Littafin Ina Son Sa Haka
Littafin Ina Son Sa Haka wanda Balaraba Ramat Yakubu ta wallafa a shekarar ta 1999, yana ba da labarin wata yarinya ce Fatima wadda aka yi wa auren dole, kuma ta aminta ta zauna saboda biyayyar iyaye. Saboda haka za a iya cewa Fatima ita ce gwarzuwar littafin, domin kuwa ita ce aka yi wa auren dole ga wani Shehu wanda ba ta so.
Ita dai Fatima kamar yadda marubuciyar ta ruwaito babanta mutumin Fage ne cikin birnin Kano, yayin da mahaifiyarta mutumiyar Yamai ce, a jamhuriyar Nijar. Ta yi karatun sakandare, bayan ta gama aka maida ta wurin kakarta, wadda ta haifi mahaifinta sakamakon rasuwar mahaifiyarta.
Shi kuma Shehu wanda ya auri Fatima ba tare da tana son sa ba ya girma a Kano ne, amma ya yi karatunsa a Jami`ar Oxford da ke Ingila, bayan ya dawo daga karatunsa suka haɗu da Fatima, amma kafin nan ya haɗu da mata iri-iri, amma duk ya watsar sai Fatima da suka haɗu ya ga yana so, ita kuma ta ƙi shi.
Duk da wannan ƙi da Fatima ta yi wa Shehu, wannan bai hana ta auren shi ba, domin dama an matsa mata kan maganar aure, wanda gamuwa da Shehu da hikimomi na iyayensa suka sanya aka ɗaura auren Fatima da Shehu.
Bayan auren, Shehu ya yi ta fama da Fatima domin ta yarda da shi, amma ƙiri da muzu ta ƙi shi, wannnan ne ma ya sa shi ya haƙa mata tarko ya kai ta kulob inda ya yi ƙoƙarin shayar da ita kayan maye, maimakon wannan ya ɗan jayo hankalin Fatima ga Shehu, sai abu ya ta`azzara, inda ta yi yaji, ta koma gidan kakarta.
Da lallashi da ban haƙuri daga wurin kakarta, kwatsam sai ga kira daga babanta domin Shehu ya je ya kwashe abin da ya faru na cewa ta fita daga gidansa. Nan babanta, Alhaji Haruna ya fatattake ta, ta koma gida, shi kuma Shehu a gida ya ci gaba da lallashin Fatima, duk dai don ta yarda da shi.
A haka dai rayuwar aure ta ci gaba da gudana a gidan Shehu, inda har Fatima ta haifar masa `ya`ya huɗu, daga nan kuma shi ya sakankance da cewar ya mallake zuciyar Fatima, amma fa ga wautarsa.
A cikin irin wannan yanayin ne wata rana suka yi faɗa sosai, har ta kai ga har Shehu ya saki Fatima, ta koma gidan kakarta, amma babanta na samun labarin sakin ya je har gidan kakar ya nemi maida Fatima gidan mijinta, amma suna zuwa Shehu ya ce ba zai karɓe ta ba, domin shi ya gaji da irin abin da Fatima ke yi masa.
Zaman da ake yi na jiran Shehu ya maida Fatima, shi ya ba ta damar tafiyarta wurin wata ƙawarta mai suna Saratu ta zauna, daga baya Saratu ta kai Fatima wurin wata ƙawarta a Sabon Gari, wato Zulai wadda take karuwanci. A lokacin Zulai ta gayyaci Fatima da su tafi Obalande, a Legas, kuma Fatima da ta yi niyyar bin ta, amma sai ta tuna da `ya`yanta da ke wurin kakarta, wanda wannan shi ya hana ta yin wannan tafiyar.
Fatima ta koma gidan kakarta, kuma mahaifinta na samun labarin dawowarta, ya je ya yi ta yi mata faɗa, kuma ya tursasa cewa lallai sai ta tashi su tafi ya maida ta ɗakinta, kakar ce ma take lallashin shi, ya haƙura sai da marece, shi kuma ya matsa, nan ne ma kakar ke nuna masa cewa kamata fa ya yi a lallashi Fatima, ba wai a tilasta mata ba.
Fatima ta koma gidan Shehu, inda har ta samu wani cikin. Wata rana Fatima na barci, sai ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya yi ta ciwo, ita kuma saboda wahalar da cikinta yake ba ta tana bacci, sai ga Shehu ya dawo, ya isake yaro na ta kuka, ita kuma mahaifyarsu na ta barci, wannan ya baƙanta masa rai, ya je ba tare da ya ba ta wani hurumi ba ya hau ta da duka, ya ba ta kashi sosai har sai da ya gwama ta da da kujera, wannan ya sa cikinta ya bugu, sai jini ya yi ta kwarara, shi kuma ya sa ƙafa ya fice daga gidan.
