Tag: malaria

  • Cizo Nawa Sauro Take A Kamu Da Malaria?

    Cizo Nawa Sauro Take A Kamu Da Malaria?

    Cizo ɗaya tak yakan iya saka Malaria, macen sauro da ake kira da Anopheles mosquito ce take wannan ta’asar. Tana ɗiban jinin mutum ne wanda yake ɗauke da microscopic malaria parasite.

    Alamomin malaria suna bayyana ne daga kwana na farko zuwa kwana 30 bayan mutum ya kamu da cutar duk da cewar ya danganta da yanayin kalar parasite ɗin, yayin da wasu ma ba sa rashin lafiyar har tsawon shekara guda, duk da cizon na sauron haka kuma cutar parasite ɗin ka iya zama shekara da shekaru ba tare da alamomi sun bayyana ga wanda sauron ya ciza ba.

    Komai yana da amfani da kuma rashin amfani

    Sauro yana da amfani ga al’umma domin kuwa idan har ka yi haƙuri da cizon sa to zai zama silar kankare maka zunubi da kuma samun lada.

    Kuma kamar “ƙudan zuma” da kuma “malam buɗa mana littafi” haka sauro yake saka pollen daga flower zuwa wata flower ɗin sakamakon samun abincinsu a nectar wanda hakan yake sa tsirrai su haɓaka. Daɗin daɗawa: ba wai jini ne abincin macen sauro ba, pollen flower ita ce abincinta, jinin kawai ana sarrafa shi ne wajen ƙwayaye.

    Yaɗa cutar Malaria shi ne babban rashin amfaninsu sakamakon cutar Malaria ita ce ta fi kowacce cuta saurin kisa a cututtukan duniya baki ɗaya Kamar yanda masana bincike suka faɗa. Amman mu a matsayinmu na musulmai sai dai mu ce komai da Allah SWT ya yi akwai hikima a ciki ko mun gane ko ba mu gane ba, domin kuwa zazzaɓin Malaria ko kuma waninsa zai zamo silar kankarewar zunubban musulmi ne kamar dai yanda cizon cinnaka zai zamo silar kankarar zunubi (Cikakken bayanin zai zo a littafin da zan wallafa mai suna: AMFANIN CIZON CINNAKA)

    Wannan dalilin ne yasa ma’aiki (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar da mu adduar da za mu dinga faɗawa mara lafiya yayin dubiya: “Laba’atha ɗahuran insha Allah” ma’ana “Tsarkakewa ne (daga zunubbai) da yardar Allah”

    (Sahihul Bukhari)

    YANDA ZA MU MAGANCE CIZON SAURO 

    Mu yawaita Istighfari a dukkanin al’amuran mu domin kuwa idan Allah Azzawajallah ya ga dama sai ya halakar da kai da cizon macen sauro ɗaya tak sakamakon zunubban da kake aikatawa musamman na ɓoye. 

    Akwai magungunan sauro kala-kala musamman waɗanda suke da alaƙa da hayaƙi. Dalilin da ya sa sauro ba ya son hayaƙi shi ne: akwai cikakkiyar iska (oxygen) wadda take shiga ramukan (cavities) da ke jikin sauro (spiracles) waɗanda su ne kamar hancinsa da suke a doron jikinsa. Hayaƙi yana ɗauke da wasu particles da idan sauro ya shaka suke fasa hunhunsa, hayaƙin kan hana sauro shaƙar tsaftatacciyar iska, shi yasa ba ya buƙatar kusantar inda aka saka maganin sauro (mosquito coils).

    Akwai magungunan sauro na shafawa a jiki kamar irinsu “Gardia mosquito repellent cream” wanda gaba ɗaya sauro baya son shi saboda yana ɗauke da diethyltoluamide kaso 13% wanda yana da matuƙar haɗari ga rayuwar sauro shi yasa ba ya iya sauka fatar mutum yayin da ya shafa maganin.

