Tag: Ado Da Kwalliya

  • Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci

    Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci

    Mafi yawan mutane a wannan zamani, sun afu da sha’anin ado da kwalliya, musamman mata waɗanda a kullum ake ƙirƙiro musu da kayan ado da sanyawa iri-iri.

    Har ta kai wasu kayan kwalliyar na iya kawo tangarɗa ga lafiya da tattalin arziƙi da sauran su. Ga alama wannan ce ta sanya malamai su ka tashi tsaye wajen karantuwa da wayar da kai a kan illolin wasu daga kayan ƙawa (ado) na mata, domin kare su daga matsalolinsu.

    Amma kuma yawanta yin suka da bayyana hatsarin mummunar shiga da mata suke yi, sai ya sanya wasu mutane suke ganin kamar malamai ba su damu da ado da kwalliya da tsafta ba, kamar sun fi so mata su kasance cikin shiga marar tsari da ƙayatarwa, wasu ma gani suke yi kamar koyarwa musulunci ɗungurungum ba ta damu da kwalliya da ado da tsafta da tsari ba!.

    Domin karanta Waya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada Danna nan 

    Amma abin ba haka yake ba, malamai sun san muhammancin tsafta da ado ga musulmi baki ɗaya, maza da mata manya da yara, sai dai ganin yadda wasu mata Musulmi suke kwaikwayon.

    Turawan Yamma a fannin shiga marar tsari, kuma ko’ina ba tare da tsare dokakin Allah ba, shine ya sanya malaman suka fi yin bayani a kan abin da zai nesantar da Musulmi daga irin
    waɗancan miyagun halaye.

    Tabbas shari’ar musulunci tana la’akari da muhimmanci ado da ƙwatarwa a ɗabi’ar
    ɗan’Adam , domin haka ne Allah ba ni haramta wa bayinsa ado da kwalliya da kayan daɗi na
    halaliya ba.
    A gaskiya, da wuya a sami koyarwa da ta fi ta Musulunci nuna muhimmancin kwalliya da
    ƙawatarwa ba. Saboda har a cikin Alƙur’ani ayoyin da Allah yake bayanin buwayaSa cikin wasuhalittunSa domin ɗan’Adam ya gujjan ta samuwar Ubangiji, kuma ya kaɗaita shi, kana ya godewa ni’imarsa, dake cikin waɗancan halittu daban- daban, duk da haka sai mu ga Allah na nuna mana ɓangaren ado da ƙayatarwa dake cikin halittun nan nasa, misali:

    Yana dakyau ku karanta bayani akan Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2)

    (1) Halittar Sama:
    ● Allah Ta’ala Yana cewa: “Haƙiƙa mun ƙawatar da halittar sama ta duniya, da
    adon taurari”. (Suratul Annali :14)
    To, a nan za mu ga ashe taurari bayan sauran ayyuka da manufofin samar da su, kuma su
    zamo ado ne da ƙaye ga samaniya.
    (2) Halittar Ƙasa:
    Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma da abin da (Allah ) Ya halitta muku a cikin ƙasa (na
    abubuwa) masu launi iri-iri, haƙiƙa cikin wannan akwai abin lura ga mutane masu
    tunatuwa”.
    Wannan aya tana nusar da mu ya zuwa halittun Allah na ƙasa masu kyan gani da ban
    sha’awa, kamar su barewa da doki da jakin-dawa da raƙumin-dawa , a cikin dabbobi,
    kamar kuma ɗawisu da zabo da baini, a cikin tsuntsaye, kamar kuma
    malam-buɗa-mana-littafi da wutar-yola, a cikin ƙwari, da dai sauransu.

    Haka kuma a cikin halittun Ubangiji masu ƙaye dake cikin ƙasa, aƙwai furanni da
    huda da ganyaye masu launi mai armashi, da ban sha’awa, kuma wasu bayan launi da
    suke dashi har da ƙanshi mai tausasa zuciya, duka wannan baiwa ce ta Allah ga bayinsa.

    (3) Halittar Ruwa:
    Haka kuma Allah Ta’ala ya bayyana ni’imominsa ga ɗan’Adam waɗanda Ya sanya a
    tekuna da koguna dake bayan ƙasa, inda yake cewa:
    “kuma Allah shi ne wanda Ya hore muku kogi domin ku sami nama lafiyayye daga
    cikinsa, kuma ku fito da kayan ado wanda za ku dinga sanyawa”.(Sura Annahl, Aya ta
    14).
    A wannan ayar Allah Ya nuna muhimmancin dangin abinci mai gina jiki wanda ake
    samu a kogi kamar kifaye da sauran su. Amma saboda nuna muhimmancin kayan ado a
    Musulunci sai ga shi an yi ishara ya zuwa kayan ƙawa Allah ya halitta a ruwa, kamar su
    jauhari da mirjanai da gwala-gwalai da sauransu.