Kamar haɗin baki, sai ga Gwaggo, mahaifiyar Shehu, nan suka ɗauki Fatima sai asibiti, likita ya duba ta ya ce ta yi ɓari, kuma ma mahaifarta ta taɓu sosai ta yadda da wahala ta sake haihuwa. Duk da cewa Shehu ya yi ta zuwa asibiti ganin Fatima, amma Gwaggo ta ƙeƙasa ƙasa ta ce sai dai a raba auren Shehu da Fatima, shi kuma mahaifin Fatima ya ce abadan, ba a raba wannan auren, sai yake ma ganin cewa ai laifin Fatima ne, ita ce ba ta son zaman aure, ita kuma Fatima sai take nuna cewa babanta ba ya tsayawa ya binciki abin da ya faru in rigima ta haɗa su da mijinta, sai kawai ya ce ita ke ba ta da gaskiya.
Baban dai ya kasa cewa komi game da wannnan, sai dai kawai daga ƙarshe ya ce in dai har ta sake ta bar gidan Shehu, to sai dai ta nemi inda za ta zauna amma ba a gidansa ba. A nan wurin Fatima ta shiga tsaka-mai-wuya, domin mijinta ya ƙi ta, an zo gida wurin mahaifinta, shi ma ya fatattake ta. Ba arziƙi Fatima ta tuno da gidan su ƙawarta Saratu, nan take ta ce wa `Yansandan nan da su kai ta gidan, suna zuwa kuwa aka buɗe mata ƙofa, bayan `Yansandan sun yi masu bayani, a nan Fatima ta ƙarasa daren wannan rana.
Gari na wayewa mahaifin Fatima ya zarce gidan Gwaggo, domin ya san ba makawa can Fatima ta dosa, amma yana zuwa don ya kore ta, sai ya iske ba ta nan, ita kuma Gwaggo ta hau shi da faɗa da ta fahimci cewa Fatima ta gudu, daga ƙarshe ma ta kore shi daga gidan, ta ce ba ta, ba shi har abada, tun da ya kori Fatima.
Ita kuma Fatima daga ƙarshe ta yanke shawarar ta bar garin gaba ɗaya, domin ta huta, Saratu ta ba ta shawarar ta tafi Legas wurin Zulai (tun da dama ta taɓa yi mata tayin zuwa can ɗin), a nan Saratu ta ba ta wasu kayan da za ta yi amfani da su, kuma ta ranta mata kuɗin jirgin da za ta tafi Legas ɗin.
A lokacin da Saratu ta raka Fatima filin jirgi don tafiya Lagos, sai suka ga wani Alhaji, iyalinsa sun rako shi zai yi tafiya, Saratu ta ce wa Fatima za ta je su gaisa da shi, domin ta san shi a ma`aikatar da ta yi wa ƙasa hidima, bayan ta dawo ne Fatima ke tambayar ta waɗanda suke tare da shi, ta ce mata iyalansa ne suka rako za shi kwas na shekara huɗu a ƙasar Sin, amma ta Legas zai bi.
Bayan tafiyar iyalan Alhaji Sadiq ne ya kira Saratu, inda ya yi mata tambayoyi kan wadda suke tare da ita, wato Fatima, da kuma inda za ta, ita kuma ta ce masa za ta Obalande wajen `yar uwarta, daga baya ya ce mata ta kira Fatima. A nan dai Alhaji ya nuna ra`ayinsa kan Fatima, ya nemi kuma ya biya mata kuɗin jirgi tare da raka ta har Obalande ɗin, don dai shi ya nuna damuwarsa na yadda za ta tafi Legas ita kaɗai, ga ta ba ta san wurin ba, ta dai amince. Kan ka ce me, soyayya ta shiga tsakaninsu.
A Legas, masoyan biyu sun kwana a ɗaki guda, kuma duk da cewar ba abin da ya shiga tsakaninsu, amma sun shafe dare suna ba junansu labarinsu, a nan ta bayyana cewa Alhaji Sadiq ba ya jin daɗin matansa, domin suna gallaza masa. Daga ƙarshe dai Sadiq ya nemi da idan Fatima za ta iya jiransa nan da shekara huɗu in ya dawo daga birnin Sin, sai su yi aure, ta yarda.
Bayan tafiyar Alhaji Sadiq, Zulai ta shigar da Fatima karuwanci gadan-gadan, an dai karantar da Fatima harkar karuwanci kafin ta waye, ta fara haɗuwa da Chukumeka, kafin ta koma wa wani Ibon, Ugochukwu wanda shahararren ɗan fashi ne.