    A ƙarshe ina son in ja hankalin mu da mu yawaita tsaftace muhallin mu domin kuwa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: “Tsafta tana daga cikin cikin Imani” (Sahihul Bukhari)

    Danna nan don karanta cikakken littafin

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Yadda Zaku Magancewa Marasa Lafiyarku masu Cutar Malaria

    Yadda Zaku Magancewa Marasa Lafiyarku masu Cutar Malaria

    Wannan Bayanin nayi sa ne musamman domin kananun ma’aikatan lafiya dake matakin farko,saboda idan aikin ku ya gyaru ba bukatar ace sai me malaria yakai ga babban likita. Inkuma kunƙi ku gyara tofa mara lafiya inyasan wannan karku ji haushi inyazo yana gyara muku aiki.

    Malaria Babbar cuta ce dake sawarwarin rayukan bayin Allah sama da dubu ɗari shida da talatin duk shekara musamman tsakanin yara ƴan kasa da shekara 5, mata masu ciki,da mutane masu raunin garkuwa jiki.

    Tana Zuwa Da Duk Wasu Alamomi Da Baku Zaton Nata Ne, Kamar:
    • Tsananin kasala
    • Fita daga hayyaci
    • Jijjiga
    • Wahalar numfashi
    • Canzawar ido zuwa ruwan ɗorawa
    • Canzawar fitsari zuwa ruwan coca-cola ko kuwa jajur da jini
    • Murdawar ciki
    • Fitar jini ta hanci da baki ko kunnuwa.

    Duk wadannan kadan ne daga aikin malaria.

    Ƙaramar malaria ce ke zuwa da zazzaɓi, rawar sanyi,da ciwon kai,inta ratsa jiki ta wuce da karamin sanin mutum.galibi wadancan manyan alamun kananun ma’aikata ke kuskuren daukar su a matsayin alamun cutar typhoid.

    Karanta cikekken Mataki Domin Kare Kanka Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda Danna nan

    Binkicen da mukai mun fahimci cikin mutum 100 na masu malaria kwata-kwata mutum 10 ke bukatar maganin typhoid,kuma 10% din basu nema ake ba maganin typhoid din ba,wannan ke nuna duk wanda ake ba maganin typhoid yayin treatment din malaria ƙwata-ƙwata basa buƙatar hakan. Erroneous practice ne.

    Galibi sanda malaria ke bayyana mutum yakai kimanin kwana 10 zuwa 15 da haduwa da cizon sauron,bawai irin dare ɗaya dinnan don kaji ciwon kai tunanin sauron jiya da daddare bane,domin idan sauro ya zuba maka merozoites cikin jini zuwa hantarka anan ne ƙwayayen zasu zauna don kyankyashe kansu “Schizonts” a tsawon kwana 10 sannan alamun malaria su fara bayyana.

    Wanda rashin maganceta da kyau ko kasha maganin malaria ko allura bayan kwana 3 ragowar wadancan ƙwayayen kan ƙara kyankyashe kansu kaji ciwon ya dawo sakamakon rashin treatment me kyau.

    Take Home Message 

    Akwai wani abu da nake son ƙananun jami’an lafiyar mu ku kiyaye kuma ku dauka da muhimmanci wanda indai kuka gyara hakan zai sa treatment success dinku na malaria yai matukar sama,za’a rage yawan dawo muku akan ciwon malaria.

    • Awon  Nauyi:

    Sanin nauyin mara lafiya abinda muke kira weight nada matukar muhimmanci,galibi kuskuren farko daga nan yakan fara, kukan lamincewa kanku kurum indai mutum Adult ne duk magani guda zaku basu,haka childrens,kuyi ƙoƙari ku tanaji weight scale a guraren aikinku koda da kudin aljihunku ne.

    Domin karanta cikekken bayani akan Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura} Danna nan 

    • Idan zakai wa mutum allurar ARTEMETER  kasani dole ka auna saboda duk kilo ɗaya na nauyin mutum sai ka bashi 3.2milgram nata,ita duk ƙwalbar artemeter tana zuwa ne a 80mg dama.

