Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa

0
25

Kamar yadda tarihi ya hakaito cewa roƙo na daga cikin muhimmin abu a wurin Bahaushe; wannan ya sanya har ake samun maroƙa a ƙasar Hausa; kuma da wannan sana’a ta roƙo suke yin dukkanin wata ɗawainiya ta rayuwarsu.

Mawaƙa sun fi kusa da maroƙa, domin wasun su ma sukan yi roƙo ne ta hanyar waƙa. Kamilu ɗaya ne daga cikin mawaƙan Situdiyo wanda yake waƙar siyasa; wanda a mafi yawan waƙoƙinsa za a riski salo daban-daban na roƙo.

Cikin wuraren da aka sami wannan roƙo a waƙoƙin da aka nazarta akwai:

1. Waƙar Hon. Alhaji Baba Bukar Mashina

Gindin waƙa : Baba na Mashina kowa ya bi.
Jagora : Baba na Mashina nai waƙa baba kaƙara mini ƙarfi na ba,
Babu gida kuma ba ni da mota ban je Saudiya na dawo ba,
Masu gida na haya sun tashen ban miƙa musu ‘yan kuɗi ba,
Baba na Mashina ya ci ka duba ni ma ga ni gwanin talakawa.

Idan aka lura a wannan baiti, za a ga Makaɗi Kamilu ya fito da gayar roƙo ta sigar bayyana wa wanda yake yi wa waƙa wasu matsaloli nasa. Wato ya nemi a ƙara masa ƙarfi, wato a ba shi kuɗi ko dai wani abu mai daraja. Sannan ya bayyana ba shi da gida da mota, kuma bai je Saudiya ba (aikin Hajji ko Umara), wanda hakan na nufin a ba shi gida da mota sannan a kai shi Saudiya. Sannan ya bayyana cewa masu gidan haya sun tashe shi, saboda ya kasa biyan kuɗin haya. A nan, idan an saya masa gida, shi ne abin da ya roƙa a farko, amma idan haka ba ta samu ba, to sai a biya masa kuɗin haya na tsawon wasu lokuta.

2. Waƙar Alhaji (DR.) Ibrahim Geidam ta Ruwa Baba

Gindin Waƙa : Ruwa Baba, Sannu Baba Gwamna Bra-Bra.
Jagora : Ahmad Lawan ka duba mini ya Maigidana,
Maganar rashin gida ɗazu a mota na kwana,
Fili nake buƙata na biya Maigidana,
Kaza gare ta gashi na biɗa ba jini ba.

A wannan waƙar, Makaɗi Kamilu ya bi wani salon yin roƙo ta yadda ya fara neman Ahmad Lawan da ya dube shi. A nan, da ya ce, yana nufin a yi masa wani alheri, amma a layi na gaba sai ya bayyana matsalarsa ta farko, wato rashin gida wanda ya sabbaba kwanansa a cikin mota yayin da ya je Abuja.

3. Waƙar Gafara Koko

Gindin Waƙa : Gafara Koko, tunda mun taɓa mun ji Fura.
Jagora : Yanzu waƙa ta tashi sai gurin Gwarzona,
Jinin sharifai ba ka san ɗumi ba balle ƙuna,
Dutsin cikin ruwa ba ka yamutse ba domin rana,
Mu gaida Babagoni dole na yaba Gwarzona,
Fage na kyauta wallahi ka fi wancan suna,
Batun siyasa bana o’o ya ware da suna,
Mu gaida SSG Jarumi na ce Gwarzona,
Fage na alƙawari duk a duniya kai suna,
Idan ya ce zai mana ai kamar yana hannuna,
Mu gaida Babagoni Jalla ya tsare Gwarzona,
Ka duba lambata kuma ka je zuwa sunana,
Ka ban kujera ni ma na je Gabas ɗan baiwa.

A nan kuma, ya yi ƙoƙarin yin roƙo ta sigar ambato Babagoni Mashina da jarumi wanda muddin ya ce zai bayar, to tamkar ya bayar ɗin. Sai ya shiga fagen roƙonsa nan take, a inda ya roƙi ya ba shi kujerar Hajji. A nan dai, ya roƙi kujerar Hajji ce a taƙaice.