    Domin karanta Yadda ‘Yan Mata Ya Kamata Su Kula Da Jikinsu Daga Lokacin Balaga Danna nan

    (4) Tufafi (Suttura):
    Duk da yake babbar manufar tufafi ita ce suturta jiki, amma wata aya dake bayani a kan
    ni’imar sutura, sai da ta faɗi ɓangaren ado da kwalliya, a matsayin cikamakin baiwar da
    Allah Ya yi wa bayinsa ta hanyar hore musu tufafi. Allah Ta’ala Yana cewa:
    “Ya ku ‘yan Adam haƙiƙa mun saukar muku da tufafi masu rufe muku tsiraicinku, da
    gashi (don ado da kwalliya) da kuma tufafin tsoron Allah, wannan (Kuma) shi ne mafi
    alheri”. Al- A raf:( (24).
    (5) Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya:
    Wata aya ta tabbatar da cewa ado na Allah ne, don haka babu wanda zai haramta wa
    bayinsa kayan da ya fitar don amfaninsu. kuma shi ado da kayan daɗin duniya na halak,
    duk an fitar da su domin Musulmi su more su a duniya , haka kuma a lahira su kaɗai ne
    za su sha daɗin waɗannan ni’imomi. Ayar tana cewa:

    “Ka ce wane ne ya haramta kayan Ubangiji na ado da kayan daɗi na halal wanda ya
    fitar da su ne, don amfanin bayinsa, ka ce wannan (duk) na musulmi ne duniya, kuma a
    lahira su kaɗai ne za su more su”.Al-A’raf:32.
    A nan za mu ga cewa, Allah Ta’ala ya yi tsawa ga wanda ke ƙoƙari haramta wa
    musulmi more kayan ado da na halal, kuma ya jingina ado ya zuwa ga zatinsa saboda ya
    ce, (ado Ubangiji), sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa musulmi tun a duniya , ya halatta su more waɗannan ni’imomi, bugu da ƙari a lahira su kaɗai ne ma za su amfana da
    su.

    (6) Allah Ta’ala mai Kyau ne, kuma yana son abu mai kyau.
    Magana a kan matsayin ado da ƙaye a addinin Musulunci ba za ta cika ba, har sai an
    kawo Hadisin Manzo Allah (S. A.W) da ya ke cewa:
    “Haƙiƙa Allah (Ta’ala) mai kyau ne kuma yana son abu mai kyau”. (Hadisi ne
    ingantancce).

    Saboda haka duk abin da za a faɗa an yi ne don a hana su kyautata jikinsu da ƙawata
    kansu ba ne, sai dai a faɗakar da su a kan abin da zai iya zame masu illa idan sun saɓawa
    ladubban ado da kwalliyar tasu a Musulunci.

    Tabbas, a irin yadda kwalliyar mata ta zamani take, tana buƙatar mata Musulmi su yi
    mata gyare-gyare, akwai nau’o’i da yawa na kayan sawa da na kwalliya, waɗanɗa suna
    iya zama matsala gare su, a kan haka bai kamata garin kwalliya a jawo wa jiki illa ba, ko
    kuma a jawo wa aljihu ko jaka naƙasu ba! Ko Hausawa ma suna cewa: “kada garin
    gyaran gira a tsone ido”!

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin “Sutura Da Kwalliyar Mata” Domin karanta cikakken littafin ko daukoshi  Danna nan

  • Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki suka yi yawa a kasuwa; zaɓar abubuwan da za su taimaka wa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan kin san yanayin fatarki, sai ki zaɓi abubuwan da za ki yi wajen kula da fatarki a kullum.

    Ga misalan yadda za ki kula da fatarki:

    1. Goge Kwalliya Kafin Bacci

    Idan ya kasance an miki kwalliya mai yawa ta zamani, to yana da kyau ki samu abin da za ki goge ta tas, kafin ki kwanta barci. Koda wacce ta yi miki kwalliyar ta taya ki gogewa, amma idanuwa da laɓɓa suna buƙatar kula ta musamman, saboda haka; sai ki samu abin goge kwalliya (wiper) jiƙaƙƙiya, ki sake gogewa a hankali.

    2. Wanke Fuska

    Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin ki yi kwalliya, sai kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi, ba mai zafi ba; sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska, sannan a sake ɗaurayewa.

    3. Amfani Da Toner

    Bayan an wanke fuska, ana so a shafa toner. A samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan, sai ana shafawa a hankali ban da gurin ido sannan ba a wankewa.

    4. Amfani Da Moisturizer

    Bayan toner ta bushe a kan fuskarki, yana da kyau a yi amfani da moisturizer a kan fuska, hadda tafin hannu ma idan kin so. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido, sai ki samu wani mai na musamman.

