ba. Haka kuma, babu wata al’ada da ba ta da gurbi cikin adabi. An ga yadda Abdullahi, (2000) ya hasko hotunan magunguna da siddabarun Hausawa a cikin ƙagaggun labarai. Aikin Haliru, (2018) ya nuna yadda ake samun nason yaƙi cikin adabi.[4] Bunza, (2019) kuwa ya hasko yadda ƙwarya ta ratsa adabin bakan Bahaushe.  A aikin Abdullahi, (2021) kuwa, an ga yadda doki ya fito a nau’ukan adabin bakan Bahaushe, musamman labaru da karin magana. Waɗannan da makamantansu suna daga cikin dalilan da suka ƙarfafa hasashen wannan bincike na cewa al’ada da adabi na tafiya ne hannu da hannu.

    3.1 Matakan Rayuwar Hausawa A Cikin Adabin Baka

    Matakan rayuwa na nufin waɗansu muhamman gaɓoɓi ko zanguna da rayuwar ɗan’adam ke ratsawa ta cikinsu, waɗanda ke dabaibaiye da al’adu daban-daban masu sauyawa daga lokaci zuwa lokaci sakamakon yanayi da sauyin zamani da kuma tasirin baƙin al’ummu. Manyan matakan rayuwa su ne (i) aure da (ii) haihuwa da (iii) mutuwa. Wannan ɓangare na aikin ya mayar da hankali kan zawarcin matakan rayuwar Hausawa cikin adabin baka.

    3.1.1 Aure

    A tunanin Hausawan ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21), ana iya cewa aure na nufin wata yarjejeniya ta musamman da ake ƙullawa tsakanin namiji da mace, bisa wasu sharuɗa da ƙa’idoji da suka fara tun daga nema har zuwa ɗaurawa da tarewa da abubuwan da ke biyo baya da suka shafi zamantakewa a matsayin miji da mata, bisa waɗansu ƙayyadaddun tanade-tanaden al’ada da addini. Wannan muhimmin mataki cikin matakan rayuwar Hausawa ya mamaye adabin baka.

    Tatsuniyoyin[5] Hausa da dama an gina su kan wannan jigo na aure ko dai a matsayin babban jigo da ya mamaye tatsuniyar, ko kuma ƙaramin jigo a cikinta. A tatsuniyar ‘Yar Bora da ‘Yar Mowa, an ga yadda auren ɗan sarki ya kasance sakamako mai kyau ga ‘Yar Mowa. Mummunan aure kuwa ya kasance sakamako marar kyau ga ‘Yar Bowa. A tatsuniyar Icen Ƙosai ma, an ga yadda auren ɗan sarki ya kasance sakamako nagari ga ‘yar kishiyar da ta sha baƙar wuya a wurin kishiyar uwarta.[6]

    A ɓangare guda kuwa, duniyar karin maganar Hausa na cike da batun aure. Waɗansu daga cikin karin maganganu da suka shafi aure da ake yawan ji a bakin Hausawa sun haɗa da:

    1. Aure ba ka da malam
    2. Ba haka aka so ba, ƙanin miji ya fi miji kyau
    3. Ƙarya ba ta sa amarya lalle.
    4. Ƙoshin takaba aure da mai ƙararren kwana
    5. Larura auren namiji da ‘ya’ya
    6. Matar na-gode, ba ta rasa mijin aure[7]

    3.1.2 Haihuwa

    Haihuwa na nufin fitar wani abu mai rai daga jikin wani abu mai rai bayan saduwa tsakanin mace da namiji, wanda yawanci abin da ya fita na kama da waɗanda suka samar da shi a bayyane kamar ta fuskar launi ko zubi da tsari, ko kuma a ɓoye kamar ta fuskar ƙwayoyin halitta da halayya da ɗabi’u. Haƙiƙa jigon haihuwa ya karaɗe adabin bakan Hausawa. Wannan ɓangaren nazarin ya kawo ‘yan misalai.

    A cikin almarar Ɗan Zaki da Ɗan Mutum, an ga yadda tun farko aka gina ta kan mace mai ciki da ke shirin haihuwa. A ɓangare guda kuwa, sai aka koma kan zakanya da ita ma ke shirin haihuwa. Daga nan almarar ta ci gaba da ginuwa a kan Ɗan Mutum da Ɗan Zaki, har zuwa girmansu da gwagwarmayar rayuwarsu.[8]

    A ɓangare guda kuwa, ɗaya daga cikin ƙissoshin[9] da suka kama bakin Hausawa shi ne na wani hukuncin hikima da Annabi Sulaiman ya yanke game da haihuwar wani jariri. Mata biyu sun kafa gardama inda kowa ta ƙeƙashe ƙasa cewa ita ta haifi jaririn. Duk ƙoƙarin duniyan nan da Annabi Sulaiman zai yi don gano asalin mahaifiyar ya faskara. Daga ƙarshe ya ce a samo zarto a raba jaririn gida biyu, kowace mata a ba ta rabi.

    Nan fa ɗaya daga cikin matan ta ce ita ta haƙura, a ba wa ɗaya matar jaririn ta tafi da shi. Bisa wannan ne kuma Annabi Sulaiman ya ce lallai jariri na wacce ta haƙura ɗin ne, domin sanin zafin haihuwarsa da soyayyar da take masa ya sa ba za ta bari a yi masa haka ba. Wannan na nuni ga matsayin haihuwa tare da dangantaka da shauƙi da tausayi da ke tsakanin abin da aka haifa da mahaifansa.

    3.1.3 Mutuwa

    Mutuwa na nufin gushewar rai daga ganganr jiki da ake iya tabbatarwa ta la’akari da manya da ƙananan alamomi da suka haɗa da daina motsi da sandarewar jiki da kafewar idanu da ɗaukewar numfashi da tsayawar bugun zuciya na tsawon lokacin da ya zarce suma a sababbiyar al’adar tsarin halittar ɗan’adam. Tsattsafin mutuwa ya ratsa ɓangarori daban-daban na adabin bakan Hausawa.

    A ɓangaren labarai[10] ma, ana iya tsintar matakan rayuwar Hausawa, ciki har da lamarin mutuwa. A labarin Shehu Jaha da Wani Malami,[11] an ga yadda lamarin mutuwa ya bayyana. Babu abin da Shehu Jaha ya buƙata sai a sanar da shi ranar da zai mutu.

    3.2 Bayyanannun Al’adun Hausawa Cikin Adabin Baka

    Bayyananniyar al’ada ita ce duk wata nau’in al’adar da idanu ke iya gani ko hannu ke iya taɓawa. Ta fi shafar ƙere-ƙere da sauran sarrafe-sarrafen al’umma da suka haɗa da abinci da gine-gine da sutura da zane-zane da duk sauran nau’ukan kayan al’ada da ba su ɓoye wa idanun ɗan’adam ba, ciki har da abubuwan da suke samammu ko wanzazzu a muhallan al’umma. Tsattsafin bayyanannun al’adun sun mamaye duniyar adabin bakan Hausawa. Wannan ɓangaren nazarin ya kawo misalai da ke tabbatar da hakan.

    3.2.1 Abinci

    Abinci shi ne duk wani abin da al’ada ta ɗauka a matsayin marar illatarwa da ake sa wa a baki, a tauna, a haɗiye domin kawar da yunwa ko marmari. Yayin da aka leƙa adabin bakan Hausawa, za a tarar da abinci ta kowane lungu. Misali, akwai nau’ukan salon magana[12] daban-daban da aka gina su ta amfani da tubalin abinci. Daga cikinsu akwai:

    A – Misalin salon magana mai ma’anar abinci

    1. Salon magana: Abin sawa a baki

    Ma’ana: Abinci

    B – Misalan salon magana da aka gina da tubalan abinci

     Salon magana: Ban ci nanin ba nanin ba ta ci ni ba

    Ma’ana: Tun da ban amfana ba ba zan yi asara ba

    iii. Salon magana: Ci kare ba babbaka

    Ma’ana: Mutum ya yi yadda yake so ba tare da shakka ko fuskantar ƙalubale ba

    1. Salon magana: Cin tumbin kunkuru

    Ma’ana: Yin haƙuri da wahalar da mutum ba shi da maganinta

    1. Salon magana: Zaman doya da manja

    Ma’ana: Ƙiyayya ko rashin jituwa

    A ɓangaren yanken[13] Hausawa ma za a tarar da waɗanda aka yi amfani da abinci a matsayin tubalan gina su. Daga ciki akwai:

    1. Ana rige-rigen shiga aljanna ka tsaya wawan ɗanwake!
    2. Da ka ɓurka tusa sai da malmala ta yi nishi!
    3. Da wani hancinka kamar an kai alale/alala walda!
    4. Ka ci zogale ɗaya ka cika duniya da koren kashi!
    5. Ka ɗauko baki kamar ɓarnar wuƙa a kabewa!
    6. Kana ci ba ka ƙiba kamar ka ci matsefata!

    3.2.2 Zani

    Ɗuriyar zani a matsayin wani nau’in tufafin Hausawa ta mamaye duniyar adabin bakan Hausawa yadda har ta kai an samu sara[14] da yayi[15] game da shi. A ƙasa an kawo waɗansu misalan sara da yayi game da zani da suka ci zamaninsu a ƙasar Hausa. Daga ciki akwai:

    Jad. na 2: Sara masu alaƙa da zannuwa

    Sara Tsokaci
    1. Kama ta kare! Ko

    Wuh-wuh! Ko

    Mai barewa!

    A wajajen shekarar 2015 an yi wani nau’in zani mai hoton barewa a jahar Bauchi. Sai dai kash! Zanin ya yawaita sosai a cikin al’umma har ya zama abin aibantawa. Abin ya kai ga har yara da matasa na zolayar masu ɗaura shi. Yara sukan yi waƙa kamar haka:

    Bayarwa: Mai barewa

    Amshi: Wuh-wuh!