4. Waƙar Masassara Mai Saurin Duka

Gindin Waƙa : Masassara mai saurin duka, kun ji kunya ‘yan PDP.
Jagora : Abdul’aziz Yari yau na zo ni wajen ka waƙa ta kawo ni,
‘Yan amshi : Masassara mai saurin duka
Jagora : Mota nake so amma ta hawa zan hau na tuƙa in ka ba ni,
‘Yan amshi : Kun ji kunya ‘yan PDP,
Jagora : Birnin Gusau za ni gun sa kwa nan ne ya ba ni motar in ya ji ni,
‘Yan amshi : Masassara mai saurin duka,
Jagora : In ya ce ga ta ba shakka wallahi waqa ta tai riba.
‘Yan amshi : Masassara mai saurin duka
Jagora : Kun ji kunya ‘yan PDP,
‘Yan amshi : Dukkanin mutumin da ya bar ku a ko’ina ne shi ya ci riba.

A nan, ya roƙi mota a wurin Abdul’aziz Yari da ya ba shi mota, har ma yake nunawa cewa fa, idan aka ce ga motar; to fa waƙa ta yi riba, ma’ana roƙon da ya yi ya amfanar.

Jagora : Mai Mala Maigidana wai shin ni da kai me yai zahi ne?,
‘Yan amshi : Masassara mai saurin duka
Jagora : Ni so nake yi na je ni Haji ga kuma lokacin tsadar jirgi ne,
‘Yan amshi : Kun ji kunya ‘yan PDP,
Jagora : Ka ce da Gwamnanmu B.B yai mini agaji Oga ka gane,
‘Yan amshi : Masassara mai saurin duka,
Jagora : In ban da Barno zuwa Legas na tabbata ban hau jirgi ba.
‘Yan amshi : Masassara mai saurin duka
Jagora : Kun ji kunya ‘yan PDP,
‘Yan amshi : Dukkanin mutumin da ya bar ku a ko’ina ne shi ya ci riba.

Duk a cikin waƙar, sai ya ƙara yin wani roƙon ga Mai Mala Buni inda ya nemi ya nemar masa kujerar Hajji a wurin Gwamnan Jihar Yobe, wato Alhaji Ibrahim Geidam, har ma yake nuna shi fa in ban da daga Borno zuwa Legas bai taɓa hawa Jirgi ba. A Taƙaice dai a nan ma ya roƙi kujerar Hajji ce.

5 Waƙar Na Je Buni

Gindin Waƙa : Na je Buni, Mai Mala ba ya gida
Jagora : Zuwa da wuri mutanenmu ya hi zuwan wari,
Idan Kura ta kuɓuce a nemo sasari,
Hausawa sun ka ce walla guntun gatari
Shi yaf fi ka je ka ce wane yi min haƙƙuri,
Akwai wahala da nomansa kun san tsaddari,
Idan har za ka nome shi sai kai haƙƙuri,
Gwani ɗan Boni mai maganin ‘yan tunziri,
Idan dai ga ƙuli gehe saura ƙahuri,
Kujerar Hajji aka ba ni saura guzziri,
Ka ba ni dala dubu ukku na bar damuwa.

A wannan ɗiya, ya bayyana cewa an riga an ba shi kujerar Hajji, to abin da yake son Mai Mala Buni ya masa, shi ne ya ba shi guzirin da zai bari a gida da abin da zai yi ɗawainiya yayin aikin Hajji, har ma ya yanke adadin abin da yake so, wato dala dubu uku. A taƙaice a nan, ya roƙi a ba shi kuɗi domin samun tafiya aikin Hajjin da zai tafi wanda tuni an biya masa ko kuma dai ya biya wa kansa.

6 Waƙar Daga Geidam Sai Buni

Gindin Waƙa : Daga ya ƙare Gwamna Geidam sai Buni.
Jagora : Wai Mai Mala ya za a yi ne to ni dai ga ni,
Da ka canjan mota da ka birge ni,
Domin waccan motar Oga tai rauni,
In za ka sayan wata to in zo har Buni,
Da ka ƙi sayan motar da an nuna ni,
Sarki Allah Shi ne mai kakkare ni,
Da ‘yan bangar wancan da sun yanka ni,
Kyautar nono ita ce kyauta ta Hilani,
Kyautar mota ita ce kyautar ɗan Buni,
Iyakar su yi kuwwa ban hau motar ba.

A wannan ɗiya kuwa, Makaɗi Kamilu Almajiri ya roƙi Mai Mala Buni da ya canja masa mota, inda har ma yake shaida masa cewar motarsa ce fa ta yi rauni, wato ta lalace.

Sannan ya yi nuni idan fa ya ƙi saya masa motar, to fa za a nuna shi, ma’ana maƙiya ko ‘yan adawarsa za su rinƙa yi masa dariya, domin ga shi ya yi roƙo amma an ƙi amsa masa, kuma alhali ya cancanci a amsa masan.

