Ya kamata kafin mu je ko’ina mu fara bayyana shin su wane ne matasa wato matashiya ko matashi. Akwai ra’ayoyi daga masana daban-daban game da batun matashi ko matashiya, kuma an karkasa su kashi-kashi mun kawo su kamar haka:
Akwai matakin yarinta, wanda ya soma daga shekara uku zuwa goma sha biyu. Masana ilimin tarbiyya sun karkasa wadannan matakan shekaru zuwa shekara biyu zuwa biyar a matsayin lokacin fara girman yaro ko yarintar farko. Sai kuma shekara shida zuwa takwas a matsayin matsakaiciyar yarinta.
Sannan kuma akwai shekara tara zuwa goma sha daya a matsayin lokacin yarinta na ƙarshe.Yara ba sa gushewa a cikin matakin yarinta har sai lokacin da suka zama baligai ta hanyar sha’awar jinsi wanda yake faruwa daga shekara goma sha ɗaya ga da namiji ko shekara goma sha uku ga ‘ya mace.
Akwai shekarun yarinta wanda ya kama daga shekara bakwai zuwa goma sha biyu, lokacin da ake kula da mutum wajen yin ibada, musamman salla, kafin ya kai ga balaga.
Sannan akwai kuma ayyamul murahaƙa, wato wanda bai balaga ba amma yana dab da balaga a tasakanin shekara goma sha huɗu zuwa goma sha bakwai (ya danganta da yanayin jikin mutumin ko saurin balaga ko kuma rashin balaga da wuri).
Don haka ana ɗauka wannan ne lokacin da za a kira na tasawa (matasa). Ko kuma dab da balaga zuwa shekara ashirin da biyar. Ana iya ɗaukar su a matsayin matasa wato muhariƙ d Larabci, wato matashi kenan.
A addinance za mu iya ɗauka cewa, matasa su ne waɗanda suka balaga daga nan har zuwa shekara ashirin da biyar. Alwai kuma shekarar gwarzantaka wato lokacin da mutum ya kai shekara arba’in, sanda ya kai matsayin cikakken mutum.
A binciken da aka gudanar wanda aka sanya a kundin ƙidayar al’umma na duniya za mu ga cewa waɗanda suka faɗo cikin wannana ƙwarya da ake cewa matasa su suka fi yawa a cikin al’ummar duniya baki ɗaya. Bayan haka kuma, hukumomi da masana sun yi ta bayyana su wanene matasa, kuma daga shekara nawa zuwa nawa ne za a iya ce wa mutum matashi, kamar yadda za mu gani a nan gaba, irin fassarori ko ma’anoni da aka bayar na zama matashi ko matashiya.
Hukumar UNESCO ta bayyana matashi ko matshiya da cewa waɗanda shekarunsa suka tashi daga goma sha biyar zuwa ashirin da huɗu su ne matasa. A cikin ƙamus Oxford Dictionary, bugu na shida wanda aka buga a cikin shekara ta dubu biyu miladiyya (2000AD) kuwa, an bayyana matasa a matsayin lokacin yarinta zuwa girma.
A kundintsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999 kua, tsarin mulkin ya ce waɗanda suka kama daga shekara goma sha takwas zuwa talatin da biyar su ne matasa. Idan muka yi la’akari da waɗannan mabambantan bayanai za mu gane su wane ne matasa. Amma a ƙasar Hausa abin ba haka yake ba, domin akwai bambancin matashiya mace da matashi namiji wajen shekara, domin a ƙasar Hausaba za a taɓa kiran mace ‘yar shekara arba’in a matsayin matashiya ba, sai dai mu ce daga shekara goma sha biyar zuwa talatin za a iya kiran ta matashiya.
Masana halayyar dan Adam da rayuwarsa kuwa sun nuna cewa masu shekara tsakanin sha biyar zuwa arba’in, ko ka ce daga balaga zuwa shekara arba’in, su ne jinsi na matasa. A tsakanin waɗannan shekaru ne mutum yake kammala gina jikinsa da hankalinsa. Kuma a tsakanin waɗannan shekaru ne, kamar yadda masu sanin yanayin jikin ɗan Adam suka tabbatar cewa, jiki zai ta bunƙasa,a inda gaßobi kan ƙara tohuwa, kuma tunani na ƙara yawa har ya zuwa lokacin da ɗan Adam ya kai shekara ashirin da uku ko da biyar.