    Bayarwa: Kama ta kare!

    Amshi: Wuh-wuh![16]

    Yayin ya karaɗe garuruwa sosai[17] yadda ko da ɗaya daga cikin kalmomin aka furta, ana dai nufin zolaya ga mai ɗaure da zanin.

    2. Mai ganyen rogo! A wuraren 2006 an yi wani zane mai zanen ganyen rogo. Da zarar an ga mace da shi sai a fara zolayar ta da cewa: “Mai ganyen rogo!” Wannan dalilin ya sa kasuwar zanin ta mutu duk da kyawunsa.
    3. Karen miski! A shekarar 2017 an yi wani zane na mata mai laushi da gashi-gashi a jikinsa. An yi yayin sa ne a lokacin bikin salla. Da zarar mace ta sanya sai a ce mata: “Karen miski!”[18]

     

    Jad. na 3: Yayi masu alaƙa da zannuwa

    Yayi Tsokaci
    1. Kamfala Kamfala da soso da koken da siliki duk nau’ukan zannuwa ne da aka yi yayinsu a ƙasar Hausa. S. Habiba, (keɓantacciyar tataunawa, 21 ga watan Ogusta 2023) ta bayyana cewa, a shekarar da aka yi yayin waɗannan zannuwa, ko’ina mutum ya waiga ranar salla ‘yan mata zai gani ɗaure da su.
    2. Soso
    3. Koken
    4. Silikin

     

    Yana da kyau a lura da alaƙar da ke tsakanin sara da yayi a wannan gaɓar. Haƙiƙa su ma sun yi canjaras da falsafar Hausawa game da cuɗe ni in cuɗe ka da ke aukuwa tsakanin lamuran da suka shafi rayuwar duniya. Misalai uku (3) da aka bayar a jadawali na 1 duk sara ne da suka samu a sanadiyyar yayi. Ko misalai huɗu (4) da aka bayar a ƙarƙashin jadawali na 3, S. Habiba, (keɓantacciyar tataunawa, 21 ga watan Ogusta 2023) ta bayyana waɗansu nau’ukan sara da suka tsiro a sanadiyyarsu. Misali, yawaitarsu ya sa yayin wata waƙa ya karaɗe gari inda yara ke rerawa kamar haka:

    Mai silikin silellukan babanta!

    Mai kamfala kamfanin babanta!

    Mai koken uwarta ba ta salla!

    Mai Jamila da Jamilu shegiyar ‘yar banza!

    3.3 Ɓoyayyun Al’adun Hausawa Cikin Adabin Baka

    Ɓoyayyun al’adu su ne nau’ukan al’adun da ido ba ya ganin su sannan hannu ba ya iya taɓa su. Sun shafi tadoji da tunane-tunane da ra’ayoyi da falsafofin al’umma, kamar gaskiya da amana da kawaici da kunya da tarbiyya da tausayi da zumunci da makamantansu. Wannan ɓangare na nazarin ya kawo misalan gurabun da ɓoyayyun al’adun Hausawa suka fito cikin adabin bakansu.

    3.3.1 Amana

    Amana ita ce riƙo da gaskiya a zamantakewa da hulɗa tare da karewa da alkinta dukiya da mutunci da sirrin abokin hulɗa a gaban idonsa da bayan idonsa. Amana tana da babban gurbi a cikin kirarin[19] Hausawa. Sau da dama mai yin kirari na amfani da kalmar amana wajen nuna dangantakarsa da ubangidansa, ko wajen nuna wurin da ya gaji jarumta da hatsabibanci. Misali:

    1. Wayyeeeehoho! Ni Abu amanar Lamara!
    2. Ni Abu na Abu mai amanar daji! An ba ni amana na karɓa!

    A misalin “a” da ke ƙarƙashin “3.3.1,” za ga a cewa mai kirarin yana danganta kansa da wanda ake yi wa laƙabi da “Lamara.” Lamara ya kasance Ciroman Aska a garin Misau da ke Jahar Bauchi.[20] A ƙarƙashin “b” kuwa, a bayyane take mai kirarin na ishara ne kan cewa shi ɗan gado ne ba ɗan haye ba. Sannan ya gaji laƙanin da suka shafi daji, kuma ya ƙware kan harkar.

    Ko bayan ire-iren waɗannan, akwai maganganun kirari na yau da kullum da ke ƙunshe da kalmar amana. Misalansu sun haɗa da:

    1. Ni kububuwa amanar mutuwa.
    2. Ni mahaukacin kare amanar yaƙ

    Idan aka leƙa duniyar waƙoƙin gargajiya ma za a tarar da hotun al’adu, ciki har da amana. A waƙar roƙon ruwa ta Allah Mun Tuba,[21] za a ga yadda masu waƙar ke bayyana cewa ba za su sake cin amana ba, don dai jaddada tubansu ga Allah domin ya tausaya musu ya ba su ruwa. Kamar yadda suke cewa:

    Bayarwa: Gero a dawa ya bushe,

    Amshi: Allah mun tuba.

     

    Bayarwa: Masara a dawa ta bushe,

    Amshi: Allah mun tuba.

    Bayarwa: Ba mu cin amanar ɗan kowa,

    Amshi: Allah mun tuba.

    3.3.2 Zumunci

    A farfajiyar al’ada, zumunci kalma ce mai rassan ma’ana da ke da dangantaka da nau’in hulɗa da jin kusanci ga juna tare da jiɓintar lamuran juna da ke samuwa a sanadiyyar nasaba ko alaƙa ta jini ko maƙwabtaka ko kasuwanci da makamantan cuɗanya na dogo ko gajeren zango tsakanin mutane biyu ko fiye. Zumunci tubali ne da akan yi amfani da shi wajen gina adabin bakan Hausa.

    Babban misali game da wannan shi ne barkwanci, wanda nau’in adabin baka ne da aka gina shi kacokan kan zumunci. Tun daga ma’anar da Ɗangambo ya bayar a cikin Muhammad, (2008) za a iya ganin hakan. Ya bayyana barkwanci da cewar: “…zantuttuka ne na raha da wasu mutane waɗanda Allah ya hore wa iya magana da ban dariya ke wa mutane. Akwai wasanni tsakanin ƙabilu iri-iri, su irin waɗannan wasanni (yawanci da baki ake yi), suna ƙara danƙon zumunci, misali akwai wasa tsakanin Fulani da Barebari, Kanawa da Zage-Zagi, Katsinawa da Gobirawa da Haɗejawa da sauransu.”

    Bugu da ƙari kuma, maganganu da labaran barkwanci da dama suna ɗauke da ƙunshiyar amana. Daga ciki akwai kalamai irin su:

    1. “Ina kwana, tun da ka ƙi gai da uban gidanka.”
    2. “Ka san mu ba ma mantawa da yaranmu.”

    A ire-iren waɗannan kalamai da ke gudana tsakanin masu wasan barkwanci, za a ga nason zumunci. A misali na “a” da ke ƙarƙashin “3.3.2”, za a ga cewa mai maganar na ƙoƙarin nuna cewa ya yi riƙo da zumunci. Hakan ne ya sa ya fara gaishe da wanda yake maganar da shi, duk da ya fi shi matsayi, don dai kada zumunci ya yanke. A ƙarƙashin misali na “b” kuwa, ƙarara mai maganar ya nuna cewa ba za su yanke zumunci ba ta hanyar mantawa da yaransu.

    Idan aka leƙa kacici-kacicin Hausawa ma za a tarar da tsattsafin zumunci. Misalan kacici-kacici da ke ɗauke da nason zumunci sun haɗa da:

    1. Kacici-Kacici: Bishiyar gidanmu, inuwar gidan waɗansu.

    Amsa: Budurwa[22]

    1. Kacici-Kacici: Daga nesa na ga layun ƙawata.

    Amsa: Bishiyar ɗorawa[23]

    iii. Kacici-Kacici: Ki shiga, ki fita, ɗakin na uwarki ne?

    Amsa: Moɗa/guga[24]

    1. Kacici-Kacici: Malam ya faɗi almajirai sun taru

    Amsa: Kashi da ƙuda[25]

    4.0 Sakamakon bincike

    Lallai ya tabbata ƙarara cewa adabi da al’ada suna wanzuwa ne bisa tsarin cuɗe ni in cuɗe ka. Tsarin tattara bayanai da zaɓar samfurin bincike da aka bi na ƙara tabbatar da hakan. An ga yadda matakan rayuwa suka bayyana cikin fannonin adabi mabambanta. Misali, an ga yadda aure ya fito a cikin tatsuniya da karin magana (3.1.1). An ga lamarin haihuwa kuwa a cikin almara da ƙissa (3.1.2). Lamarin mutuwa kuwa, an hasko shi cikin labari (3.1.3).

    A  ɓangaren bayyanannun al’adu kuwa, an kawo yadda samfuran al’adu da aka ɗauka suka bayyana cikin nau’ukan adabi. Misali, abinci ya fito cikin salon magana da yanke (3.2.1). Zani kuwa ya fito cikin sara da yayi (3.2.2). Samfuran al’adu da aka ɗauka a ƙarƙashin rukunin ɓoyayyun al’adu kuwa su ne amana da zumunci. An leƙo amana a madubin adabi na kirari da waƙoƙin gargajiya (3.3.1). Zumunci kuwa aka hango shi cikin barkwanci da kacici-kacici (3.3.2).