‘Yan amshi : Daga ya ƙare Gwamna Geidam sai Buni,
Babban Zaki ba ya tsoron kuraye,
Ga ƙarfi ga ƙarfe ba mu ɗau roba ba.

Jagora : Kura har limamin tsoro ban tsoro,
Ga Kura na yawo ga Giwa toro,
Jiya na ga zuwan Gwamna taro yai taro,
Ga nan shukar Malum ga shanun Jauro,
Wasa za ai ko ko zancen ‘yan horo,
In Mai Mala na gwamna da mun yi ta voro,
Sabon shuka taka waccan kuma gyauro,
Waken Suya shi ne ƙarshen duk ƙwaro,
Kai sarkin kyauta ne Ogana ƙaro,
Ni dai mota ita ce ba ka ɗan miƙan ba.

A wannan ɗiya ma, ya roƙi mota ce daga wurin Mai Mala Buni, inda a sigar roƙon yake nuni da cewa fa ya masa wani abu, amma bai miƙa masa mota ba, ma’ana bai ba shi kyautar mota ba.

7. Waƙar ‘Yan Jo’aye

Gindin Waƙa : Komai munaƙisa
Jagora : Gida nake biɗa Damaturu dan ni ma na sha kwana,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : In dai akwai Bukar Dauda ku ma kanku kun shina,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : In dai gyaɗa tana waje ba a zance da geguna,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : Na gaida Maigida Bukar bin Dauda ban da shi gudun talakkawa.

A nan kuma, sai ya roƙi gida a wurin Hon. Bukar Dauda, inda ya nemi a ba shi gida a Damaturu Fadar Gwamnatin Jihar Yobe. Kasancewar Makaɗi Kamilu ɗan Nguru ne, ya sanya kuma ga Damaturu inda nan ce gidan mulki, sai ya nemi a ba shi gida domin shi ma ya zama yana da gida a can, ko kuma ma ya tare ya koma can gaba ɗaya.

Jagora : Kowa ya zo gaban ka Sarki sai ya doka tambura,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : Na gaida shi Sanate President mai ƙaunar mu nai ƙira,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : Zan je da tambura gaban Sardauna na ba da shawara,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : Oga ka taimaka ka ban matsayi ni ma a san ina gidan Giwa.

A nan kuma, sai ya roƙi Shugaban Sanatocin Nijeriya da ya ba shi aiki. Wani abin mamaki a nan, mafi yawan roƙon mawaƙa, sun fi roƙon gida, kujerar Hajji da mota, amma a nan, sai Kamilu ya roƙi a ba shi aiki.

Jagora : Sai Baba Malam ina S.S.G namu na yaba,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : In dai akwai dala hannun dogo ba a kai shi ungo ba,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : Kyauta da igiya ta lilo ya fi a ba ni tak kaba,
‘Yan amshi : Talakawa,
Jagora : Kahin da rana in yi ɗanwake gara tun da sahe in biɗo kanwa.

A nan, Kamilu ya bi wani salo a saye domin yin roƙo. Domin da farko bayan ya yaba wa Baba Malam , sannan sai ya nuna ita kyauta idan za a yi da babban abu ita ce kyauta, wato idan za a ɗaure wani abu domin a yi kyautarsa da igiya, to muddin wannan abin mai yawa ne, to fa da lilo za a ɗaure, domin igiya ba za ta iya ɗaure shi yadda ake so ba, misali kuɗi. To wannan ɗabi’a ce ta Baba Malam Wali. Sannan sai ya nuna idan fa zai nemi wani abin da zai yi amfani da shi da safe, to tun rana ko dare zai nema domin da safe ya samu ya yi amfani da wannan abin. Sai a nan ya yi amfani da kanwa idan ana son yin ɗanwake.

8. Waƙar Rtd. Hon. Adamu Dala Dogo

Gindin Waƙa : Sannu Adam Dala Dogo.
Jagora : Taimaka Difiti ka ban wata mota mai kyawu kalar birni,
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Saboda mahassada in na zo na wuce sai sui ta ruɗani,
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Kullum magana suke maja ma bai samu ba balle ni,
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Ni dai Allah na roƙa Tabaraka ba gunki na roƙa ba,
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Dubban jama’a muna sai kai,
‘Yan amshi : Bana ma mun nemi alfarma Difiti ka wuce muna fata.