    Misali 

    (1) Bayan ka auna nauyin Sa’adiyah ko Umar me dauke da malaria a scale sai kaga 55kg ne,don haka adadin artemeter dinsa zai kama 3.2 × 55 wanda shi zai baka 176 Milgram wannan shine adadin da zaka basu duk bayan awa 12 na tsawon kwana uku.

    Toh kaga kuskuren mutanen mu kuke yi ku kurum inde babban mutum ne ƙwalba biyu kuke fashewa kuyiwa mutum wanda 80×2=160mg kacal,alhalin sadiya da umar 176mg suke bukata,kunga taya malaria kota lafa bazata dawo ba bayan kwana biyu?. Ƙwalba wajen biyu da kusan rabi suke bukata.

    (2) Fatima ita da yake me ƙiba ce sosai bayan an auna nauyinta sai kaga 97kg ce, toh in zakai mata amfani da artemeter dole zaka ce 3.2×97=310.kaga ita fa magana ake ta saika fasa ƙwalabe 4 bawai biyu ba.

    (3) Amma ita Farida dake babu auki daka auna sai kaga 38kg ce kacal,don haka zai kama 3.2×38=122. kaga ita kwalba biyu ma yai mata yawa domin ƙwalabe biyun 160mg ne. ita kuwa 120mg ne daidai da ita,bata duk kwalba biyun ba amfani.

    • Idan kuma ARTESUNATE CE ita ma kaga tana zuwa duk kwalba kode 30mg ko kuma 60mg.

    To ita duk kilo guda na nauyi kana buƙatar ka bada 2.4mg ne muddin nauyin mutum ya wuce 20kg,amma idan yaro ne wanda bai kai 20kg irin yan kasa da shekara 5 dinnan to su 3mg ne duk kilo.

    Misali:

    (1) Asama’u me nauyin 62kg zakai mata artesunate,toh zaka ce ne 2.4×62=149,toh kaga ita 149 ko kace 150mg take buƙata, kaga sai ka bude kwali 2 na artesunate me 60mg da kuma kwali daya me 30mg sannan zaka sami daidai dose din da kake buƙata.

    Sannan bayan awa 12 ka ƙara mata hakan,sannan bayan awa 12 ka ƙara mata hakan bayan wata awa 12 din,kaga a 24hrs ta sami 150mg sau uku kenan,0hrs sanda kara,12hrs da kuma 24hrs.

    To daga nan idan a allura zaka dorata tsawon ƙwana ukun sai acigaba da bata 150mg kullum tsawon kwana 3,daga randa akai ta kwana 3 din sai kuma adorata kan maganin sha na wasu ƙwanaki uku din koda ana ganin ta warke hakan shine ka’ida walau Lonart, ACT, ko Camosunate, dade sauransu.

    Idan kuma after 24hrs akan maganin sha ta baki zaka dorata toh saika dorata kan na kwana 3,anan ne zaka iya ƙara mata da antibiotic wanda yake da tasiri wajen kashe ƙwayayen bacteria a hanta kamar doxycycline ko clindamycin.

    (2) Baby khadija yar wata 6 me nauyin 10kg in zakai mata amfani da artesunate zaka ce ne 3×10 = 30mg,toh ita kwalin artesunate me 30mg kwaya daya a 0hrs, 12hrs & 24hrs kenan, kaga kwali uku ya isheta daga nan in akan allura zata tafi itama sai acigaba da mata 30mg wato kwali daya kullum tsawon kwana 3. daga nan kuma ka bata ACT 1 tablet ko suspension ko dai wani antimalarial din daidai da shekarunta ta cigaba na wasu kwanaki ukun.

    • Idan kuma ARTEETHER ce wato EMAAL toh ita kuma duk kg kana bukatar bada 3.0mg walau babba ko yaro.

