Physiology da Hausa Kashi na Hudu: Autonomous nervous system (Sashin Bada Umarni Da Amsa Saƙo)

0
64

Ire-iren Nervous system wato sashin bada umarni da amsa saƙo mai amfani da lantarki ya kasu kashi 2:

Somatic nervous system Wato sashen bada umarni na sa-kai: Yana sarrafa gaɓoɓi wanda muke iya motsawa da kanmu.

Misali tsokokin dake jikin ƙashi wanda ke ba mu damar tafiya da motsawa…

Autonomic nervous system 

Yana sarrafa gaɓoɓin wanda ba mu da iko a kansu . Misali tsokar dake zuciya da kuma tsokokin cikin hanji.

Rabe-raben Autonomic Nervous system

Ya kasu kashi 2:

yana dakyau ku karanta Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)

Kashin Sympathetic: Wato nau’in da ke aiki a lokacin firgici ko wasanni na motsa jiki, misali gudu.

Parasympathetic: Nau’in dake aiki a lokacin hutu ko barci

Bambancin dake tsakaninsu
  • Motsi ko tsoro na zaburar da Sympathetic
  • Barci ko hutu na zaburar da parasympathetic.

Ana fitar da Sinadarai na bayar da ƙarfin jiki a yayin da mutum ya yi niyyar fada ko gudu, wanda ake cewa fight or flight. 

Catabolism wato sarrafa abincin da aka ajiye na cho domin ba wa jiki ƙarfi. Ana kuma killace sinadairai masu ba wa jiki ƙarfi a lokacin buƙatar hutu. Wato Anabolism.

Shin kun karanta Physiology da Hausa kashi na biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam Shiga nan domin karantawa 

Sympathetic na aiki a dukkan gaɓoɓi da sashe na jiki. 

Parasympathetic na aiki a waje ɗaya inda ake so ya yi aiki. 

Neurotransmitter (tsaka-tsakiyar isar saƙo)

Wasu sinadarai ne masu zaburar da  neuron, wato ɗan aiken umarnin kwakwalwa zuwa ga na gaba. 

Su ne:

  • Achetilecholine da noradrenaline a sympathetic 
  • Achetilcholine a parasympathetic

Yadda jiki ke sauyawa idan sympathetic da parasympathetic na aiki:

  • Ƙwayar Idanuwa da bubbuɗewa a sympathetic 
  • Ƙwayar idanuwa na tsukewa a parasympathetic 
  • Yawu na samuwa a adadi kadɗan tare da kauri. 
  • Yawu na samuwa a adadi mai yawa kuma a tsinke ba da kauri ba. 
  • Hanyoyin shigar iska na cikin huhu wato bronchioles na bubbuɗewa. 
  • Hanyoyin shigar iska na huhu na tsukewa. 
  • Bugun zuciya na ƙaruwa a sympathetic. 
  • Bugun zuciya na raguwa parasympathetic. 
  • Ƙarfin matsar zuciya domin fidda jini na ƙaruwa a sympathetic. 
  • Amma bai ƙaruwa a parasympathetic,sabo da ba shi da alaƙa da babban ɗakin da ke da jini wato ventricle na zuciya. 
  • Motsin kayan ciki domin sarrafa abinci da na raguwa a sympathetic.
  • Motsin kayan ciki domin sarrafa abinci da na ƙaruwa a parasympathetic.
  • Hanyoyin jini na tsuttsukewa na jiki amma wanda ke ba wa zuciya jini wato coronary artery na bubbuɗewa a sympathetic.
  • Parasympathetic ba su da alaƙa da ƙofofin jini.
  • Sympathetic Na Sa Gumi
  • Parasympathetic Bai da alaƙa da sashen gumi.

Domin karanta Physiology da Hausa kashi na uku: Excitable Tissues (Sassan motsi na jiki) Danna nan

labarin da ya wucePhysiology da Hausa Kashi na Uku: Excitable Tissues (Sassan motsi na jiki)
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Biyar: Temperature and Metabolic Rate (Ɗumi Ko Yanayi Na Jiki)
Dr. Yasir Aminu Ado
Ni dalibin likitanci ne nayi karatun likitanci a Kasar Sudan, Ina koyar da daliban jami'a masu tasowa ilimin karutun likitaci a saukake cikin harshen Hausa