    Wani abin lura shi ne, yawanci tubalan al’ada sama da guda ne ke haɗuwa domin gina wani nau’in adabi. A misalin waƙar roƙon ruwa da aka bayar a ƙarƙashin “3.3.1” da ke sama, an mayar da hankali ne kan ɓoyayyiyar al’ada (amana) da ta fito a cikin waƙar. An yi hakan ne ba don ɗangwayen sun taƙaita ga ƙunshiyar amana kaɗai a matsayin al’ada ba, sai don taƙaitawa kan abin da ake magana kansa a wannan bagiren. Akwai ɗangwayen da suka ambaci “gero” da “masara” waɗanda dukkanninsu suna daga cikin bayyanannun al’adu. A falsafance, ana iya cewa adabi guda na iya haska nau’ukan al’adu daban-daban a madubinsa.

    5.0 Kammalawa

    Babu wani nau’in al’adar Hausawa face sai an tarar da ita cikin madubin adabi. Haka kuma, babu wani nau’in adabin Hausa face sai an tsinci tsattsafin al’ada a cikinsa. Ke nan ana iya cewa, al’adu ne tubalan gina kowane nau’in adabi. A ɓangare guda kuwa, adabi madubi ne ko hoto da ke ɗauke da kowace nau’in al’ada. Tun da kuwa haka ne, akwai buƙatar zurfafa bincike a fuskar nau’ukan tasiri da al’ada ke da shi kan adabi, da kuma musamman tasirin adabi a kan al’ada.

    Ta irin waɗannan nazarce-nazarce ne za a iya gano shin tasirin al’ada kan adabi ke samar da sababbin nau’ukan adabi da sauye-sauye cikin waɗanda ake da su? Ko kuma adabi ne ke yin tasiri kan al’ada da har yake samar da sababbin al’adu? Ko wannan tasiri ana samun sa ne ta dukkannin fuskokin guda biyu? Nazarce-nazarcen da za su amsa ire-iren waɗannan tambayoyi za su taimaka wajen ƙara fahimtar fagagen biyu wato adabi da al’ada. Za kuma su yi ƙarin haske kan muhawarar nan da ke ci gaba da gudana ta tasirin zamani kan al’adun Hausawa.

    Manazarta

    Abdullahi, A. (2021). Doki a tunanin adabin bakan Bahaushe: Nazari daga labarun baka da karin magana [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Abdullahi, I. S. S. (2000). Magani da siddabaru cikin rubutattun ƙagaggun labarun Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Atuwo, A. A. (2009). Ta’addanci a idon Bahaushe: Yaɗurwarsa da tasirinsa a wasu ƙagaggun labarai na Hausa [Kundin digiri na uku da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Buba, M. (2016). Adon harshe a adabin baka: Nazari a kan amfani da tsuntsaye a waɗansu waƙoƙin Ɗanƙwairo [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Bunza, A. M. (2006). Gadon feɗe al’ada. Tiwal Nigerian Limited.

    Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a Farfajiyar Adabi da Al’adun Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(12), 720–727.

    Bunza, A. M. (2013). Wani ra’ayi dangane da yadda aka fitar da rayuwar Hausawa a cikin littafin Shehu Umar [Takardar da aka gabatar]. Taron Ƙara wa Juna Sani, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Giwa, A. A. (2012). Gurbin tarbiyya a cikin tatsuniyoyin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Gobir, Y. A., & Sani, A.-U. (2021). Waƙoƙin Hausa na gargajiya. Amal Printing and Publishing.

    Haliru, A. R. (2018). Yaƙe-Yaƙe a wasu rubutattun littattafan ƙagaggun labarai na Hausa na gasa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Muhammad, M. S. (2008). Hauka a idon Bahaushe [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Musa, M. Y. (2019). Tarken tarbiyya a cikin waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Mustapha, S. (2003). Gurbin gaskiya cikin adabin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Najahu, I. K. (2018). Adabi madubin al’ada: Tsokaci a kan al’adar baƙunci a adabin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Sarkin Gulbi, A. (2014). Magani a ma’aunin karin magana [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Yahya, A. B. (2001). Dangantakar waƙa da tarbiyyar ‘ya’yan Hausawa. Harsunan Nijeriya, XIX, 94–109.

    Yahya, A. B. (2004). Tattalin zaɓen rubutattun waƙoƙin Hausa domin yara. FAIS Journal of Humanities, 3(1), 217–232.

    Yahya, A. B. (2013). Tsattsafin raha cikin waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno. Mujallar Nazarin Waƙoƙin Hausa, 1(1).

    Yahya, A. B. (2016). Salo asirin waƙa (sabon bugu). FISBAS.

    Yahya, A. B., & Aliyah, A. A. (2020). Kukan kurciya cikin waƙoƙin Korona biyu. Amadu Bello University Press.

     

    [1] Rubuce-rubuce da aka gudanar a fannin adabin Hausa sun haɗa da ayyukan Yahya, (2004) da Bunza, (2006) da Yahya, (2016) da Bunza, (2019) da Yahya & Aliyah, (2020) da Abdullahi, (2021) da makamantansu.

    [2] An keɓance matakan rayuwa ne (aure da haihuwa da mutuwa) ba don ba su da muhalli cikin rabon farko na bayyanannu da ɓoyayyun al’adu ba, sai don a ba su gurbi na musamman kasancewar suna ba babban matsayi a fannin nazarin rayuwa. Samun dukkanninsu cikin madubin rayuwa wani mataki ne na fara samun tabbacin ana iya kallon dukkannin al’adun Hausawa cikin wannan madubi.

    [3] Keɓancewar zai tabbatar da iƙirarin binciken na cewa kowanne rukunin adabin baka na ƙunshe da al’ada a matsayin tubalan gina shi.

    [4] A shafi na 54 ya nuna cewa: “Yaƙi wata mu’amula ce ta gwadi da nuna fifikon ƙarfi tsakanin mutanen ƙasashe ko ƙungiyoyi fiye da ɗaya, masu gaba da juna, domin neman biyan wasu buƙatu na rayuwa waɗanda ba a iya samu sai ta hanyar tilastawa.”

    [5] “Tatsuniya wani tsararren labari ne mai ɗan tsawo na hikima da nuna ƙwarewa da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da kuma cinye lokaci” Yahaya da wasu a cikin Buba (2016: 85).

    [6] A duba (Gobir & Sani, 2021: 122) domin samun cikakkiyar tatsuniyar.

    [7] Domin samun ƙarin misalai, ana iya duba https://www.amsoshi.com/2017/07/karin-magana-game-da-aure_5.html.

    [8] Yahanya da wasu a cikin Buba, (2016 p. 85) sun bayyana cewa, almara “… labari ne shiryayye, ƙagagge cikin hikima da ake aiwatarwa don kaifafa tunanin masu sauraro ko don nishaɗi da nishaɗantarwa.”

    [9] A mahangar addini, ƙissa labari ne na annabawa da sahabbai da mala’iku da waɗansu muhimman mutane ko halittu a cikin addini. A mahangar adabi da al’adun Hausawa kuwa, akan samu sauye-sauye da ƙirƙire-ƙirƙire a lamarin ƙissoshi domin fitar da waɗansu darusa tare da faɗakar da al’umma.

    [10] Buba, (2016: 92) ya rawaito inda Zarruk da wasu suka ba da ma’anar labari da cewa: “… zance ne tsararre mai kai da gindi. Wato irin zance da ka iya cewa ga farkonsa. Sannan kuma idan an ƙare, kana iya sani. Irin wannan labari yana iya zuwa ko a magance ko kuma a rubuce, kuma wani lokaci akan same shi da ɗan tsawo.”

    [11] Domin samun wannan labari a kammale, ana iya duba https://www.amsoshi.com/2023/08/labarin-shehu-jaha-da-wani-malami.html.

    [12] Salon magana na nufin amfani da kalmomi biyu ko fiye waɗanda dunƙulalliyar ma’anarsu ta bambanta da ma’anoninsu yayin da suke a matsayin ɗaiɗaiku.

    [13] Yanke tsararrun zantukan hikima ne na muzanci ko kushe ko soka baƙar magana ga wani mutum ko waɗansu mutane ta hanyar siffantawa ko kwatanta su ko wani ɓangare na jikinsu ko wani abu da ke da alaƙa da su ko halayya da ɗabi’unsu da wani abu ko wani lamari mai ƙasƙancin matsayi ko wanda zai ba da hoton zuci da ke bayyana su a matsayin nakasassu ko ƙasƙantattu ko koma-baya.

    [14] Sara ƙirƙirarrun zantuka ne da kan yi tashe a wani lokaci, masu ba da ma’ana ta musamman ga wanda ya san su, waɗanda ake tsarawa game da wani mutum ko wasu mutane ko wani abu ko waɗansu abubuwa domin yabawa ko kushewa ko gorantawa ko zolaya ko ƙarfafawa, waɗanda kuma ke dusashewa ko ma su ɓace bayan sun ci zamaninsu.

    [15] Yayi na nufin wani abin da ya yi fice a tsakanin mutane a wani taƙamaiman lokaci wanda mallakarsa ko samar da shi ko mu’amala da shi ko aiwatar da shi cikin wani ayyanannen salo da tsari shi ne burgewa, wanda kuma armashinsa ke dusashewa ko ma ya salwanta bayan ya ci zamaninsa.

    [16] A wannan gaɓa ma za a tarar waƙa ta samu a sanadiyyar al’ada. Duk wannan na ƙara tabbatar da iƙirarin falsafar nan ta Hausawa game da “cuɗe ni in cuɗe ka.”

    [17] Wannan bayani ya fito ne daga jahar Bauchi. Ba a samu tabbacin ko ya karaɗe garuruwan waɗansu jahohi na daban ba.

    [18] I. Hamza, (keɓantacciyar tattaunawa, 21 ga watan Ogusta 2023)

    [19] Kirari wasu gajerun zantukan hikima ne, tsararru da ake shiryawa domin yabo da jinjina da kambamawa ga mutum ko mutane ko wani abu ko waɗansu abubuwa, tare da kushewa ko ƙasƙantar da darajar kishiya ko kishiyoyinsa.