Jagora : Da sanda muna qanana muna tashe tsaba muke nema,
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Amma kuma yau a tashen da za mu yi Toyota muke nema,
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Difiti bari dai na zo kusa in zauna dan in kwatanta ma,
‘Yan amshi : Ɗan duƙununu,
Jagora : Sai an ba shi,
‘Yan amshi : Ba ya tashi,
Jagora : Sai da tsaba,
‘Yan amshi : Kamilu kai fa?,
Jagora : Sai an ba ni,
‘Yan amshi : Kai ma ba ka tashi, × 4
Jagora : Sai da mota, × 4
‘Yan amshi : Sannu Adam Dala Dogo,
Jagora : Dubban jama’a muna sai kai,
‘Yan amshi : Bana ma mun nemi alfarma Difiti ka wuce muna fata.

Idan aka lura da waɗannan ɗiya biyu da suka gabata, za a iske nan ma Kamilu Almajirin Mawaƙa ya yi roƙo, roƙon kuwa a fili; inda ya nemi a saya masa mota kai tsaye.

A wannan salo, ya bayyana ƙarara nau’in motar da yake so, wato nau’in motar da ake shiga a birni, sai kuma ya bayyana dalilansa na neman mota. Idan muka koma ga ɗa na gaba, sai kwatanta abin da suke roƙa a yayin wasan tashe , kuma har ma ya kawo ɗaya daga cikin wasannin, wato wasan Ba Ma Tashi . Amma shi a nan, sai ya bayyana abin da yake so, wato mota, kuma ma sai ya bayyana ƙirar motar da yake so Toyota. A lura, a nan Kamilu ya haɗe wasanni guda biyu wuri ɗaya, wato ‘Ɗan duƙununu’ da tashen ‘Ba na tashi’, waɗannan tashe ne guda biyu mabambanta, amma sai ya haɗe su a matsayin tashe guda.

9. Waƙar Hon. Alhaji Shu’aibu Ɗanladi Hamza

Gindin Waƙa : Sai Baba Shu’aibu mun gamsu.
Jagora : Jamilu zan kira Cross Fire zauna daram ka ƙyale sokaye,
‘Yan amshi : Mu dai ba za mu fasa canji ba,
Jagora : Jamilu Rabbana ya kare ka bar banza da shi da ɓallaye,
‘Yan amshi : Mu dai ba za mu fasa canji ba,
Jagora : Akwai batu da ni da kai babba Jamilu dan ka ba ni filaye,
‘Yan amshi : Mu dai ba za mu fasa canji ba,
Jagora : Addu’a nake gami da fata Jamilu ban so ka bar ni ‘yamti ba.
‘Yan amshi : Sai Baba Shu’aibu mun gamsu,
Jagora : Guru Central ka zo ka gyara ta,
‘Yan amshi : Wuce mu bi ka 2011 ba za mu fasa canji ba.

Jagora : Na gai da Nura sai Oga wataƙil Nura za ya duba ni,
‘Yan amshi : Mu dai ba za mu fasa canji ba,
Jagora : Domin kwa maigidan haya ne Nura yake ta ƙoƙarin ya ta da ni,
‘Yan amshi : Mu dai ba za mu fasa canji ba,
Jagora : Jiya ma ya shigo da ‘yan sanda ya turo su zo su kama ni,
‘Yan amshi : Mu dai ba za mu fasa canji ba,
Jagora :Wannan wata ga shi yai nisa kuma ga shi ban biya su wancan ba,
‘Yan amshi : Sai Baba Shu’aibu mun gamsu,
Jagora : Guru Central ka zo ka gyara ta,
‘Yan amshi : Wuce mu bi ka 2011 ba za mu fasa canji ba.

Idan aka bi waɗannan ɗiya guda biyu da suka gabata, za a ga Kamilu ya yi roƙo ta wasu sigogi mabambanta guda biyu.

Siga ta farko, sai ya nemi Jamilu ya ba shi fili, amma fa idan har filin bai samu ba, to kar ya bar shi hannu-rabbana, ma’ana ya ba shi wani abu. A taƙaice a nan, ya bayyana abin da yake son a ba shi kyauta. A sigar roƙo ta biyu, sai ya nuna gida yake buƙata, domin a roƙon ya yi saye inda ya nuna masu gidan haya ne suka azazzale shi; har ta kai ga suna ta ƙoƙarin sai ya tashi la’akari da yadda suke takura masa.

A nan, ya nuna cewa, bai biya su kuɗinsu na haya ba, to ka ga kenan idan ana son faranta masa, shi ne a ba shi gida ko a saya masa wani, ko kuma a biya masa kuɗin hayar gaba ɗaya.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Wayon Roƙo a Adabin Baka: Nazarin Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta bayani a kan Nazarin Yabo Daga Cikin Waƙoƙin Ala dannan nan.

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceNazarin Yabo Daga Cikin Waƙoƙin Ala
Labarin na GabaChinese Rice