Shin Ko Kishi Yana Hana Faɗar Gaskiyar Kishiya?

0
29

A’a, a musulunce kishi ba ya hana faɗar abin da aka sani a gaskiyar abokin kishi. Domin kuwa Imamu Muslim Allah ya rahamshe shi ya rawaici hadisi da aka karɓo shi daga Muhammad ɗan Abdurrahman cewa, haƙiƙa Aisha (Radiyallahu An ha) ta ce: 

“ … Zainab ‘yar Jahsh ta kasance tana gasa da kuma kunnen doki da ni wajen matsayi gurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Ni kuwa) tun da nake ban taɓa ganin macen da ta fi Zainab ba; wajen addini da tsoron Allah da gaskiya ba a magana, da sadar da zumunta, da yawan sadaka da mayar da kanta ba kowa ba wajen yin aikin kusantar Allah, sai dai fa tana da saurin fushi lokaci lokaci”. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Saboda haka, adalci shi ne, kishiya ta faɗi gaskiya a duk lokacin da ta so yin Magana a game da kishiyarta. Sannan kuma ɓata kishiya da kushe ta don kawai tana kishiya, ba daidai ba ne, domin kuwa yin hakan ba riba ba ce, faɗuwa ce. 

Domin kuwa Imamu Muslim ya rawaito hadisi da aka karbo shi daga Abu Huraira (Radiyallahu An hu) ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah tabbata a gare shi ya ce: “…. Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne (don haka) ba a cutar da shi, kuma baya kwaye masa baya, kuma baya ƙarya ta shi, sannan kuma ba ya wulaƙanta shi….” 

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

Kuma duk Musulmi dangane da ɗan’uwansa Musulmi, haramun ne zubar da jininsa, haka taɓa masa kuɗi, (ba da haƙƙi ba), haka kuma zubar masa da mutunci” 

Sai dai kuma kash! Abin takaici a wannan zamani namu na yanzu, wasu kishiyoyin ba su da wanda suke kare wa zagi ta uwa ta uba, sai kishiyoyinsu, wasu ma har lakuce hanci, kai wasu ma idan suka samu sake har da dukan kishiya da muciya, ko makamantan saboda kawai ƙin jini da ƙazamar gaba.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMenene Maganin Ƙazamin Kishi ( Haramtacce)
Labarin na GabaDuhun Kan Mace Mai Gaba Da Kishiya