Ugo, kamar yadda marubuciyar wannan littafin take kiran sa, yana matuƙar son Fatima, daga bisani ma har gida ya gina musu ita da Zulai a Surelere, kuma sun daɗe suna harka tare. A irin haka ne Fatima da Saratu suka yi shawarar cewa su kwashe kayan ƙarau ɗinsu da wasu kayansu, ta yadda ko da an kama wannan gagararren ɓarawon, a ƙalla su tsira da wani abu.
Kamar suna duba kuwa! Wata rana sai ga Ugo ya shigo gidansu afujajjan, inda ya shaida masu cewa sun yi wa jakadan Ingila da ke nan Nijeriya fashi, kuma sun samo kuɗi, saboda haka shi da muƙarrabansa za su bar garin sai ƙura ta lafa, nan dai ya ba Fatima kuɗi kimanin naira miliyan biyu, kuma ya amince mata ta ci gaba da harkarta har sai ya dawo.
Zulai ma bai bar ta haka nan ba. Ashe rabuwar ƙarshe ce da Ugo, domin ba a daɗe ba aka kama shi dangane da wannan satar, aka kuma kashe shi. Su kuma su Fatima suka gudu daga gidan, don tsoron kar tsautsai ya sa a kawo farmaki a gidan, suka koma wurin wani maigadi kusa da gidan, sannan suka sa shi a hankali ya kwaso masu kayayyakin da ke gidan nasu, daga baya Ibrahim, saurayin Zulai ya mai da su gidansa.
A lokacin wannan gudun hijra ne Sadiq ya dawo daga China, ya kuma nemi Fatima kamar yadda suka alƙawarta wa juna, amma ba ta. Bayan ya sha wahalar nema da taimakon maigadin da su Fatima suka zauna gidansa, Sadiq ya gano Fatima, tare da jaddada mata soyayyarsa, ita kuma ta rinƙa kwatanta masa abin da ta aikata lokacin da ba ya nan, a haka dai ya natse da son ta, soyayya ta dawo sabuwa!
Kuma Fatima ta nemi da in dai da gaske ne yana sonta, to ya aure ta don ya raba ta da karuwancin da take yi, ya yarda, Zulai ma ta nemi Ibrahim da ya aure ta, shi ma ya yarda, kuma take suka yanke shawarar cewa su Fatima su koma gidan Gwaggo, don su yi idda.
Fatima ta sake komawa Fagge ta Kano shekara huɗu da wata takwas da kwana bakwai bayan barin gida, kan ka ce me, duk unguwar aka samu labarin dawowarta, `yan uwa da abokan arziki aka yi ta zuwa murna, ciki kuwa har da babanta, ya kuma yafe mata. Kwatsam! sai ga tsohon mijin Fatima a guje, ya nemi ta koma gidansa, ta ƙi, ya yi lallashin duniya, ta ƙi, daga ƙarshe dai ya haƙura, amma kuma ya zama mashayi na sosai, wanda shan ya yi ajalinsa.
Bayan auren Fatima da Sadiq, sai matsalar kishiyoyi ta addabi gidan Sadiq, wanda wannan har ta ja a wani faɗa da aka yi a gidan, Sadiq ya biyo Fatima yana ba ta haƙuri ya zame daga matattakalar bene ya kuma ji ciwo sosai, wanda aka yi ta faman magani amma abu ya yi ƙamari, har dai sai daga ƙarshe aka kai shi asibitin Ibadan, suka ce za su iya yi masa aiki, amma kafin nan duk matan Sadiq sai da suka guje shi, sai Fatima kaɗai ta tsaya kai-da-fata kan lafiyarsa, ta kuma bayar da zunzurutun kuɗin da aka nema don yi masa magani.
Dangin Fatima sun damu da yadda ita kaɗai ta tsaya tana jinyar Sadiq, amma ita ta nuna masu cewa ita fa tana Son Sa Haka, kuma daga nan ne ma sunan littafin ya samo asali, wato tana son sa a yadda yake. Daga bisani dai Sadiq ya warware, bayan dawowarsa gida ya saki sauran matan, suka zauna shi da Fatima, rayuwa ta zame masu sabuwa, Fatima ta shiga harkar safarar motoci daga cikin ɗimbin kuɗin da ke gare ta, wanda ta samo daga wurin Ugo, ta gina masallatai da makarantun Islamiyya da taimaka wa gajiyayyu.
Jigo a Littafin Ina Son Sa Haka
Kai tsaye za a iya cewa jigon wannan littafin rayuwar aure ce da take magana kan auren dole, domin kamar yadda wasu masana suka nuna, (Adamu, 2001), littafin yana da kama da littafin Balabara na Wa Zai Auri Jahila? Saboda dukkansu dai suna yin magana ne kan auren dole.