    [20] An halarci taron janjanko (taron mafarauta da ƙauraye da wanzamai) a garin Misau, jahar Bauchi, a ƙofar Ciroman Aska da ke unguwar Mangari.

    [21] Domin ƙarin bayani, ana iya duba Gobir da Sani, (2021 p. 134-135).

    [22] Zumuntar aure ke sa budurwa tarewa wani gida.

    [23] Idan har ƙawa na iya hango layun ƙawarta daga nesa sannan ta gane su, lallai zumunci ya yi zumunci.

    [24] Da a ɗakin uwarta ta riƙa shige da fice, lallai ba za ta fiskanci tsangwama ba saboda ƙarfin zumuntar da ke tsakani.

    [25] Da zarar wani abu ya faru da wani, zumai za su yi caa, har sai inda ƙarfinsu ya ƙare.

    Karanta Maƙala Mai Taken: Nason Kishi a Zubin Zaɓaɓɓun Tatsuniyoyin Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken: Nason Kishi a Zubin Zaɓaɓɓun Tatsuniyoyin Hausa

    Maƙala Mai Taken: Nason Kishi a Zubin Zaɓaɓɓun Tatsuniyoyin Hausa

    Maƙala Mai Taken: Nason Kishi a Zubin Zaɓaɓɓun Tatsuniyoyin Hausa

                                                   Daga

    Dr. Adamu rabi’u bakura

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: arbakura62@gmail.com

    Phone: 08064893336

                                                     Da

    Abu-Ubaida Sani

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng

    ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

     Citation: Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2025). Nason Kishi a Zubin Zaɓaɓɓun Tatsuniyoyin Hausa. In Mukhtar, I., Muhammad, A.S. & Lawal, N. (eds), Kadarkon Adabin Hausa: A Festschrift in Honour of Professor Sa’idu Muhammad Gusau. Department of Nigerian Languages, BUK, p. 661-670. ISBN: 978-978-772-21-2-1

     Tsakure

    A maganar yau da kullum, an fi danganta kishi da mata a ƙasar Hausa. Duk da haka, nazarce-nazarce da dama sun nuna cewa al’amarin kishi abu ne da ya kasance gama-gari a tsakanin mutane – bai taƙaita ga mata ba kawai. Manufar wannan takarda ita ce nazartar nason kishi a cikin wasu tatsuniyoyin Hausa domin tabbatar da ‘kishi’ a matsayin wani al’amari da ya mamaye al’adun Hausawa.

    An samu bayanan binciken kai tsaye daga zaɓaɓɓun tatsuniyoyin Hausa. Binciken ya gano cewa, lallai akan yi amfani da taurari da kayan cikin tatsuniya domin bayyana hotunan nau’ukan kishi daban-daban. Bugu da ƙari, nau’in kishin yana iya kasancewa fari (dangin soyayya da ƙoƙarin kare martaba da mutuncin masoyi) ko kuma baƙi (wanda ya shafi hamayya da ƙyashi da ƙiyayya).

    Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarar amfani da hanyoyin zamani domin zamanantarwa da sanya tatsuniyoyin Hausa cikin manhajoji da tsarin bidiyoyi domin ci gaba da cin gajiyar darussan da suke cikinsu.

    Fitilun Kalmomi: Kishi, Tatsuniya, Al’ada, Adabi, Zube

    1.0 Gabatarwa

    Akwai fuskoki uku da ya dace a dubi lamarin kishi idan dai ana son a gane yadda yake da yadda yake gudana a rayuwa. Da farko a fahimce shi a matsayin abin da ake samu a kowace irin halitta, ko kuma a tarbe shi bisa tsarin al’adu ko kuma a luggance, kamar yadda masana suka yi nazari. Na ƙarshe kuwa shi ne a kawo bayaninsa kamar yadda yake a aikace, wato yadda masana da manazarta suka kalle shi.

    Akwai nazarce-nazarce da aka gudanar a ƙoƙarin gano ko kishi halitta ce ko al’ada da ake samu a kowace irin halitta. Heiman da Iyon (1998) sun yi nuni da cewa, yadda ake kallon kishi a tsakanin kowace al’umma ya mabambanta. Hakan ne ya sa suka so su amince da cewa kishi abu ne da ya dogara kan yadda kowace halitta take gudanar da rayuwarta. Haka kuma, al’ada takan yi tasiri a kan kishi.

    Haƙiƙa lamarin kishi ya zarce zancen halitta kawai. Ya haɗa har da al’ada. Za a iya ɗaukar babban misali daga yadda a tsakanin wasu al’ummu, kwana da matar wani ya kasance abin karramawa ga baƙo. A tsakanin wasu al’ummu kuwa, kallo kawai ga matar wani babban al’amari ne da zai iya haifar da hatsaniya.

    Duba cikin adabin al’umma hanya ce da za a iya gano yadda wani al’amari ya mamaye al’adarsu. A bisa haka ne wannan takardar ta ƙuduri aniyar nazartar al’amarin kishi a cikin adabin Hausa. Kwatanta fannin al’ada da adabi abu ne mai faɗin gaske. Wannan nazari ya leƙa wani muhimmin ɓangare na adabin Bahaushe da ya ƙunshi adabin gargajiya (tatsuniyoyin Hausa).

    Aikin ya mayar da hankali wajen nazartar wuraren da aka samu nason kishi a cikin tatsuniyoyin Hausa tare da ƙoƙarin fayyace falsafar da ta samar da su. Hakan ne zai iya tabbatarwa ko kore hasashen binciken da ya ginu kan fahimtar cewa kishi da halitta sun kasance tamkar tsoka da jini.

    1.1 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

    Wannan bincike ya shafi nazartar al’ada ne a cikin adabi. Zubinsa ya taƙaita ga ƙalailaice batutuwa, a inda aka nazarci nason kishi a cikin tatsuniya. An dubi zaɓaɓɓun tatsuniyoyi kai tsare inda aka yi nazarin su. Ba a bi wani mataki na musamman domin ɗaukar samfurin tatsuniyoyin da za a yi magana a kansu ba. Hakan ya faru ne sakamakon manufar binciken ta taƙaita ga hasko nason kishi a cikin tatsuniyoyi na Hausa kawai. Ma’ana dai, ba a mayar da hankali kan ƙididdigar alƙaluman da za su nuna ƙiyasin kason tatsuniyoyin Hausa da suke ɗauke da tsattsafi ko nason kishi a cikinsu ba.

    An nazarci rubuce-rubucen da suka gabata domin samun haske musamman game da kalmar ‘kishi’ da abubuwan da ya ƙunsa. Haka kuma, ayyukan da suka gabatan sun kasance jagoranci ga wannan bincike wajen haska masa hanya game da dabaru da matakan gudanarwa. Kai tsaye an dogara da littattafan tatsuniyoyin Hausa wajen zaƙulo misalan tatsuniyoyi. An yi hakan ne domin dogaro da rubutaccen manazarta da za a iya yi wa mai karatu ishara zuwa gare shi.

    2.0 Bitar Kalmar ‘Kishi’

    Kishi al’amari ne da ya daɗe yana jan hankalin masana da manazarta. Rubuce-rubuce da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar kishi. Bargery (1934) a ƙamus ɗinsa, ya bayyana ma’anar da cewa: “… shi ne ganin ƙyashi da ke tsakanin kishiyoyi.” A cigaba da bayanin kishi, ya kawo rabe-rabensa kamar haka:

    1. kishin birni
    2. kishin kai
    3. kishin sauri
    4. kishin zuci

    Shi kuma Talata Mafara (2002) ya fassara ma’anar kalmar Larabci ta ‘algirah’, wadda take ɗauke da ma’anar kishi da: “Canjawar zuciya da motsawar jini domin nufin ramuwa, saboda dalilin tarayyar wani a kan wani abu da ba ya karɓar tarayya.” A fahimtarsa, “mafi tsananin kishi shi ne wanda ake samu a tsakanin ma’aurata.

    A wani bayani mai kama da wannan, Talata Mafara (2000) ya ruwaito cewa, an fassara kalmar Larabci ta kishi wato algirah da ma’anar: “Namiji ya yi kishi ga mace ko mace ta yi kishi ga namiji, idan ransa/ta ya/ta motsa saboda macen ta bayyanar da adonta ga wani, ko kuma ta juya masa baya, tana mai sha’awar wani. Haka ita ma idan ranta ya motsa, za a ce ta yi kishi, idan mijinta ya karkata ga wata.

    Ko bayan ma’ana ta lugga, manazarta da dama sun bayyana ma’anar kishi a cikin rubuce-rubucensu. Wani abin lura shi ne, dukkannin ma’anonin za a tarar suna bayyana kishi a matsayin wani yanayi ko ƙoƙarin kare abin da ake so. Zai iya kasancewa mutum ne ko wani abu ko ma wani muradin zuci. Aikin Gwandu (1997) ya kalle shi a matsayin “wani hali na ƙaƙa nakan yi, wanda yake sakar wa mutum wani ƙololo na baƙin-ciki a zuciyarsa na zafin cewa wani abu ya faru.” Sauran ayyukan da suka kawo ma’anar kishi sun haɗa da na Ingawa (1989) da Malik (2000) da Bakura da Sani (2022).

    Idan aka nazarci waɗannan ma’anonin da aka bayar, za a iya ƙwanƙwancewa tare da tabbatar da cewa, kishi wata hanya ce ta gwagwarmaya da ke tattare da zargi da tuhuma da saɓani da rashin jituwa da husuma da mugun nufi, domin ƙoƙarin kare ƙeɓantacciyar ƙauna ga abin so ba tare da yin tarayya da wani ba. Duk da haka, kishi yana iya ɗaukar faffaɗar ma’ana ko wasu ma’anoni a fannonin rayuwa na daban.

    Haka kuma za a iya kallon kishi a ɗabi’ance da cewa wata halittacciyar ɗabi’a ce ga ɗan’adam da take tattare da gwagwarmayar rashin son yin tarayya ga keɓantacciyar soyayya da take aukuwa a tsakanin jinsin namiji da mace. Irin wannan soyayya tana tattare da tuhuma da zargi a tsakanin masoya.

    Yana kuma iya ɗaukar ma’anar matuƙar ƙauna da fatar alheri ga wani abu da yake haddasa wa ɗan’adam aiwatar da gwagwarmayar da za ta taimaka masa wajen kare mutuncinsa da kansa da martabarsa da ɗaukakar darajarsa, da kuma ɗorewar wanzuwar abin da yake so da ƙauna. Irin wannan ma’anar ta kishi, ita ta haifar da wanzuwar abubuwan da ake kishin su sakamakon kusantuwa gare su. Sun haɗa da:

    1. kishin zuci
    2. kishin addini
    3. kishin ƙasa
    4. kishin harshe
    5. kishin al’ada, da dai makamantansu.

    Kyawun kishi ko rashin kyawunsa ya danganta da yanayi da kuma bagiren da aka aiwatar da shi. Hadisin Manzon Tsira (SAW) ya kawo cewa: “An karɓo daga Mugiratu ɗan Shuuba (R.A.) ya ce: Saadu ɗan Ubaida (R.A) ya ce: “Da zan ga wani mutum tare da matata, wallahi da na sare shi da kaifin takobina.” Sai wannan magana da ya furta ta kai ga kunnen Manzon Allah. Sai ya ce: “Kuna mamakin kishin Sa’adu ne? Na rantse muku da Allah na fi shi kishi. Ni kuma Allah Ya fi ni kishi.”” (Muslimu ya ruwaito hadisin).

    Idan aka nazarci wannan Hadisi, za a tarar da cewa, yana ƙunshe da abubuwa da yawa. Da farko za a iya cewa, kishin Annabi (S.A.W.) ya ƙunshi kishin addini. Za a ga misalin hakan idan aka yi la’akari da irin gwagwarmayar da ya yi wajen isar da manzancinsa da yadda ya yi artabu da kafirai da irin yadda yake mai tsananin fushi idan aka saɓa wa umurnin Ubangiji. Bayan wannan, za a tarar Annabi (S.A.W) yana kishin matansa kuma yana kare su daga duk wani abu da zai haifar da cuɗanya tsakananinsu da maza.

    Akan samu muhallan da kishi yakan kasance ƙazantacce, abin zargi. Irin wannan kishi ya haɗa da kishin da ake aiwatar da shi ta hanyar tsafe-tsafe domin gusar da wata ni’ima da Allah Ya yi wa wani. Misalan ni’ima a nan sun haɗa da sarauta ko ilimi ko dukiya ko mata. Masu irin wannan kishi ne Allah Ya ja wa kunne, a inda yake cewa:

    “Kuma kada ka yi burin gushewar abin da Allah Ya fifita sashenku da shi a kan sashe” (Alƙur’ani, 4: 32).

    Haƙiƙa lamarin kishi ga halitta abu ne da aka halicce ta da shi, musamman ma ɗan’adam. Babu ko shakka, kishi a rayuwar ɗan’adam ya zama tamkar jini da tsoka. Abu ne mai matuƙar wuya a gudanar da wani al’amari na rayuwa ba tare da an samu ɓirɓishin kishi a cikinsa ba. Idan Bahaushe ya ce abu ya zama jiki, abin nufi a nan shi ne, ko’ina ana tare da wannan lamari ko ɗabi’a. Wannan yana iya kasancewa, ko dai ana sane ko kuma ba da sanin mahalukin da abin ya zamar masa jiki ba.

    2.1 Matsayin Kishi a Rayuwar Hausawa

    Kishi yana da gurbi na musamman a tsakanin Hausawa. Hasali ma, babu wani al’amari da za a iya taɓukawa ba tare da an nuna kishin abin ba. A bisa haka ne har al’ummar Hausawa suke kallon kishin a matsayin ginshiƙin ɗorewar wanzuwar ƙasar Hausa. Dalilin hakan shi ne, ta hanyar nuna kishin ne har al’ummar ƙasar ta wayi gari ta kasance a cikin kafaffiyar daula ɗaya, masu al’adu da ɗabi’u da manufofi bai ɗaya. Haka kuma, kishi wani tubali ne na ginin al’ummar Hausawa tare da tabbatar da tsaron mutunci da ɗorewar zaman lafiya, wanda ya tattara a kan dukkan al’ummar gaba ɗaya.

    Ba a nan kaɗai ya tsaya ba, domin yana kasancewa ginshiƙin dogaro da kai da haɓaka tattalin arzikin ƙasa tare da tabbatar da martabar al’umma a idon duniya. Yakan sa mutum ya kasance mai taimakon dangi da al’ummarsa gaba ɗaya. Hakan kan tabbatar da haɗin kai da rufin asiri da fitar da juna daga kunya dawwamammiya. Don haka ne idan sarki ya fita fada, shi kuma sarkin noma sai ya nufi gona, sarkin maƙera kuwa ya hura wutar ƙira, yayin da mata za su zuba ribiɗi (daka). Ta haka sai al’umma ta zauna da ƙafafunta.

    Kishi wani ginshiƙi ne na tabbatar da haɗin kai a tsakanin al’umma. Sukan haɗu, su haɗa ƙarfi don kariyar mutuncinsu. Kowace ƙungiya ta yi shiri don kuɓutar da sauran dangi daga zalunci. Babban zalunci kuwa a lokacin da ya gabata shi ne harin yaƙi. Ta ƙoƙarin bayyana kishin al’umma ne har aka sami jarumai da yawa da suka shahara ta hanyar nuna kishin zuci da ƙaunar ‘yan uwa.

    Kishi yana taimakawa wajen kyautata rayuwar al’umma da fito da al’adunsu a fili, kowa ya san su. Haka kuma, yana tabbatarwa da nuna martabar al’umma da ƙasar baki ɗaya, har a wayi gari an san ta. Yana kuma cusa wa al’umma alfahari da kai tare da girmama abin da suka gada, kaka da kakanni da ƙoƙarin bayyana abubuwan fasaharsu.

    3.0 Kishi a Tatsuniyoyin Hausawa

    Tatsuniya tana ɗaya daga cikin nau’o’in zuɓe na adabin baka. A luggance, Bargery (1934, sh. 1005) ya bayyana tatsuniya a matsayin “almara.” A wani ƙaulin kuma an kira ta da “wasa ƙwaƙwalwa.” Yahaya da wasu (1992 sh. 7-10) sun ce:

    Tatsuniya wani tsararren labari ne mai ɗan tsawo na hikima da nuni zuwa ga halaye da ilimin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da kuma cinye lokaci.

    Wannan ma’ana ta yi kama da ta Gusau (2013 sh. 5) inda ya bayyana ma’anar tatsuniya da cewa:

    Wani tsararren labari ne kuma shiryayye wanda ake shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe domin koyar da dabarun zaman duniya daban-daban.

    Akasari a ɗakunan tsofaffi mata da amare yara suke taruwa da dare ana yi musu ita. Tatsuniyar Hausa tana da salon farawa da akan ce: “Ga ta nan ga ta nan ku.” Haka kuma akan rufe da “ƙurungus” a karin harshen Sakkwatanci da Katsinanci. A karin harshen Zazzaganci da kuma karin harshen Kananci, ana cewa “ƙurunƙus” ko “taƙurunƙus.” A cikin irin waɗannan tatsuniyoyin Hausawa, akan samu nason kishi. Lamarin yana da girma ta yadda da wuya a aiwatar da tatsuniya biyu zuwa biyar ba tare da an samu ɗaya da take da wani fasali da yake tattare da nason kishi ba. A nan, an dubi wasu daga cikin tatsuniyoyin Hausa domin nazartar yadda sha’anin kishi yake fitowa a ciki. 

    3.1 Tatsuniyar Ta-Kitse

    Duk wanda ya nazarci tatsuniyar Ta-Kitse zai yarda da cewa sha’anin kishi ya mamaye tatsuniyar. Hasali ma a iya cewa, kishin ne ya zama babban tubali da aka yi amfani da shi wajen gina tatsuniyar. A sakamakon tsegumin da Gizo ya kai wa sarki na ‘sa’ da kuma labarin Ta-Kitse, shi ne mataki na farko da sarki ya bayyana kishinsa a yayin da Gizo ya ce:

    Daga ba jidanka ba shai jidana”.

    Wannan lafazi da Gizo ya yi, ya haifar da bijirowar kishin sarki, wanda ya sa har sarki ya nemi Gizo da ya maimaita abin da ya faɗa, a inda ya ce:

    Me ka ce?”

    Wannan ya nuna cewa, sarki ba ya son wani ya yi tarayya da shi a kan mallakar wani muhimmin abu kamar sa da kuma mata. Jin irin wannan tambayar da sarki ya yi masa, sai shi kuma Gizo ya sha jinin kijinsa. Ya yi waskiya domin ya kauce wa fushin sarki, a inda ya ce:

    Daga ba jidanka ba shai jidan ‘ya’yanka” (Yahaya, 1979 sh. 14).

    Babu shakka, ana iya cewa wannan shi ne tubalin farko da aka fara amfani da shi wajen ginin wannan tatsuniya. Za a iya lura da cewa, shi ma Gizon, kishin kansa ne ya sa ya sauya maganarsa, domin ya tsira da mutuncinsa, kar ya gamu da fushin sarki.

    A ci gaba da tatsuniyar, za a tarar inda ‘yan matan nan suka rinƙa jayayya a kan wadda za ta kai wa baƙo ruwan sha. Kowacce tana kishin ta yi aiki, alhali ga ‘yar’uwarta tana zaune. Daga ƙarshe tsohuwa ta umurci Ta-Kitse da ta kai wa baƙon ruwan sha. Ita ce kawai kuma ta bi umurnin tsohuwar.