    Misali: 

    Khadija me nauyin 45kg in zaka bata emal 3.0×45= 135. kagaa ita 135mg kenan,duk ƙwalba tana zuwa ne 90mg,kaga ƙwaba biyu zaka fasa ka zuƙi rabin ta ka hada da guda daya.

    Bayin Allah atakaice dai wannan shine regimen na malaria treatment,kunga yadda amfani da nauyi kacal zai gyara maka aikinka.

    • Inde anyi aamfani da allura na kwana uku kowacce iri ce Rekmal,Artesunate, Artemeter ko Emal dole abi da maganin sha na ƙwana uku koda an warke.
    Toh haka zalika akwai wasu rukunin mutane da kwai buƙatar lura.
    • Me cikin da take da malaria anso a kauracewa bata ACT ko coartem musamman a watanni ukun farko. QUININE shine maganin da ya dace da ita, abata 20mg per kg.
    • Amma inya girma ana iya bata ACT din ma musamman 3rd trimester.
    • Haka wanda zaije garin da yake da sauro yana iya fara shan doxycycline ɗaya safe,ɗaya yamma kullum har yaje ya dawo garinsu,hakan rigakafi ne,musamman ga yan kasar waje,ko wanda ke shirin zuwa Kano.
    Batun Paracetamol 

    Shi walau allura ko na sha a baki kurum 10mg per kg ne,shima kuskure ne kace biyu safe,biyurana,biyu yamma,idan mutum me kilogram 70 yazo kaga 10×70= kaga 700mg yake bukata duk bayan awa 8,bawai safe rana dare ba,batu ne na awoyi,har tsawon yini gudu ko kwana uku idan zazzabin bai sauka ba,haka ma yara 10mg per kg.

    A kwai wani Practice da zan so duk kananun jami’an lafiya su gyara aikinsu su daina! wato rubuta antibiotic yayin treatment din malaria. Da yawa sun tafi akan cewa indai ansami malaria toh akwai typhoid… wannan kuskure ne,ba haka abin yake ba.

    Ku duba ma’anar typhoid fever da kyau zaku fahimci lallai typhoid ba abu ne me sauki ba irin yadda ake kallon kowanne gastric symptoms matsayin typhoid.

    Kurum inka duba kaga malaria na damun mutum bashi iya maganin malaria,koda hakan na nufin magani kala ɗaya zaka bashi…kurum bashi ka sallamesa,ba sharadi bane ko yaushe sai kaba mutum tarin magunguna. Antimalarial ko ba paracetamol is Ok.

    Sannan idan kasan allura kadai zaka dora mutum akai ta malaria tsawon kwana uku to ku sani bayan anƙare allurar kasha gari dole ya dora da maganin malaria nasha tsawon kwana 3 zuwa 5,ba’a allura ita kadai muddin ba a asibiti mutum yake a kwance ba,rashin irin wannan kesa ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa,ballantana da.

    Shiga nan domin karanta Abubuwa Wanda Yakamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada

  • Malaria In Pregnancy

    Malaria In Pregnancy

    Malaria: Rashin lafiya ce da ake samunta sanadiyyar cizon macen sauro,wadda take sakawa mutum ƙwayoyin cutar malaria a cikin jini.

    A na samun cutar ne a sanadiyar ƙwayoyin cutar da macen sauro ke zubawa mutum acikin jini.

    Ƙwayar cutar da take kawo malaria a Najeriya ana kiran ta da plasmodium falciparum.

    Mata masu juna biyu suna daga cikin mutanen da idan malaria ta kama su rayuwar su yana cikin hatsari.

