Abubuwan Suke Sa Hakan
- Babban abinda yake kawo hakan shine fata ko Kuma garkuwar jikin mutum saboda bakon yanayi data tsinci kanta aciki dalilin karfen allurar kokuma ruwan allurar musamman allurar rigakafi wato vaccines.
- Wasu kuma allergic reaction ne yasa hakan
- Wasu kuma rashin bin ka’idar allura yayin gabatar da ita ga ma aikacin lafiya da kuma marah lafiya misali (wasu matan sai suce a musu a zaninsu) ga ma’aikaci kuma rashin gwarewa wajen jan allurar hakan zai jawo bakin allurar a baci, da dai sauransu
Alamomin Sun Haɗa Da
- Zafi in an taba gun
- Kumburi agun (swelling)
- Kaikayin wajen allurar
- Zafi (pain)
- Wajen zai yi ja (redness)
- kuraje
Abunda Mutum Zaiyi Wajan Yadaina Ciwo Sune Kamar Haka
Mutane dayawa hakan yana warkewane batare da sunsha komai ba dakanshi yake tafiya amma in yakai kwana biyu
- Mutum yanemi kankara yasa agun na tsawon mintina 10 zuwa 15
- In kuma yana zafi sosai sai a sha maganin rage radadi
- Amfani da lidocaine skin cream
Abu Na Ƙarshe Kuma Sshine Inhar Alamomin Suka Hada Da :
- Taruwar jini a wajen allurar
- Matsanaicin zafin wajen allurar
- Matsainaicin ƙaiƙayi
Ko kuma ya kai kimanin sati daya sai mutum ya garzaya asibiti mafi kusa domin tantancewa dakuma daukar mataki so inaga bawani abun ɗa ga hankali bane in anbarshi ma insha Allah within 2day’s zai warke da kanshi
Domin karanta amsar wannan tambayar Ina Bada Nono Amma Baya Isar Jaririna, Ko Kuwa Ba Maiƙo Danna nan
[…] Domin karanta cikekken bayani akan Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura} Danna nan […]