    Wannan ya nuna mana irin yadda Ta-Hanta take kishin Ta-Tumbi, Ta-Tumbi take kishin Ta-Hanji, Ta-Hanji take kishin Ta-Huhu, da yadda Ta-Huhu take kishin Ta-Zuci, Ta-Zuci take kishin Ta-Ƙoda, Ta-Ƙoda take kishin Ta-Kitse. Za a iya lura da cewa, kowace daga cikinsu tana da kishiya, wadda take hamayya da ita, in an cire Ta-Kitse, wadda ita kaɗai ce ba ta da kishiya, balle har ta nuna hamayyarta gare ta. Kuma wannan ne ya ba ta damar zama matar sarki, wanda yake wani matsayi babba gareta kamar yadda Yahaya (1979 sh. 19-21) ya bayyana.

    A ci gaba da tatsuniyar, an nuna irin yadda matan sarki suka nuna kishinsu kai tsaye a kan Ta-Kitse a yayin da suka sami labarin sarki ya yo amarya, wai Ta-kitse. A nan suka nuna damuwarsu. Ganin cewa ba su da magani, illa su dogara ga Allah, wannan shi ya sa suka ce:

    To ku bar ta, ai shi ke nan, ta zo. Don ma ya yi amaryar kitse, meye har za mu ɓata ranmu? Ai za ta narke ne. Abin da za mu sa ta yin girki. In ta je gurin wuta ba sai ta narke ba, tun da yake kitse ba ya son wuta? (Yahaya, 1979 sh. 21).

    Wannan ya nuna mana a fili irin matakan da matan sarki suka ƙuduri aniyar bi domin su kauce wa zama da kishiya, wadda suke ganin ta tamkar alaƙaƙai ce a gunsu.

    A ɗaya ɓangaren kuma, a cikin wannan tatsuniya ta Ta-Kitse, ita ma tsohuwa za mu ga irin yadda ta nuna kishinta a kan rashin ganin ‘yarta Ta-Kitse. Hakan ya sa ta tunkari gidan sarki, duk kuwa da ƙarfin mulkinsa, har ma ta gaya masa magana a inda take cewa:

    Yallaɓai amma ba ka kyauta mini ba. Ai in son yarinyar nan kake yi sai ka ce mini, kana son ta, in rabonka ce sai in ba ka ita; amma ba ka je daga cewa za ka sha ruwa ka sato ta ba (Yahaya, 1979 sh. 22).

    Dubi irin yadda kishi ya rufe wa tsohuwa ido har ta kira sarkin gari a matsayin ɓarawon ‘yarta! Babu ko tantama, ana ma iya cewa Bahaushe ya gina wannan tatsuniya ne, ba don kome ba face ya ɗebe takaicinsa a kan basarake, saboda irin mulkin mallakar da ake yi masa. Don haka, a iya bugun ƙirji a ce yunƙurowar kishi ne ya haifar da ƙirƙiro wannan tatsuniya, idan aka yi la’akari da irin yadda jigon kishi ya nashe a tatsuniyar.

    A sakamakon tarewar amarya ɗakin mijinta, kishi ya yunƙuro wa matan sarki, har ya sakar musu sambatu, suna habaici suna cewa:

    Ƙn, mhn, ashe fa a gidan nan an yiwo abin da ba ya son rana da wuta. Ke ki fito ki yi aiki mana? (Yahaya, 1979 sh. 22).

    Ta-Kitse ta bayyana wa kishiyoyinta cewa, ita ba ta son zafin rana da na wuta, don haka ba za ta yi aiki a tsakar rana ko kusa da wuta ba. Duk da wannan bayani da ta yi musu, kishi bai bar su suka gamsu da uzurin da ta ba su ba. Hasali ma sai suka ce:

    Kya ma fito, ko ba kya ƙaunar Allah dole kya yi. Da ƙin ki da son ki, dole sai kin yi aiki. (Yahaya, 1979 sh. 23).

    Sarki ya ja wa matansa kunne ta hanyar gargaɗin su a kan kada su kuskura su sa Ta-Kitse aiki kusa da wuta ko cikin rana. Hasali ma ya ce ko su ma bai ce su yi aikin kome ba. Duk wani aiki da ake son yi, a sa barori su yi. Duk da haka, kishi bai sa suka ɗauki gargaɗin sarki ba, balle har su yi tunanin sakamakon da zai biyo baya idan har sun karya dokar sarki. Domin kuwa yayin da kishin ya yunƙuro sai suka ce wa Ta-Kitse:

    To saura, sai ki fito ki tura wuta. Bayin naki masu yi miki aiki ki ci, ki sha, sun gaji. Sai ki fito yau ke ma ki miƙe ‘yar ƙashinki, ki yi, ba mai yi miki. Ki fito ki tura wuta, mu da muke yi miki, mun gaji. Ai mu ba bayi ba ne! Kin ji ba? (Yahaya, 1979 sh. 23).

    Idan muka dubi waɗannan kalamai da matan sarki suka yi wa Ta-Kitse, za mu ga cewa suna bayyana mana hoton rayuwar zaman aure a ƙasar Hausa, a inda kishiya ko kishiyoyi suke nuna ƙyamarsu da ƙiyayya tare da tsangwama ga kishiya tare da bin hanyoyin da za su taimaka wajen kawo ƙarshen zamanta a gidan miji.

    Kamar yadda bayani ya gabata ne, Bahaushe ya shirya tatsuniyar Ta-Kitse a sabili da irin kishin da yake yi a kan yadda ake gallaza masa ta amfani da ƙarfin mulki. Wannan ne ya sa shi kuma ya fake da tatsuniya, a inda a kaikaice ya bayyana basarake a matsayin mai tsananin jarabar son mata.

    Hakan ya sa ya taso da kansa don ya ga irin kyau da Ta-Kitse take da shi da kuma irin yadda ya bar muhimmin aiki da ya shafi kare martabar ƙasarsa, wato yaƙi, ba don kome ba sai kawai don jarabar mata. Bayyana irin waɗannan abubuwa a bainar jama’a, wata alama ce da take nuna siffar yadda kishin talaka yake yunƙurowa.

    3.2 Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    A cikin tatsuniyar Daskin Dariɗi, ana iya hango lamarin kishi. An nuna yadda sauran kayan abinci kamar su Gero da Dawa da Maiwa da Shinkafa da Acca da Ibiro da Alkama, suka haɗe wa Burtuntuna kai tare da nuna mata ƙiyayya a lokacin da suka ga ita ma ta ci ado za ta tafi wurin saurayi, (mai suna Daskin Dariɗi), kamar yadda Yahaya (1976, sh. 12) ya kawo. Sun nuna kushewarsu, har ma suka ɓuge da cewa:

    Kun ga waccan shegiyar. Wa ya ba ta aron kaya ta ɗaura? Sai kuma suka ce, wa ya sani ne? Mu yi maza mu je kada ta riga mu. Kodayake ma ko ta je me zai yi da ita? (Yahaya, 1976 sh. 16).

    Wannan kalamin nasu ya fito mana da yadda suka bayyana kishinsu a kan Burtuntuna, kuma suna tsoron kada ta ja ra’ayin saurayin, har ya ce ita zai aura. Lamarin kuwa haka yake, domin su da kansu sun nuna hakan a inda suka nemi su yi sauri domin su riga ta isa.

    Idan muka dubi wannan nau’in kishi za mu tarar cewa, kishi ne da yake wanzuwa a tsakanin matan Hausawa a sakamakon fifikon kyau ko asali ko hali ko suturar yin ado ko kwalliya. A ɗabi’ance za a tarar kamar yadda ya zo a tatsuniyar, haka abin yakan gudana a rayuwa ta zahiri.

    Sau da yawa za a tarar waɗanda aka fi kyau ko iya kwalliya ko asali ko suturar kwalliya, su suka fi gabatar da kishinsu a kan waɗanda suka fi su. Wannan al’amari ba wai ya tsaya a tsakanin kishiyoyi ba ne, har ma ya haɗa da ‘yan-mata. Sai dai abin kula a nan shi ne, kishin da ya zo a cikin wannan tatsuniya, kishi ne mai sauƙi, domin kuwa an nuna cewa, sun nemi da su zama barorin Burtuntuna daga baya (bayan ta samu nasara).

    3.3 Tatsuniyar Ɗan Sarkin Agadas

    Da zarar an leƙa wannan tatsuniya, za a tarar tana ɗauke da ɓirɓishin kishi. Wannan kishi ya sha bamban da waɗanda suka gabata. Da farko an gina tatsuniyar ne a kan yadda hamayyar da take tsakanin kishiyoyi takan yi naso ta shafi ‘ya’yansu. Har ma takan zarce zuwa ga samarin ‘ya’yan nasu, kamar yadda ya zo a cikin wananan tatsuniya ta Ɗan Sarkin Agadas. A cikin tatsuniyar, an yi masa sammu domin a kawo cikas game da alherin da yake yi wa budurwarsa. Wannan lamari zai iya tabbata, idan muka yi la’akari da abin da Mowa take cewa:

    A’a waɗannan shegun ina suka samu kuɗi haka ne? Bari dai in je wurin malami ya duba mini inda suke samun kuɗin nan. (Yahaya, 1977 sh. 5 ).

