ZANGON RAYUWAR ‘YA MACE A ƘASASHEN YAMMA (TURAI)
1- Mahaifiyarta in ta haifeta tana farin ciki da ita matuƙa amma fa ba wanda ya san waye mahaifinta!!
2- Ta shiga makarantar Nursery ba ta san waye mahaifinta ba!!
3- Ta shiga Primary ba ta san waye mahaifinta ba!!
4- Ta shiga ƙaramar sakandire (Junior) ba ta san waye mahaifinta ba!!
5- Ta shiga babbar sakandire (Senior) da shekarun ‘yan matanci kuma ba ta san waye mahaifinta ba!!
6- A dukkanin waɗannan zango da ta yi ta shiga mahaifiyarta kuma tana can tana gararamba daga hannun wannan namijin zuwa wani don ta samu miji kar rayuwarta ta ja ta tsufa!!
7- Lokacin da budurwa ta kai shekara 18 tana da zaɓi biyu ne ko dai ta cigaba da zama da mahaifiyarta tana biyan kuɗin zaman da take a gidan (haya) ko a kore ta daga gidan gaba ɗaya!!
8- Yawanci takan fita daga gidan sabo da lokacin tana ɗaliba a jami’a kuma tana so ta zauna tare da abokinta (Boy Friend) a lokacin!!
9- Bisa larura na ba yadda za ta yi hakan sai ta sa ta fara ko wacce irin sana’a don ta samu kuɗin da za ta biya kuɗin karatunta na jami’a da kuma kuɗin zaman da take da abokinta (Boy Friend) (wannan in ta cigaba da zama da aboki ɗaya fa kenan) !!
10- A kullum tana fuskantar taɓe-taɓe (Sexual Harassment) ba ta kuma da zaɓi sai abu biyu ko dai ta fanɗare ta zama cikakkiyar karuwa ko kuma ta cigaba da gararamba daga wannan gidan zuwa wancan gidan daga kuma ƙarƙashin wannan abokin (Boy Friend) zuwa wancan abokin (Boy Friend) daban!!
11- Wasu kamfanoni na turai suna amfani da buƙatar kuɗi da ‘yan matan da suke ciki sai su shiga amfani da su wajen shirya fina-finan batsa!!
12- Da yawa daga cikin matan suna fuskantar fyaɗe wataƙila ma a kashe su akan titi a banza!!
13- Lokacin da ta girma ta tsufa sai ‘ya’yanta (wataƙila su ma ba su san waye uban su ba) su rabu da ita babu kuma makawa na jefa ta gidan gajiyayyu, masu imani da mutunci a cikin su su ne waɗanda za su dinga zuwa shekara bayan shekara ranar bikin uwa (Mother’s Day) su ba ta furanni su yi hotuna daga nan kuma su kama gabansu sai wata shekarar kuma (in ma ta haifi ya’yan kenan da za su ji tausayinta har ma su kai ta gidan gijayayyun kenan) !!
ZANGON RAYUWAR ‘YA MACE MUSULMA:
1- Lokacin da aka haife ta mahaifinta da mahaifiyarta da kakanta da kakarta da ‘yan uwa da masoya duk su yi farin ciki.
2- Za ta shiga gaba ɗaya zangon karatunta tana rayuwa ƙarƙashin kulawar mahaifinta da mahaifiyata ta na mai rayuwa cikin jin daɗi da farin ciki.
3- Za ta gama karatunta tana rayuwa a gidan mahaifanta cikin girmamawa da darajtawa.
4- In mai son ta da aure ya bayyana sai mahaifinta ya shiga bincike a kansa da tambaya akan halayyarsa.
5-Ta yi aure ta haihu jin daɗin da ta ji a baya ya ƙara maimaituwa a kan ‘ya’yanta.
6- In ta girma lokacin da ta manyanta ‘ya’yanta sai su shiga rigegeniya don kulawa da ita da yi mata hidima.
Bayan duk waɗannan sai wani sakarai ya zo cikinmu yana ihu cewa wai ana tauyewa mata haƙƙinsu, ya kuma dinga jifan masu kamun kai a cikin al’umma da ƙauyanci da rashin wayewa!!
Yana mai kira cewa lallai sai an yi koyi da turawa wanda mun ga yadda rayuwar mace take farawa take karewa !!
Allah mun gode maka bisa ni’imar musulunci.
14 August 2018
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu