Samuwar Rubutun Ajami

0
91

Bincike ya nuna cewa an fi samun rubuce-rubucen Ajami na zube a cikin hanyar rubutu Magaribi, wato ba a faye samun rubutun Ajami da yawa a cikin rubutu na sharƙiyya ba. Haka kuma bincike ya nuna cewa, an fi shekaru ɗari biyu (200) ana amfani da Ajami a ƙasar Hausa kafin shigowar rubutun boko wanda sai kuma ya faru ne a dalilin zuwan Turawa ƙasar Hausa.

Dalilin cewa rubutun Ajami ya shekara 200 kafin na boko shi ne idan mutum ya yi la’akari da irin rubuce-rubucen da aka samu tun wajen ƙarni na 17 irin rubuce-rubucen Malam Abdullahi suka Kano da Wali Ɗanmasani a cikin Birnin Katsina da Malam Muhammadu na Birnin Gwari da dai sauransu.

Amma dangane da ilimin Arabiya da samuwar Musulunci wannan tun wajen ƙarni na 9 ne, domin akwai alaƙa tsakanin ƙasashen Hausa da na Larabawa tun a wannan ƙarni inda a Jami’ar Al-azhar akwai wani sashen da ake kira Ruwaq- Al-Barno, inda mutanen Borno suke zama a cikin Jami’ar. Yahaya (1988)

Har kwanan gobe Malaman zaure na ƙasar Hausa idan za su yi rubutu na zube a cikin rubutun Ajami suke ƙaddamar da shi. Haka kuma akwai jaridu da akan buga a cikin ajami kamar su Albishir da Alfijir. Haka kuma ba wai kawai a Hausa ba hatta a ƙasashen Afirka ta Gabas kamar su Tanzaniya da Uganda da Afirka ta kudu suna rubuta harshen Ki-swahili da Ajami.

Amma a ƙasar Hausa Ajami bai sami cikakken gata ba sai a 1985 a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato ƙarƙashin shugabancin Shugaban Jami’ar na wannan lokaci, wato Farfesa Mahdi Adamu Ngaski inda ya sa aka kira taro na ƙasa domin kyautata rubutun Ajami inda aka kira manyan malamai daga ko ina a ƙasar Hausa, taro ya fara zama ranar 28 ga watan Janairu na 1985 inda aka yi kwana uku sai kuma a cikin 19 ga watan Agusta inda aka sake kiran taron aka yi kwana uku aka tattauna akan abubuwa kamar haka:

a)A samar wa Ajami tsayayyiyar ƙa’idar rubutu
b)A kyautata rubutun Ajami domin a sauƙaƙa wa mai karatu yadda zai ji daɗin karanta shi.

Ka san an ce “Ajami gagara mai shi”, da aka kirawo taro, daga ƙarshe an samar da nagartacciyar hanyar rubuta Ajami, karɓaɓɓiya wadda wata hukuma ce ta gwamnati ta yi wannan hoɓɓasa . Kafin wannan lokaci masana sun kasafta hanyar rubuta Ajami zuwa gida uku:-

1700-1950

1950-1985

1985/88 zuwa yau

Daga 1700 inda aka sami rubuce-rubuce irin na su Wali Ɗanmasani babu wata ƙa’idar rubuta Ajami kowa yana rubutawa yadda yake so, sai a 1950 inda Alhaji Halliru Binji da Alhaji Na’ibi Sulaiman Wali suka rubuta wani littafi mai suna Mu Koyi Ajami Da Larabci (1950). Shi kuwa wannan yunƙuri ba na gwamnati ba ne, illa dai mutane kawai wanda ya karanta shi ke nan.

To sai a 1985 inda Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo aka kira masana suka gabatar da shawarwari a kan ƙa’idar rubutun Ajami to amma rahoton binciken da masanan suka yi bai fito ba sai a 1988, wato bayan shekara uku, mai suna “Report On Hausa Ajami Writing” (1988). Shi wannan littafi a kan Ajami ya ƙunshi babi (13) amma babu 2-10 su ne suka ƙunshi zallar yadda ƙa’idar rubuta Ajami take.

Idan aka ce rubutun zube ana nufin rubutun da ba waƙa ba, ba kuma wasan kwaikwayo ba. Zube ana nufin tsagwaron rubutu kai tsaye wanda aka yi shi cikin shafi ko shafuka da sakin layi daban-daban, a rubuce ko a maganance, wato ta hanyar magana.

Rubutun zube na Hausa ya samo asali ne ta hanyoyi guda biyu. Hanya ta farko ita ce ta hanyar addini wato rubutun zube ta hanyar Ajami wato hanyar rubuta Hausa cikin haruffa na Larabci. Wannan hanya Hausawa ne suka ƙirƙiro abarsu tun asali ta hanyar rubuta sunaye na gargajiya a jikin fahami kamar misali; Malam Ɗantsoho, Malam Ɗantsamiya, da kuma ire-iren sunayen da akan haɗa laƙunƙuna da su kamar gaɓar kara, ɓawon yawa, da dai sauransu to ta irin wannan hanya kuma manya-manyan malamai da manyan sarakuna sukan rubuta wasiƙu a tsakaninsu. Mukhtar (2004)

Samuwar Rubutun Boko

Kafin a fara rubutu da Hausar boko a ƙasar Hausa, sai da aka daɗe ana amfani da ita a ƙasashen Turai. Amma mutumin da ake jin ya fara amfani da ita shi ne wani Baturen ƙasar Jamus mai suna James Frederick Schon wanda ya zo ƙasar Saliyo aikin Mishan a 1840. Schon shi ya yi tunani ya kuma ƙirƙiro cewa ya kamata ya yi amfani da haruffan Latiniyya ya rubuta lafazin Hausa:-

“na riya waɗannan ƙa’idojin rubutu a raina ne, bayan na yi shakaru inda lura da abubuwa. Saboda haka na yi amanna da dacewarsu.” (Schon, 1862:X).