    Tsananin kishi ne da take nuna wa Bora da ‘yarta shi ya sa har take jin haushin kuɗin da suke samu. Ta kai ga tuntuɓar ɗan duba domin a bayyana mata inda suke samun wannan alheri, don ta san matakin da ya kamata ta bi. An bayyana mata cewa ɗan sarki ne yake son ‘yar Bora wanda saboda haka ne yake kawo musu kuɗi tare da yi musu kakin zinariya da azurfa. A lokacin da ta samu cikakken bayani sai ta nemi shawarar Boka a inda ta ce:

    To yanzu ya ya za a yi? Sai Bokon ya ba ta allurar tsafi, waɗanda in sun shiga jikin ɗan sarki, sai su zama ajalinsa. A yayin da ta tafi taɗi sai alluran suka shiga cikin jikinsa, da ya yi kaki sai jini (Yahaya, 1977 sh. 7).

    Haka kuma, idan muka dubi ɗaya ɓangaren, za mu ga ita ma ‘Yar Bora ta nuna kishinta a kan saurayinta, a inda ta yanke shawarar zuwa nemo masa magani, kamar yadda ya zo a tatsuniyar, a inda ‘yar Bora take cewa:

    Kai amma kuwa alƙawari bai ce haka ba. Duk inda maganin allurai yake a duniyar nan sai na samo masa shi (Yahaya, 1977 sh. 8).

    Babu shakka wannan kalami na ‘Yar Bora ya fito fili ya bayyana mana yada take kishin saurayinta. Sai dai shi wannan nau’in kishi ba na hamayya ba ne. Ya kasance na kyakkyawar fata ce da nuna ƙauna da ƙoƙarin bayar da kariya domin kuɓutar da masoyi daga halaka. Wannan lamari haka yake idan aka yi la’akari da yadda ‘Yar Bora ta aske kanta ta faɗa cikin ƙauyuka wajen neman magani. Ta fake da bara, har Allah Ya yi mata gamon katar, ta samu labarin maganin allurai. Duk da kasancewar maganin yana da wuya, domin sai an nemo wutsiyar ɗan autan dodo. Wannan bai sa ‘Yar Bora ta karaya ba, domin sai da ta yi ido biyu da dodanniya. Dodanniya ta ce mata:

    “Me ya kawo ki nan?”

    Ita kuwa ‘Yar Bora ta feɗe mata biri har wutsiya. Daga ƙarshe ta ce:

    Saboda rashin lafiyar nan tasa ne fa na je ina neman magani. Aka ce da ni sai na sami wutsiyar ɗan autan dodo, na jiƙa a sabon kasko ya sha sannan zai amaryar da alluran (Yahaya, 1977 sh. 10).

    Idan aka dubi wannan tatsuniya ta wata fuskar za a iya cewa, tatsuniyar tana ƙunshe da ɓirɓishin kishi nau’i-nau’i. Domin shi ma sarkin kansa ya nuna kishinsa a dalilin ganin ɗansa ya warke, har inda yake cewa ya ba ɗan almajiri rabin garinsa. Haka shi ma Ɗan Sarkin Agadas (dubi shafi na 18 – 19), ya fito fili ya bayyana kishinsa a lokacin da suka yi bankwana da ɗan almajiri, a inda ya ce:

    Ka ga kuwa ɗan almajiri, in Allah Ya yarda takobin nan sai ya sha jinin Jimmai, budurwata.

    Sai ɗan almajiri ya ce: Ba ka yi haƙuri ba? Sai ɗan sarkin ya ce: Ai wannan haƙurin ba zan yi shi ba.

    Dubi irin sharaɗin da ɗan almajiri ya gindiya wa ɗan sarki na cewa duk wani abu da zai yi, in an ce ya bari don ɗan almajiri to ya daina.

    Sakamakon tsananin kishin da yake tare da shi na ganin cewa saboda son da yake yi wa Jimmai ne ya faɗa cikin wannan masifa ta rashin lafiya, ga abin da yake cewa:

    Ai na gaya maka, garin sonta ne wannan cutar, wadda Allah Ya taimake ka kai kuma ka taimake ni ka warkar mini da ita, ta same ni (Yahaya, 1977 sh. 19).

    Wannan ba ya rasa nasaba da rashin zuwan Jimmai, domin ta duba shi a halin da yake kwance yana jinya. Amma kuma bai san Jimmai ce ta zama ɗan almajiri, ta samo masa maganin da ya sha, ya warke ba.

    Ba a nan kaɗai ta tsaya ba, domin a tatsuniyar an fito fili an nuna mana yadda ɗan sarki ya nuna kishin ɗan almajirinsa, duk da kasancewar ya sha alwashin sai ya kashe Jimmai a gaban ɗan almajiri; amma a lokacin da ya ɗaga takobi zai sare ta, sai ta ce masa:

    Ka bari don ɗan almajirinka mai zoben nan da ke hannuna (Yahaya, 1977 sh. 20).

    Wannan kalamin da ta yi ya sa jikinsa ya yi sanyi, ya ajiye takobinsa. Babu shakka kishin da ake yi wa ɗan almajiri a nan shi ne son da ɗan sarki yake yi masa, wanda har ya kai a matsayin idan zai yi abu, aka haɗa shi da shi, sai ya bari. Daga ƙarshe an nuna mana cewa ɗan sarki ya auri Jimmai, duk kuwa da irin makircin da Mowa ta ƙulla.

    3.4 Tatsuniyar Wata Tsohuwa Da Aljana

    Yayin da muka karkato linzaminmu ga tatsuniyar tsohuwa da aljana, a nan ma za mu tarar cewa, tatsuniyar tana ƙunshe da ɓirɓishin kishi. Kishin da ta ƙunsa, irin wanda sarakai suke bayyanarwa ne a kan wanda suke tsammanin zai gaje su; musamman idan ba daga cikin tsatsonsu ba ne.

    A wannan tatsuniya, an bayyana mana matakin da sarki ya bi a yayin da ya sami labarin haihuwar ɗa namiji da tsohuwa ta yi, wanda aka ce masa sai ya yi sarautar wannan birni. Sai sarkin garin ya fara tunanin yadda za a yi a halaka yaron. Daga ƙarshe ya tara fadawansa ya ce:

    Waye zai iya ɗauko wannan jinjiri a yanka shi? (Yahaya, 1982 sh. 6).

    Sarki ya nuna rashin tausayi saboda kishi ya riga ya yunƙuro masa. Har ma fadawansa suka nuna masa rashin dacewar ƙudurin sarki, duk da kasancewar fadawan sarki sun yi ƙaurin suna a kan rashin imani. Duk da haka, daga ƙarshe su suka bayar da shawarar, a saka shi cikin akwati a jefa a kogi. Hakan kuma aka yi. Ruwa ya tafi da shi.

    Bayan shekaru da dama da suka shuɗe, har yaron Allah ya raya shi ya girma, amma da sarki ya gan shi, kuma ya tabbatar da shi ne, kishi bai sa zuciyarsa ta sauya ba, a kan ƙudurinsa na kashe Na-Allah. Wannan ne ya sa sarki ya rubuta wa Madawaki takarda a inda ya umurce shi da ya sa a kashe yaron da ya kawo wasiƙar. Hasali ma ya ƙara ƙarfafawa da cewa:

    Kada a kuskura a bari ya kwana, in ya kwana, to a bakin ran Madawaki (Yahaya, 1982 sh. 10).

    Duk da kasancewar sarki ya bi matakai don ganin ƙarshen Na-Allah, amma a ƙarshe sai Na-Allah ya zama surikinsa, wanda daga baya kuma ya ɗare gadon sarautar garin bayan rasuwar sarki.

    4.1 Sakamakon Bincike

    Wannan bincike ya gano cewa, kishi shi ne babban sinadarin ɗorewar cigaban kowace irin al’umma a farfajiyar doron wannan duniya. Dalilin hakan kuwa shi ne, sai da kishin kai da kishin ƙasa da na al’umma ne mutane za su iya aiki tuƙuru domin ciyar da al’ummarsu gaba. Da kishi ne mutum zai aikata abin da zai amfane shi, sannan ya aikata abin da zai bayar da kariya tare da amfanar waɗanda yake ƙauna.

    A ɓangare ɗaya kuwa, an fahimce cewa kishi yana da nau’uka daban-daban. Akwai baƙin kishi da ya ƙunshi gaba da hamayya da ƙyashi. Wannan yakan kai ga yunƙurin ganin bayan wanda ake kishi ko ƙoƙarin bin matakan daƙushe shi domin tauraronsa ya daina haskawa. A gefe ɗaya kuwa akwai farin kishi da ya shafi soyayya da ƙoƙarin kare mutunci da daraja da martabar abin da ake kishi.

    Haƙiƙa kishi yana da babban gurbi a cikin al’adun Hausawa. Wannan ne ma ya sa tsattsafin kishi ya mamaye duniyar tatsuniyoyin Hausa. A matsayinsa na ɗaya daga cikin tubalan gina tatsuniyoyi, akan kawo nason kishi cikin sigogi mabambanta, kamar dai yadda aka gani a misalan tatsuniyoyin Hausa da aka bayar a sama.

    4.2 Kammalawa

    Tun da adabi madubi ne ko hoton hango rayuwar al’umma, samuwar nason kishi a cikin adabin Hausawa yana nuni da yadda kishi yake mazaunin ɓangaren al’adun Hausawa. Ana nuna hoton kishi ta hanyar mutane da dabbobi da sauran halittu da suke fitowa a matsayin taurari ko kayan cikin tatsuniya.

    Har yanzu tatsuniyoyi da sauran fannonin adabin gargajiya na Hausawa ba su zama tsohon yayi ba a ma’aunin ilimin duniya. Ana iya gudanar da nazarce-nazarcen zamani domin sake yi musu fasali da na’urantar da su. Labaran za su iya kasancewa a cikin sababbin littattafai da odiyo-odiyo da bidiyoyi da kuma manhajoji, ɗauke da labaran da bayanan darussan da suka ƙunsa.

    Manazarta

    Abdulmalik, H. A. (2000). Tasirin kishi a littattafan soyayya na zamani: Nazari daga wasu littattafan Balkisu Ahmad Funtua [Bachelor’s thesis, Usmanu Ɗanfodiyo University].

