Musa Ɗanƙwairo A Koyo Da Biyayyar Waƙa

0
13

Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya tashi, ya girma a gidansu; ya tarar da ana harka ta kiɗa da waƙa. Magabatansa tun daga Kaka Maiganga da mahaifinsa dukkansu makaɗa ne na noma; da yaƙi da kuma Sarauta da suka aiwatar da kiɗa da farar ganga da kuma gangar kotso.

A bisa ɗabi’a ta gadon gida, mutum zai koyi abin da ya tarar ana gudanarwa a gidansu. Hausawa sukan ce, gadon gida alala ga rago, a yayin da Musa Ɗanqwairo ya fara tasawa, sai ya karkata wajen koyon abubuwa na hukunce-hukuncen addinin Musulunci da kuma hidimomin kiɗa da waƙa waɗanda suka shafi wasu harkoi na zamantakewar Hausawa.

Musa Ɗanƙwairo ya fara biyayya ta sanin makamar waƙar baka tun a wajen mahaifinsa, Makaɗa Usman Ɗankwanagga24. A wajen mahaifin nasa ya koyi kaɗa kanzagi da karɓin waƙa da jajircewa a karin waƙa da samar da rauji na waƙa (Gusau, 2019: sh. 10-11).

Haka kuma Musa Ɗanƙwairo ya daɗa gwangwajewa a zuba ɗiya na waƙar baka a biyayyar da ya yi a yayin Halifantakar da ya yi wa wansa Abdu Kurna. Domin himmar Musa Ɗanƙwairo da ƙwazonsa da basirarsa, wansa Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Abdu Kurna, ya naɗa shi ya zama Daudun Kiɗa kuma Ɗangaladimansa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Musa Ɗanƙwairo a Gayaunar Waƙa danna nan.

Don karanta cikakken bayani a kan Waƙar Shawara Ga Mai Bilicin danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMaganganu Na Ƙarya A Kan Kashe Husaini (RA)
Labarin na GabaZikiri Yayin Shiga Gida
Prof. Sa’idu Muhammad Gusau
FARFESA SA'IDU MUHAMMAD GUSAU, An haife shi a Gusau jihar Sakkwato, (Maris 24, 1952). Ya yi karatun firamare na Islamiyya daga 1965-1969, ya je kwalejin sarkin Musulmi Abubakar daga Junairu 1970 zuwa Yuni 1973. Ya yi Diploma, Digiri Na farko (B.A), na biyu (M.A) da Digiri na uku (Ph.D) duk a jami'ar Bayero, Kano.