Wani masani na cewa zuzzurfan bincike ba shi ne abinda ke samar da kyakkyawan littafi ba. Hanyar da ka bi wajen sa binciken naka a littafi shi ne muhimmin abu. A nan akwai wasu abubuwa da ya dace mu kula da su.
1) Ba kowanne irin sakamakon bincike ake sa wa a rubutu ba. Wani abin rashin bayyana shi ya fi zama maslaha fiye da bayyanawa.
Lokacin da Bala Anas ke bincike kan littafin Zinaru na ‘yan Kano to Jidda, ya ci karo da wani labari mai tayar da hankali. Akwai wasu ‘yan daba da ake cewa ‘yan agulla da ke zaune a Jidda. Su har maza suke yi wa fyade. Yaranmu ne da aka haifa a can suka taso ba kulawa. Da gangan ya ƙi kawo labarinsu.
Ko a kwanakin nan mun je bincike hukumar NDLEA sun faɗa mana yadda ake haɗa alawar Tom Tom da wasu lemuka ana cakewa. To ka ga ba za ka saka irin wannan a labari ba, don wani sai ya koya.
2) Ko da ka tara sakamakon binciken naka, idan ka ce za ka zuba shi haka zai iya gundurar mai karatu.
Akwai hikimar da za ka yi. Sai ka raba bayanin a ɓangare daban daban na cikin labarin. Irin yadda Amira Souley ta yi a cikin littafinta na kallo ya koma sama. Hirar da ta gudana tsakanin ma’aurata kan abinda ya shafi zuciya da ƙwaƙwalwa.
Danna nan don karanta amfanin bincike a rubutu
Edita; Rumasa’u M. Kallamu