Physiology da Hausa Kashi na Takwas: Gastrointestinal System(Sashin Sarrafa Abinci)

0
34

Yana da gaɓoɓi wanda ke aiwatar da wannan aikin. Su ne; Baki, Maƙoshi, Tumbi, Hanta, maɗaciya, Ƙaramin hanji da babban hanji, Pankiris

  1. Baki: Shi ne ƙofa ta farko wadda ake fara niƙa abinci ta hanyar amfani da yawu da haƙora da kuma sinadarai irin su Amailez.
  2. Maƙoshi: Bututu ne musamman domin wucewar abincin da aka taune aka mulmule shi. Yana wucewa ne ta ɗabi’ar matsewa da buɗewa.
  3. Tumbi (Stomach): Ana kiran shi da tanki, domin shike ajiye abinci na ɗan wani lokaci kamar awa 4 kafin a tura shi zuwa ka ƙaramin hanji. Tumbi na da wata siffa ta musamman wadda ke hana abinci komawa zuwa maƙoshi ko wucewa zuwa ƙaramin hanji idan ba a buƙatar hakan. A sama da shi akwai matsi wanda ke hana abinci komawa, ana kiran shi da lower oesophageal sphincter kasa da shi kuma pyloric sphincter.
  4. Hanta da maɗaciya: Hanta na da fa’idoji da yawa . Yayin da kowace fa’ida na da alaƙa da wannan sashin.

Yana dakyau ku karanta Physiology da Hausa Kashi na Bakwai: Respiratory System (Sashin Numfashi)

A sashin sarrafa abinci, hanta na taka muhimmiyar rawa wajen haɗa Bile wato maɗaciya, sannan a kwararo shi zuwa ga mataki na farko na ƙaramin hanji wanda ake kira da diyodenom (duodenum). Amfanin wannan maɗaciyar shi ne narkar da maiƙon da aka ci. 

Ƙaramin hanji: Ya kasu kashi uku kashi na farko shi ne Diyodenum wanda yake ɗauke da ƙofar dake karɓar maɗaciya yayin da abinci ya isa zuwa cikin ƙaramin hanjin. Ma’ana dukkan sarrafawa da niƙawa na abinci yana faruwa ne a wannan kashin farko na ƙaramin hanji. Bayan niƙa abinci a wannan matakin ne ake karɓar sarrafaffen abinci zuwa ga cikin jini domin kai su zuwa cikin ƙwayar halittu.

Yana dakyau ka/ki karanta Physiology da Hausa kashi na hudu: Autonomous nervous system (Sashin Bada Umarni Da Amsa Saƙo)

Pankiris: Wani sashe ne a cikin cikin ɗan Adam wanda yake ɗauke da sinadaran niƙa abinci, sannan yana ɗauke da maziri da ya kai zuwa ka ƙaramin hanji domin isar da wannan sinadaran niƙa abinci zuwa ƙanana.

Babban Hanji: Babban hanji na da fa’idoji da yawa. Ɗaya daga ciki shi ne; Shine yake karɓar abincin da jiki bai buƙatar sa ya sarrafa shi tare da amfani da sinadarai wajen mai da shi kashi. Sannan a wannan babban hanjin ne ake samar da Bitamin Ta hanyar kimiyya dake faruwa a wannan wajen. Babban hanji na zuƙar ruwa daga cikin jikinmu idan ana bukatar nika, domin samar da abinda ake buƙata.

A ƙarshe duk abinda jiki bai buƙata akan fidda shi ta hanyar bayan-gida ko fitsari ko kuma gumi.

Domin karanta Physiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa) Danna nan

labarin da ya wucePhysiology da Hausa Kashi na Bakwai: Respiratory System (Sashin Numfashi)
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Tara: Hematology (Jini da Abubuwan da ya ƙunsa )
Dr. Yasir Aminu Ado
Ni dalibin likitanci ne nayi karatun likitanci a Kasar Sudan, Ina koyar da daliban jami'a masu tasowa ilimin karutun likitaci a saukake cikin harshen Hausa