A wannan lokaci ne tsawo ko girman ƙasusuwan ya ƙare, sai dai wataƙila tsoka ta ci gaba da ƙaruwa ga wanda Allah ya sa yana motsa jiki da kuma yanayi da abincin da mutum yake ci. Idan mjka yi nazari za mu ga cewa, waɗannan su ne shekaru na yin tunani, na gina menene mutum zai yi a rayuwuwarsa. Su ne lokuta na neman ilimi, lokuta na sassaƙa burace-burace na zan yi kaza zan yi kaza, na zan haifar da kaza.
Lokaci ne da ake tunanin yin aure domin fara samun ‘ya’ya da makamantansu, lokaci ne na sha’awace-sha’awacen rayuwar duniya, domin a tsakanin waɗannan shekaru ne ake samun matasa suna sha’awar su zama masu kuɗi, suna sha’awar zama masu ilimi, suna sha’awara zama shugabanni da kuma sha’awar zama manyan ‘yan kasuwa.
Duk waɗannan tunane-tunane da sha’awace-sha’awace suna zuwa ne a cikin waɗannan shekaru. Lokaci ne na jin ƙarfin jiki da zafin kai da na zuciya saboda sannan ne ake jin ƙarfi da kuzari, sannan ne ake da lafiya isasshiya. Saboda haka wajibi ne mu fahimci cewa, waɗannan shekaru ne masu muhimmancia rayuwar kowace irin al’aumma, kuma idan aka yi watsida yi wa jinsi na wannan al’umma saiti, to, ba yadda za a sami al’umma ta gari.
Kamar yadda muka sani, matasa su ne ƙashi bayan ci gaban kowace al’ummaba tun yanzu batun lokacin rayuwar annabi mai tsira da amonci da sahabbansa. Haka nan a wannan lokaci da muke ciki su ɗin ne kan gaba a kowace sabga ta ci gaba da kuma bunƙasar rayuwar al’umma.
Misali mu dubi irin gudunmawar da matasa suka bayar kamar irin su Abdullahi ɗan Umaru da Abdullahi ɗan Abbas da Ammar ɗan Yasir da Zaidu ɗan Harisata da Sabit ɗan Ƙais da Hisham ɗan Urwa da Abdullahi ɗan Salim da Sa’ada ɗan Abi Waƙƙas da kuma Mua’ab ɗan Umair waɗanda aka yi yaƙi da su, kuma wasunsu har hadisai sukan rawaito. Kuma duk shekarunsu sun fara daga ashirin ne zuwa ashirin da biyar.
Mus’ab ɗan Umair ɗan masu kuɗi ne amma ba musulmi ne ba, ya yarda ya dawo musulunci ya haƙura da dukiyar gidansu ya amshi musulunci ya zo ya kasance tare da Annabi mai tsira da aminci.
Haka kuma akwai mata matasa a zamanin Annabi (S.A.W) waɗanda suka taimakawa addinin musulunci, irin su Nana A’isha ɗiyar sayyadina Abubakar wadda aka rawaito hadisai sama da dubu huɗu daga gare ta. Haka ma Nana Hafsa ‘yar Umar ɗan Khaɗɗab wadda ajiye Alƙur’ani a wajenta da Asma’u ‘yar Abubakar Saddiƙ da sauransu, duk sun ba da gudunmawa a addinin musulunci.
Sannan in muka dawo Nijeriya, Nana Asma’u ‘yar Shehu Usman Ɗanfodiyo ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin addinin musulunci don ta rubuta waƙoƙi masu yawan gaske da Hausa da Fillanci da kuma Larabci, sannan kuma ta fassara wasu waƙoƙin Shehu Usman Ɗanfodiyo, kuma ta koyar da mata a fannin addini da sana’o’i da zamantakewa.
Danna nan do karanta Waye Bahaushe
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Domin ƙarin bayani, tuntuɓi gidandabino@yahoo.com
Edita@rumasau-kallamu