A cikin littafin an nuna illar da auren dole ke da shi ga al`ummar Hausawa, ta yadda yake jefa da dama daga cikin waɗanda aka yi wa irin wannan aure cikin karuwanci. Akwai wurare da dama a cikin littafin da za su nuna mana cewa auren dole shi ne jigon wannan littafin, alal misali inda Fatima ke cewa:
‘Kai dai mijina ne, amma ba masoyina ba. Ai mutum ba ya yin soyayya shi kaɗai’ (sh:21)
An ce ido ba mudu ba ne…, ai daga jin wannan an san cewa don dole ne ake zaune da mutum, amma ba don ana son sa ba. Haka kuma mu dubi inda take cewa:
‘Ka saurare ni da kyau ka ji, don shegen nacin tsiya ka ƙi rabuwa da ni, don Babana yana sonka, ni har abada ba zanƙaunace ka ba’. (sh:35).
Babu shakka nan ma an yi amfani da kalamai masu zafi don nuna cewa ba ana zaune da mijin don soyayya da ke tsakani ba ne, ana dai zaune ne kurum don an tilasta a zauna ɗin. Haka kuma za mu ga inda wannan batu na auren dole ya fito a fili, wato lokacin da Fatima ta yi yaji ta je gidan Gwaggo, a inda Gwaggo ke lallashinta ta koma gidanta, ga abin da Gwaggon ke cewa ;
‘Ki yi haƙuri, Fatima. Ba a kanki aka fara auren dole ba. In Allah Ya so, za ki haƙura da shi. Bari dai ki fara haihuwa’ (sh:31). Haka kuma jigon littafin dai yaƙara fitowa fili a lokacin da Shehu ke lallasashin matarsa, ita kuma ta fitoƙiri-ƙiri ta nuna ba ta son shi, ga abin da take cewa ; ‘In mijina ne kai sai me, ni na ce ba na son ka Shehu, ba naƙaunar ka, koko dole ne soyayyar?’
Saboda haka babban jigon wannan littafin shi ne auren dole, idan aka lura da kyau, iyayen yara kan yi wa `ya`yansu aure ga wani wanda suke so ba zaɓin yaran ba, wato iyaye na yin amfani da damar da ke gare su kan `ya`yansu, su zartar da cewa ga wanda suke son su aura, ko da su `ya`yan ba su son shi, musamman `ya`ya mata, duk da cewar maza ma akan samu hakan, amma ya fi yawa ga mata.
Wannan littafi na Ina Son Sa Haka bisa wannan turbar aka samar da shi. Kamar yadda muka gani a ciki, mahaifin Fatima ya zaɓar mata wanda za ta aura, duk da cewar ba ta son shi, ta aure shin, saboda neman albarkar iyaye, amma zama bai yi daɗi ba.
Salo a Littafin Ina Son Sa Haka
Salon littafin Ina Son Sa Haka mai aramashi ne, an yi amfani da hikima da basirar sarrafa harshe wurin gina labarin. Haka ma kalmomin da aka yi amfani da su duk sun dace, saboda akwai nuna gwaninta wurin amfani da su. Sannan kuma ba a yi amfani da wasu kalmomin masu sarƙaƙiya ba, kawai dai a iya cewa an buɗe labarin ne cikin gwaninta ta iya tsara littafi, domin mawallafiyar ta fara ne kai tsaye da nuna cewar gwarzuwar littafin tamkar ta tuna baya ne, ko kuma ana tariyar abin da ya faru.
Domin kuwa an nuna Fatima ta zo gidansu ne don su gaisa, sai suka haɗu da wani ɗan uwansu wanda sun kwan biyu ba su haɗu ba, inda shi kuma mahaifinta ya fara da cewa ta liƙe wa wani mijinta ne wanda ba shi da lafiya, kuma ma duk matansa sun guje shi, sai ita kaɗai ta tsaya tana wahala da shi, ga abin da yake cewa;
‘Matansa uku, duk sun fita, sun bar ta da shi. `Ya`ya goma sha uku suka zube mata, sai ka ce `yar aiki. Kai da yake baƙo ne, ka yi mata magana’. (sh:3).
Kusan daga nan za a iya cewa an buɗe wannan labarin, wanda shi kan shi wani salo ne na bayar da labari da mawallafiyar ta yi amfani da shi, wato na kwan-gaba-ƙwan-baya. Baya ga wannan, mawallafiyar ta yi amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta, ta yadda kowa ya karanta littafin zai iya fahimtar komai a ciki. Yadda marubuciyar ta yi amfani da kalmomin, sun tabbatar daƙudurinta na isar da saƙonta.
Haka nan jimlolin da marubuciyar ta yi amfani da su na kai-tsaye ne, domin cikin jimla ɗaya mutum na iya gane inda ta sa gaba, kuma saƙon bai shige duhu ga mai karatu ba.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Danna nan ka karanta Sharhin Wasu Littattafan Adabin Kasuwar Kano
Edita@rumasau-kallamu