    Malaria tana kawo waɗannan matsaloli ga mata masu juna biyu:
    • IUFD (Mutuwar yaro kafin a haife shi
    • Abortion (ɓarin ciki)
    • Preterm delivery (haihuwan baƙwaini)
    • A karshe uwar da yaron dukka za su iya rasa rayuwar su.
    Kuma Malaria Tana Iya Kawo:
    • Rashin jini a jiki 
    • Matsalar ƙwaƙwalwa
    • Matsalar ciwon zuciya
    • Matsalar huhu da oda
    • Kumburi ko fashewar spleen .
    • Yana saukan da suga hypoglycemia
    Alamomin Malaria Sun Hada Da:
    • Zazzabi
    • Ciwon kai
    • Tashin zuciya
    • Amai
    • Gudawa
    • Ciwon jiki
    • Atini
    • Ɗachin baki
    • Rashin cin Abinci
    • Rashin ƙarfin jiki.
    • Kasala
    • Mutun yaji ya rasa abinda yake masa dadi.
    Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Malaria:

    Mace me juna biyu ya kamata tafara zuwa awun juna biyu (ANC) akan lokoci,lokocin awu ana bada maganin kariya daga kamuwa da cutar malaria ga mata masu juna biyu,ana bada:

    Fansider (sulfadoxine-pyrimethamine) wani magani ne wanda ake bawa mata masu juna domin kariya daga cutar Malaria.

    Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether 

    Ana bada maganin ne da zarar mace cikin ta yakai watanni hudu (16weeks), sannan abada 2nd dose a 20-22 weeks sannan a bada 3rd dose a 26 weeks(akalla ana so a samu tazarar sati 4 tsakanin ko wacce dose),kuma anaso mace tasha wannan maganin a kalla so takwas (8) kafin tahaihu.

    Sannan ana bada gidan sauro,da wasu shawarwari da mace za tabi ta kare kanta daga kamuwa da cutar malarian,idan an fara jin alamomin malaria za’a iya shan maganin malaria?

    A’a,a matsayin na mace mai juna biyu ba ko wane magani ya kamata kisha ba ko da ace kin tabbatar kina da malaria,domin mafi yawan magungunan malaria mata masu juna biyu bai kamata suyi amfani da shi ba.

    Haka kuma shan magani barkatai ba bisa ka’ida ba yana kawo resistance( ma’ana ƙwayoyin cuta su dinga jure maganin,baya kashe su.)

    Abinda ya kamata kiyi shine kiyi kokorin zuwa asibity a miki abinda ya dace.

    Domin karanta bayani akan Noristerat (Norist) Danna nan 

  • Malaria

    Malaria

    Malaria: Wannan wani rashin lafiya ne da ake samunsa ta sanadiyyar cizon macen sauro, wadda take sakawa mutum kwayoyin cuta a cikin jini.

    A na samun cutar ne a sanadiyar ƙwayoyin cutar da macen sauro ke zubawa mutum acikin jin

    ƙwayoyin Cutar Da Suke Kawo Malaria:

    •  P falciparum
    •  P Vivax 
    •  P ovale
    •  P malarias
    •  P knowlesi

    Amma amfi samun p falciparum a Nigeria shi yasa mafi yawan magani da ake amfanida shi na malaria a Nigeria ACT ne.

    Ga Wasu Daga Cikin Alamum Malaria:

    •  Zazzabi
    •  Ciwon kai
    •  Tashin zuciya
    •  Amai
    •  Gudawa
    •  Ciwon jiki
    •  Atini
    •  Dachin baki
    •  Rashin cin abinci
    •  Rashin ƙarfin jiki.
    • Kasala
    • Mutum yaji ya rasa abinda yake masa dadi.
    Ga Wasu Daga Cikin Mutane Idan Malaria Takamasu Rayuwarsu Take Cikin Hatsare:
    • Mace mai ciki
    • Yara ƙanana
    • Masu cutan sickler
    Malaria A Mace Mai Ciki Yakan Kawo Mata:
    • Haifan macaccen jariri
    • Yakan zubar mata da ciki.
    • Yakan kawo haihuwar bakwaini .
    • Yakan kashe uwar da yaron gabaki daya.
    Ya’ake Gane Mutum Yana Dauke Da Ƙwayar Cutar Malaria:

    Ana gane malaria ne ta hanyoyi guda biyu wanda dukkansu jini ake gwadawa

    sune:

    • RDTs malaria test
    • Microcopy malaria test
    Matsalolin Da Malaria Yake Kawowa (Complication of malaria) 
    •  Rashin jini a jiki 
    •  Matsalar ƙwaƙwalwa
    •  matsalar ciwon zuciya
    •  Matsalar huhu da oda
    • Kumburi ko fashewar spleen .
    • Yana saukan da suga (Hypoglycemia)
    Hayoyin Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Malaria:

    SPAQ (sulfadoxine-pyrimethamine + amodiaquine) wannan wani maganine  wanda ake bawa yara ƙanana masu watanni 3 zuwa 59 domin kariya daga cutar malaria.

    ƙungiyoyin lafiya ta cikin gida da ta dubiya sun dauki nauyin bada wannan maganin kyauta a Najeriya duba da yanayin yadda rayuwar yara kanana take shiga hatsari idan suka kamu da malaria. Domin sanin Mene Ne Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria) Shiga nan

    Ana bada maganin lokocin da ruwa yafara sauka wato tsakanin July da October domin shine lokocin akafi samun ciwon malaria.

    Note: 

    •  Yaro mai zazzabi ba’a bashi
    •  Yaron da yasha septrin ba’a bashi
    •  ba’a hadashi da ko wane irin maganin malaria.

    Fansider (sulfadoxine-pyrimethamine) shi ma wani maganine wanda ake bawa mata masu juna domin kariya daga cutar Malaria.

    Ana bada maganin ne da zarar mace cikin ta yakai watanni hudu (16weeks), sannan abada 2nd dose a 20 – 22 weeks sannan a bada 3rd dose a 26 weeks (akalla ana so a samu tazarar sati 4 a tsakanin ko wace dose).

    Akwai sauran magunguna da ake amfani da sui domin kariya daga malaria

    Kamar Su:

    •    Proguanil
    •    Doxycycline
    •    Daraprim
    Sauran Hanyoyin Sun Hada Da:
    • Shiga gidan sauro.
    • Daina barin ciyawa cikin gida .
    • kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida dan kada sauro su samu wurin zama.
    • Kwashe shara akai-akai kada abari tata ru a gida.
    Maganin Zazzabin Cizon Sauro:

    Maganin zazzabin cizon sauro shine duk sanda aka ji rashin lafiya a ziyarci asibity domin a tabbatar daganan likita yabada magani .

    Idan Naji Zazzabi Zan Iya Shan Coartem?

    A,a baza kasha ba sabida shan magani barkatai yana da illa , kuma an hana shan maganin malaria batare da an aunaka an tabbatar kanada malarian ba.

    Mafita shine idan kaji wayennan alamomi kaje asibity mafi kusa da kai domin ba malaria kadai bane yake kawo wadannan alamomin ba

    Domin karanta bayani akan Kansar Bakin Mahaifa Danna nan

  • Mene Ne Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)

    Mene Ne Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)

    Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria) cuta ce da take damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta, tana ɗaya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata.

     Ma’anar Malaria

    Malaria cuta ce wadda take saka zazzaɓi da ciwon jiki, waɗanda za mu yi bayaninsu a nan gaba kaɗan.

    • Yadda ake kamuwa da malaria

    Asalin abin da yake janyo cutar shi ne shigar wata ƙwayar halitta da ake kira ‘plasmodium’ cikin jinin mutum

    Ita wannan plasmodium ba ta shiga jinin mutum kai tsaye, sai ta hanyar sauro. Ma’ana dai, sauro shi ne wanda yake yaɗa wannan ƙwayar halittar (plasmodium).

    Shi sauro yana yaɗa wannan cutar ne a tsakanin mutane (daga mutum zuwa wani mutum daban) a yayin da yake neman abinci, wato jini. Ma’ana dai, abincin sauro shi ne jini.

    • Alamomin cutar Malaria

    Idan sauro ya ciji mutum, kuma ya saka masa wannan plasmodium ɗin a cikin jininsa, to ba a lokacin zai fara jin alamun ciwon ba, har sai bayan wasu kwanaki.