Bayan da Schon ya yi niyyar amfani da haruffan Latiniyya ya rubuta Hausa, sai wani Bature mai suna Lepsius, ya ba shi shawarwari a kan yadda zai kyautata rubutun. Sauran Turawa waɗanda suka biyo irin wannan hanyar rubutu ta J.F. Schon sun haɗa har da Prietzer (1904), sai Mischlich a (1906) sannan Westermann a shekara ta (1911) da sauran waɗanda suka biyo baya.

Wata hanyar rubutun zube cikin boko da aka fito da ita, ita ce wadda Robinson (1896) ya fito da ita, ko da yake Robinson shi ma Latinanci ya yi amfani da shi, sai dai shi ya ɗauki tsarin Ajami ne wajen sarrafu baƙaƙen da babu su a wasu harsuna. Misali v da q da x da sauransu a hanyar rubutu ta Robinson waɗannan haruffan ɗigo ake musu a ƙasa irin na Ajami maimakon lanƙwasa. Wato sai a rubuta su kamar haka:- b k d ba tare da lanƙwasa ba.

A lokaci na farko da hukuma ta tsoma baki a kan rubutun zube shi ne lokacin mulkin mallaka a nan Nijeriya inda Hanns Vischer wanda ake kira Ɗan Hausa ya tsara ƙa’idojin yadda za a yi amfani da Hausar boko a (1910) sai dai shi ma ya yi amfani ne da Hanyar Robinson inda yake sa ɗigo a ƙarƙashin harafi mai alhamza.

Wata hanyar rubutun zube kuma ita ce wadda Bargery (1934) ya yi amfani da ita; shi kuma waƙafi ya dinga sa wa hamzatattun haruffa maimakon ɗigo. Kamar haka:-

‘b k’ ‘d da kuma dai sauransu.

Hukumar Fassara ta Jihar Arewa ita ce ta fara ba da shawara a (1938) cewa ya kamata duk hamzatattun baƙaƙe a dinga lanƙwasa su maimakon ɗigo ko waƙafi.

Litattafan Ƙagaggun labarai da marubuta ke rubutawa sun kasu gida hudu:

1.) Akwai masu gajeren zango wato (fiction) wadanda ba sa wuce shafuka arba’in (40) zuwa shafi 200 da kuma,

2.) Masu dogon zango, wato (novels) masu shafuka 200 zuwa sama.

3.) Akwai Litattafan Kagaggun labarai da aka yi su, domin Hausawa a cikin akwai garuruwan Hausawa da tattalin arziki irin na Hausawa tunani irin na Hausawa. Sai kuma

4.) Litattafan Kagaggun labarai da aka rubuta su da Hausa, kawai domin a gabatar da saƙon da Hausa a matsayin harshen sadarwa amma labaran ba domin Hausawa aka gina su ba.

Irin waɗannnan ba na gyaran hali ba ne, shi ya sa akan samu batsa a ciki, sannan Hausar ba ta inganta ba. Don haka waɗanda aka gina labaran don Hausawa akwai ilmantarwa, nishaɗantarwa da gyaran halin al’umma. Saboda haka Wannan tana da muhimmanci domin tunatar da malamai, iyaye da marubuta wajen fahimtar yadda ƙagaggun labarai ke tasiri wajen gina tarbiyyar matasa. Haka kuma za ta ƙarfafa wa matasa gwiwa domin su karanta littattafai masu ɗauke da darussa da koyarwar tarbiyya a cikinsu.

Masana da dama sun tattauna a kan irin rawar da adabi yake takawa wajen gyaran halin Bil adama. Misali, Abubakar Imam cikin littafinsa Magana Jari Ce ya yi amfani da ƙananan labarai wajen koyar da gaskiya, haƙuri da adalci. Haka kuma Hafsat Abdulwaheed cikin So Aljannar Duniya ta nuna illolin soyayya marar tushe da muhimmancin kyawawan halaye a tsakanin matasa.

Waɗannan misalan sun nuna cewa ƙagaggun labarai ba wai nishaɗi kawai suke sa wa ba, har ma suna zama kayan gyaran hali da watsar da munanan ɗabi’u da ba nagari ba a cikin al’umma. Saboda haka dai a wannan takarda an yi amfani da hanyar binciken ɗakin karatu (Library Research Method), inda aka tattara bayanai daga littattafan Hausa, mujallu da wallafe-wallafen ca suka shafi adabin Hausa da yake magana a kan tarbiyya.

Wanann bayanin an ciro shi ne daga muƙalar da aka gabatar a taron makon Hausa wanda ya gabata a Ranar 24 ga wata Oktoba 2025 a Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Bichi.

Danna nan don karanta Amfanin Ilimin Kwamfuta

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWaiwaye A Kan Al’adun Gargajiya
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Bakwai
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.