    Abraham, R. C. (1975). Dictionary of the Hausa language. University Press.

    Al-Asƙalami, I. H. (n.d.). Bulugul-marami.

    Baba, A. (n.d.). Masu hikima sun ce. The Library of the University of California, Los Angeles.

    Baƙi, A. I. A. (1997). Ƙamus na Turanci da Larabci da Hausa. Hudahuda Publishing Company.

    Bakura, A. R., & Sani, A.-U. (2022). Kishi a bakin makaɗan baka. South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature, 4(2), 45–57. https://doi.org/10.36346/sarjall.2022.v04i02.002

    Bargery, G. P. (1934). A Hausa-English dictionary and English-Hausa vocabulary. Ahmadu Bello University Press.

    Bashir, A. M., & Others. (1986). Alƙur’ani maigirma: Fassara da bayanai, kashi na farko. Continental Book Centre.

    Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben adabin Hausa da muhimmancinsa ga rayuwar Hausa. Triumph, Gidan Sa’adu Zungur.

    Dar-El-Ilim Lil-Malayen. (1986). Al-maurid al-qarib.

    Dikko, I., & Macciɗo, U. (1991). Ƙamus na adon maganar Hausa. Gaskiya Corporation.

    Dumfawa, A. A. (1999). Matsayin mata ga idon ‘yan Boko da kuma gargajiyar Bahaushe. In Taron Ƙara Wa Juna Sani, Sashen Harsunan Nijeriya, Usmanu Ɗanfodiyo University.

    Edgar, F. (1913). Littafi na tatsuniyoyi na Hausa. Belfast Maine.

    Fodiyo, S. A. (n.d.). Kitabu adabil-adati ala sunnati rasuli wa tabi’ihi assadati (Zaki Aliyu Giɗaɗawa, Trans.).

    Gale, G. (Ed.). (2001). Gale encyclopedia of psychology (2nd ed.). Gale Group.

    Garba, C. Y. (1990). Ƙamus na harshen Hausa. Evans Brothers.

    Guau, S. M. (n.d.). Wasanni da waƙe-waƙen yara a ƙasar Gusau. Kungiyar Hausa, Bayero University.

    Gummi, A. (1979). Tarjamar ma’anonin Alƙur’ani maigirma zuwa Hausa. Darul-Arabia.

    Gusau, S. M. (1984). Adabin Hausa na gargajiya: Ma’anarsa da yanaye-yanayensa. In Taron Raya Harshen Hausa.

    Gusau, S. M. (2013). Tatsuniya a rubuce: Nazarin sigogi da hikimomi da tasirin tatsuniya. Century Research and Publishing Company.

    Heiman, A., & Iyon, S. (1998). Jealousy: Are we doomed? NSII Chris Myers.

    Idris, A. (n.d.). Zadul-muslimati.

    Ingawa, Z. S. (1989). Kishi a ƙasar Hausa: Yanayi da amfani da illolinsa. In Makon Hausa na sha-tara, Bayero University.

    Jinju, M. H. (1981). Rayayyen nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company.

    Kabara, N. (n.d.). Tafsiri tare da fassara ga ma’anonin Alƙur’ani maigirma zuwa harshen Hausa. Maktab al-ƙadiriya.

    Kano, C. N. H. B. U. (1993). Nazari a kan harshe da adabi da al’adu na Hausa (Vol. 3). Gaskiya Corporation.

    Knight, K. (1999). The Catholic encyclopedia. New York.

    Longman. (1978). Dictionary of contemporary English. Longman Plc.

    Muhammad, S., & Yahaya, I. Y. (n.d.). Darussa a kan adabin Hausa. Institute of Education, Ahmadu Bello University.

    Newman, P., & Others. (1977). Sabon ƙamus na Hausa zuwa Turanci. University Press.

    Newman, R. M. (1997). An English-Hausa dictionary. Longman.

    Patrick, H. (Ed.). (1971). The New Hamly encyclopedic world dictionary (1st ed.). The Hamly Publishing Group.

    Peter, S. (1991). The psychology of jealousy and envy. Cat Press.

    Sulaiman, A. (1999). Namijin dare da hukuncin aure tsakanin aljanu da mutane.

    Talata Mafara, M. I. (2000). Kishi da zamantakewar ma’aura a Musulunci. Bamoya Printing Press.

    Umar, M. B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun gargajiya. Triumph, Gidan Sa’adu Zungur.

    Yahaya, I. Y. (1971). Tatsuniyoyi da wasannin yara (Vols. 1–6). Oxford University Press.

    Yahaya, I. Y. (1984). Kishi feeling amongst Hausa co-wives. Kano Studies, 1.

    Yahaya, I. Y. (1994). Labarun gargajiya (Vols. 1–2). University Press.

    Yahaya, I. Y., & Rufa’i, A. (Eds.). (1978). Studies in Hausa language, literature, and culture: The first Hausa International Conference. Bayero University Press.

    Yahaya, I. Y., et al. (1992). Darussan Hausa: Don manyan makarantun sakandare (Vols. 1–3). University Press.

    Yahaya, I. Y., et al. (Eds.). (1982). Harsunan Nijeriya XII. Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.

    Zariya, N. N. C. (1985). Labaru na da, da na yanzu. NNPC.

    Danna nan don karanta Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Dila Da Zomo

    Tatsuniyar Dila Da Zomo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Dila ya haɗu da Akuya. Bayan sun gaisa sai Dila ya tambayi Akuya ko za ta ba shi ɗaya daga cikin ’ya’yanta su je bakin kogi shan ruwa? Akuya ta amince amma fa da sharaɗi. Sharaɗin shi ne tana so Dila ya lura da ’yarta sosai kar wani mugun abu ya same ta. Shi kuma Dila ya amince da haka.

    Da Dila da ’yar Akuya suka isa bakin rafi sai suka tarar wuta na ci a wani rami da ke kusa da kogin. Tun da ’yar Akuya ba ta da cikakken wayo, sai Dila ya ce mata shi zai shiga ruwan, ita kuma ’yar Akuya ta shiga ramin da wuta take ci. ’Yar Akuya ta bi
    maganar Dila, ta shiga ramin, wuta ta cinye ta.

    Bayan Dila ya gama kiwo sai ya zaro naman ’yar Akuyar daga ramin, ya cinye. Ya kama hanya, bai tsaya ba sai gidan Akuya, ya fashe da kuka ya ce mata ruwa ya cinye ’yarta. Akuya ta haƙura, amma abin ya yi mata ciwo. Daga nan Dila ya tafi wurin Zomo, ya nemi a ba shi ɗaya dagacikin ’ya’yansu domin su je rafi.

    Aka amince, amma da sharaɗin cewa idan ɗan Zomo zai kai kifi da yawa gida. Dila da ɗan Zomo suka je bakin ruwa, suka shiga. Dila ya yi ta iyo, amma ɗan Zomo da bai iya ruwa ba, ya tsuguna yana kallo. Jim kaɗan Dila ya sa shi ya shiga ramin da ke can gefen rafin wuta na ci a ciki. Sai dai a wannan karon wayon Dila bai yi aiki ba.

    Ɗan Zomo ya ƙi shiga ramin. Maimakon ya shiga, sai ya tuɓe takalmansa, ya jefa su a ciki, ya koma gefe ya ɓuya. Dila kuwa sai ya shiga murna, yana zaton ɗan Zomo ma ya yi irin ta ’yar Akuya. Da Dila ya gama iyo sai ya zaro takalmin ɗan Zomo da ya sha wuta, ya cinye. Ya sha ruwa, ya kama hanya ya tafi gida.

    Tsammani yake naman ɗan Zomo ya cinye. Dila bai sani ba ɗan Zomo na ɓoye a cikin jakarsa. Saboda haka a lokacin da Dila ke kan hanyar komawa gida, sai ɗan Zomo ya kama waƙa yana cewa:

    “Dila ashe kai wawa ne,

    Dila ashe kai wawa ne,

    Ka cinye takalmina,

    Tsammani kake ni ka cinye.”

    Da Dila ya ji waƙa sai ya ce:

    “Ke jakata, ashe kin iya waƙa haka?”

    Bai tsaya ba, har sai da ya isa gidan Zomo. Ya je yana kuka sharaf- sharaf, hawaye sun cika masa fuska, kamar abin tausayi. Amma tun kafin ya yi wa iyayen ɗan Zomo ƙaryar kogi ya cinye musu ɗa, sai ɗan Zomo ya yi farat ya fito daga cikin jakar Dila. Tun kafin Dila ya ce da uwar Zomo ɗanta ya mutu a ruwa, sai ɗan Zomo yace:

    “Ƙarya yake cewa kogi ya tafi da ni. Abin da ya gaya mini shi ne in faɗa cikin wuta don wutar ta ƙone ni, wai shi zai yi iyo. Dabara na yi na tsira daga sharrinsa, domin da na shiga ramin, to da wuta ta cinye ni, ya sami nama ke nan. Maimakon in faɗa wutar ne na jefa takalmana.

    Shi kuwa Dila da ya fito daga iyo ya cinye takalman da suka sha wuta. To bai yi sa’a ba, mugun nufinsa ya ci tura.” Nan take sai ɗan Zomon ya kawo shawara cewa, lalle ne su shaidawa Sarkinsu saboda abin da ya faru da ’yar Akuya haka ya kusa faruwa da shi. Da suka kai ƙara, Sarki ya ba da umurni dogarawansa su kama Dila su je su fille masa kai a bayan gari. Haka kuwa aka yi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Ba a rama kirki da mugunta.
    • Kowa ya ci amana sai amana ta ci shi.
    • Wayo ya kada sarkinsa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Kura

    Edita@rumasau-kallamu