    Alamomin ciwon sun haɗa da:
    • Zazzaɓi
    • Ciwon kai
    • Jiki yana ciwo
    • Gaboɓi suna ciwo
    • Kasala
    • Amai
    Idan ta yi tsanani, za ta iya haddasa:
    • Fita daga hayyaci
    • Jijjiga
    • Ƙarancin jini
    • Rasa rai….Da sauransu

    Hanyoyin kariya daga cutar malaria 

    Kamar yadda aka yi bayani a baya, ita wannan cuta dai sauro ne yake yaɗa ta. Don haka duk wata hanya da mutum zai bi don yaƙar sauro, to wannan hanyar za ta iya kare shi daga samun wannan cutar.

    Waɗannan hanyoyi sun haɗa da:

    (1) Hana sauro haihuwa

    (2) ka hana sauro ya cije ka (ya sha jininka)

    (3) Kashe sauron.

    Hana sauro haihuwa:
    • Gyara kwatoci: A daina barin ruwa yana zama a cikin kwatoci ba tare da yana gudana ba. Sannan kuma a rufe kwatocin.
    • A daina barin ruwa ya daɗe a buɗe a cikin muzubi.

    Yadda zaka hana sauro ya cije ka:
    • Amfani da gidan sauro (wato Insecticide Net): Ma’ana kwana a cikin gidan sauro.

      Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
      Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
    Yadda za a kashe sauro:
    • Amfani da maganin sauro na fesawa ko kuma na hayaƙi.
    • Abin da ya kamata mutum ya yi idan ya ji alamun cutar.

    (1) Idan akwai zazzaɓi, musamman a yara ƙanana, to sai a samu tsumman zani ko tawul a tsoma shi a ruwa (ba ruwan zafi ba, ba kuma ruwan sanyi ba), kamar dai ruwan fanfo.

    Sannan sai a matse ruwan, sai a cirewa yaron rigar sa, sannan sai a riƙa ɗan daddana jiƙaƙƙen tsummman a jikin yaron (ko’ina da ina) musamman inda ya fi zafi. Za a yi ta maimaita haka, har sai jikin ya yi sanyi (zazzaɓin ya sauka).

    (2) Ai maza a garzaya asibiti.

    Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
    Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)

    Abubuwa masu mahimmanci:

    Malaria daban, Typhoid daban. Zan yi bayanin zazzaɓin Typhoid nan gaba.

    • Amma dai yakamata a sani cewa:
    • Malaria ba ɗaya take da Typhoid ba
    • Typhoid ya yi ƙaranci a cikin al’ummarmu matuƙa da gaske musamman idan aka kwatanta ta da Malaria.
    • A guji yin allura da zarar ana zazzaɓi. An fiso asha ƙwayar magani idan ana zazzabi saboda yin allura kan iya haifar da wasu matsalolin.
    • A guji yin allurar jijiya idan ana yin zazzaɓi. Allurar jijiya tana da haɗari ƙwarai da gaske. Tana iya haifar da matsaloli iri daban-daban. Idan aka yi kuskure, mutum zai iya rasa ransa.

    Sai an samu ƙwaƙƙwaran dalili, likita yake umarni a yi allurar jijiya, kuma idan za a yi, to sai ƙwararren me yin allura ne zai yi (Nurse ko likita).

    Kammalawa.

    Cutar zazzaɓin cizon sauro(malaria), cuta ce da ta addabi mutanen Africa. A kowane lokaci ko kuma daƙiƙa sai an samu wanda ya mutu ta dalilin cutar malaria.

    Don haka mu kare kanmu daga kamuwa da wannan cuta sannan kuma mu guji yin allura (ta jijiya da ta tsoka) da zarar an fara zazzaɓi

    karanta yadda ake kare kai daga ciwon sanyi (toilet infection) ko Mene ne taifud (TYPHOID) ko mene ne zazzaɓin cizon sauro (MALARIA) danna koren rubutu