    5. Yin Murza (Scrubbing)

    Ana iyayin murza ta, musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati, za ki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa, sai kina dangwala da hannunki, kina murzawa a hankali a kan fuskarki.Bayan wasu mintoci sai a wanke da ruwan ɗumi.

    6. Yin Amfani Da (Sunscreen)

    Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska, ko kuma nuna alamun girma. Yana da kyau duk lokacin da za ku fita rana, ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa a kan fatarku. Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau danna nan

  • Yadda Ake Haɗa Man Gashi

    Yadda Ake Haɗa Man Gashi

    Idan aka ce man gashi, ana nufin mai da muke amfani da shi wajen kula da gashin kanmu ko mace ko namiji.

    Mukan yi amfani da man gashi domin ƙayatar da shi wajen saka shi; laushi, ƙamshi, hana ƙuraje da ƙyasbi da kwarkwata samun guri a zama gashin, sannan kuma domin gashi ya ƙara tsayi da cika.

    Sinadaran Haɗin Su Ne:

    • Petroleum jelly wato Vasseline
    • Paffarin oil
    • Palm kennel oil wato baƙin man kwakwa
    • Candle Wax wato candir
    • Menthol
    • Colour wato kala
    • Sai turaren haɗin

    Amfanin Ko Wani Sinadarin Haɗin Man Gashin

    • Petroleum jelly shi ne kamar Vasseline amma ba shi da maiƙo
    • Paraffin oil shi yake saka haɗin maiƙo
    • Palm kennel shi yake ƙara tsawon gashi
    • Candle wax shi yake ba wa haɗin damar daskarewa bayan an gama
    • Menthol shi yake taimakawa wajen kashe dandruff (ƙyasbi) da saura ƙurajen kai
    • kala shi yake canja launin man
    • Sai turare shi yake saka man gashin ya yi ƙamshi

    Duka waɗannan sinadaran sanannu ne a kasuwa, sannan farashinsu na da arha gwargwadon adadin da ake buƙata. Wajen wannan haɗi, a tabbatar da bin ƙa’idoji domin samun sakamakon da ake da buƙata

    Kayan Amfani Wajen Haɗin Man Gashi

    • Gas cooker/Murhu/Risho
    • Tukunya madaidaiciya.
    • Babban cokali ko ludayi domin motsa haɗin man gashin.
    • Robobin man gashi da za a juye man bayan an kammala haɗin.

    Yanda Ake Haɗin Man Gashi

    • Da farko za a ɗauko tukunya a ɗora ta a kan risho ko gas cooker bayan an kunna,
    • Sai a juye petroleum jelly ɗin a cikin tukunyar, a dinga juyawa da cokali ko ludayi
    • Sannan a ɗauko candle wax a saka, shi ma a cikin tukunyar bayan petroleum jelly ya gama narkewa a ci gaba da juyawa da cokali, har ya narke gaba ɗaya.
    • Sai a ɗauko parrafin oil da palm kennel oil, a juye su tare a cikin tukunyar, a ci gaba da motsawa da cokali.
    • Daga nan, sai a kashe wutar, a sauke tukunyar,
    • ana sauke tukunyar sai a gaggauta zuba kala a cikin tukunyar haɗin, a motsa shi da kyau.
    • Bayan minti uku Sai a zuba turaren haɗin
    • Sannan a kawo Menthol ɗin shi ma a zuba a cikin haɗin, a ci gaba da motsawa.
    • Sannan a bar haɗin ya kai a kalla minti goma sannan a zuzzuba robobin man gashin.
    • Daga nan kuma sai a bar su a buɗe su sha iska, domin man ya daskare. Shi kenan man gashinmu ya kammala.

    Gargaɗi

    Wajen wannan haɗin a tabbatar da cewa an tanadi kayan haɗi da sinadaran haɗin da ya kamata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sabulun Wanka danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

  • Yadda Ake Ado Da Kwalliya Ta Musamman Ga Mata Da Maza

    Yadda Ake Ado Da Kwalliya Ta Musamman Ga Mata Da Maza

    Idan ka ji ance Gaye ya iya ɗaukar wanka. To ana nufin saurayi ya haɗu sosai. Wato dai ana nufin ya iya ado da kwalliya.

    Iya tsaftace ko’ina na jiki. Da ɗanɗasa ado da kwalliya ga maza da mata. Yana matuƙar tasiri na fizgar Zuciya .

    Akwai bambanci tsakanin ado da kwalliya na maza da mata. Za mu ɗan yi taƙaitaccen bayanin kowanne.

    Yanayin shiga yana nuna wa mutane yadda kake. Irin halaye da tarbiyyar mutum. Haka ma ana girmama mutum, saboda irin yadda ya mutunta kansa wajen sutura.

    Kai hatta a wajen aiki ko kasuwanci, ado da kwalliya na taimaka wa mutum sosai.

