Daukacin Abubuwan dake jikin ɗan Adam namiji wanda nauyinsa ya kai kilo 70
Ruwa: Kashi 60
Kitse: Kashi 18
Sinadarai: kashi 7
-CHO: ƙasa da kashi 1
-Ganin yadda ruwa yake da kaso mafi yawa a jiki, hakan yasa ruwa ya kasance mafi amfanin a jikin ɗan Adam. Idan aka rasa da yawa daga cikin ruwan jiki, rayuwa za tai wahala a cikin yan kwanaki masu zuwa, saɓanin idan an rasa cin abinci, mutum yakan iya rayuwa har tsawan wata ɗaya.
Rabe raben kaso na ruwa a mutane daban-daban
Adadin ruwan jikinmu na da alaƙa da shekaru da jinsi da kuma girman jiki.
Shekaru: Ruwan jikinmu na raguwa yayin da muke ƙara shekaru, ma’ana yara sun fi manya yawan ruwa a jiki.
Jinsi: Maza sun fi mata yawan ruwa a jiki saboda yawancin mata na da kitse fiye da maza.
Girman jiki: Sirara sun fi masu ƙiba yawan ruwa a jiki, saboda yawan kitse da masu ƙiba ke da shi.
Abin da ruwan jiki ya ƙunsa
Kamar yadda muka bayyana a baya cewa, ƙwayoyin halittu na ɗauke da ruwa a cikin su, haka zalika a zagaye suke da ruwa.
Muka ce kuma ruwan jiki ya rabu kashi biyu;
Ruwan dake ciki da kuma wajen ƙwayar halitta.
- A inda ruwan dake cikin ƙwayar halitta ya ƙunshi kashi 2 cikin 3 na ruwan jiki gaba ɗaya, ko kashi 40 cikin ɗari na nauyin jiki baki ɗaya.
- Ruwan dake wajen ƙwayar halitta.
A inda ruwan dake wajen ƙwayar halitta ya ƙunshi kashi 1 cikin 3 na ruwan jiki gaba ɗaya, ko kashi 20 na nauyin jiki.
Ruwan dake wajen jiki ya rabu kashi 3
- Ruwan dake cikin jijiyoyi kaso 25 cikin 100.
- Ruwan dake tsakanin jijiya da ƙwayar halitta kaso 75 cikin 100.
Abubuwan dake sauya yanayin ruwan jiki
- Osmosis wato adadin gishiri dake jiki.
- Sodium potasium pump, wato shiga da fitar sinadarai na sodiyom da potashiyom a kowace ƙwayar halitta,
Ƙarin bayani duk inda sinadarin sodiyom ya je ruwa na biye da shi.
Saitin adadin ruwan jiki
- Adadin ruwan jikinmu na da alaƙa da adadin ruwan da muke sha a rana.
- Adadin ruwan da muke sha na da alaƙa da buƙatuwarmu ga ruwa, wato shan ruwa
- Adadin ruwan dake jikinmu na da alaƙa da rashin ruwa a cikin jiki, sanadiyyar wata cuta, misali gudawa ko amai(haraswa).
Yana dakyau ku karanta na farko wato Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)
[…] Yana dkayu ku karanta Physiology da Hausa Kashi na Biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam […]
[…] Domin karanta Physiology da Hausa kashi na biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam Danna nan […]