    A wajen ado da kwalliya ba a bayyana tsiraici. Al’aurar namiji ta fara daga cibiyarsa zuwa gwuiwoyinsa. Mace kuwa duk jikinta Al’aura ce,in ban da fuska da tafukanta.
    YADDA AKE ADO DA KWALLIYA NA MAZA :
    TSAFTA: Wanka, da aske gashin hammata, da asiwaki da kuma yanke farce(ƙumba). Na sawa ka haska.
    ƊINKI: Kaftan doguwa, da shakwara da jamfa, da ƙananan kaya na Turawa.
    HULA : Akwai huluna na dinki, Dara, Zanna, da dai Sauransu. Hula ta sha wanki ta ji sitati.
    ASKI: Yin aski, kar a bar suma ta dunƙule kamar bargo.
    AGOGO: Sanya agogo da zobe na azurfa. Kwalliya ce ta Maza. Haramun ne namiji ya sa zobe na Zinariya ( Gwal) .
    TAKALMI : Yana da muhimmanci a cika ado da kwalliyar mazaje.
    Kowacce Mace za ta iya zama tauraruwa, a dalilin iya ado da kwalliya. Idan na ce tauraruwa, Ina nufin kyakkyawar gaske wacce haskenta yake tasiri harma da janyo soyayya.

    Shi ne ta ɗauki adonta da kwalliya a matsayin ibada. Wato ta ɗauke su dole ne, kuma tana samun lada a ciki.

    Iya ɗaukar wanka, a tsaftace ko’ina na jiki. Da ƙawata jikin da kwalliya. Da yin ado na da matukar tasirin fizgar zuciya ɗan Adam.

    Haka ma dai yana ƙara wa mace daraja, ƙima, da mutunci.
    Kai ko budurwa ce sai ka ga ta zama mai farin jini sosai.

    Har mijinta yai ta yawan son ganinta. Ya dinga samun natsuwa. Yana zama a gidansa

    YADDA AKE ADO DA KWALLIYA NA MATA :
    1- TSAFTA: Zama mai tsaftace jiki da tsaftar sutura ne farko. Hausawa sun ce “in kana da kyau, ka ƙara da wanka.
    2- ƘUNSHI: Ƙunshi na fidda Mace tai kwarjini a cikin adonta. Jan ƙunshi na lallen gargajiya, da baƙin ƙunshi na zamani (na kanti) .
    3- GYARAN GASHI: Ya haɗa da wanke gashi, da turara gashi (steaming), da shafa mai, da kitso da dai Sauransu.
    4- FATAR JIKI : Amfani da Dilka, da kurkum, da ganyaye na sa fata tai kyawu sosai.
    5- KWALLIYAR FUSKA : Yin kwalliya da tozali ( kajal ), hoda, Jan baki, na canja ki kacokan daga babba zuwa yarinya. Haka ma nan take ya mai da ke tsaleliya.
    6 – KALA : Tantancewa da irin launikan da suka fi karɓar ki. Yana ba ki haske na musamman.
    7 – KALLABI : Iya canja ɗauri, ɗan kwali na da ban mamaki. Har sawa yake a biki da kallo. A zamanance akwai Goggoro, da yadika daban-daban na ɗauri.
    8 – ƊINKI : Yanayin yadda maɗinka ke zubo da basirarsu. Na taimakawa kwarai wajen fito da kyawun sutura. Dogayen riguna.
    SARKA : Sanya sarka, da ɗan kunne, da zobe da awarwaro su na fidda mace .
    KAMUN KAI : Kamun kai na bai wa Mace daraja da ƙima.
    A ƙarshe ado da kwalliya na da muhimmanci. Amma fa wani mafi muhimmanci shi ne murmushi. Ko da babu kwalliya, murmushi na sa a ga kyawun mutum. ɗandashi!  A ce ga murmushi ga ado da kwalliya.

    Amma fa mu yi hattara kar garin neman gira, a rasa ido.

    Ka da mu saɓa wa Shari’ar addinimu. Kuma ka da mu cutar da kanmu.

    Babu mutum mummuna sai ƙazami, wanda ba ya ado da kwalliya.

    Tsafta, ado da kwalliya na ƙara soyayya da kawo natsuwa a tsakanin ma’aurata.

    Ance Imam Alqama ya kan yi ado ya zauna a gida. Da aka tambaye shi, sai ya yi hujja da wannan ayar ta cikin suratu Baqara:228.

    Imam ya ce : ” Tun da ina so iyalaina su yi min ado, shi ya sa ni ma nake yin ado in zauna a cikinsu.
    Wato yadda ado da kwalliya ke da muhimmaci wajen Mace, haka yake ga Namiji. domin karin bayani danna kuren rubtun dan duba yadda ake Maraba da Mai gida

    Litattafai da aka duba