Mummunan Ƙarshe Da Kyakkyawan Ƙarshe

0
1008
MUMMUNAN ƘARSHE DA KYAKKYAWAN ƘARSHE
Babu wani abu da ya fi damun duk mai hankali da imani a wannan duniyar, irin tunanin yadda ƙarshensa zai kasance.
Mutuwa dai dole ce, sai dai tashin hankalinta shi ne rashin sanin lokacin da za ta zo. Kuma babbar damuwa ita ce, a wane yanayi za ta riski mutum? Wanda wannan shi ne zai haska me zai tarar bayan ya mutu ?
Abin da mutum ya cika a kansa, a kansa za a tashe shi, koda kuwa a farko ba a kansa ya taso ba. Misali ɗalibi a makaranta ko shekara nawa ya yi, ana la’akari ne da sakamakon da ya samu a jarrabawarsa ta ƙarshe, da zai yi shekaru uku yana abin kirki sai a ta huɗu ya kama shiririta, to fa da sakamakon shiriritar nan zai fita, haka kuma Inda shiriritar ya fara sai a ƙarshe ya yi wa kansa faɗa, ya nutsu ya gyara kurakuransa, sai ka ga ya fita da kyakkyawan sakamako.To tamkar  haka rayuwar duniya take.
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce,
وانما الاعمال بالخواتيم
Ana lura ne da aikin da mutum ya cika a kansa.(Bukhari hds 507,Muslim hds na 161)
Abin da mutum ya taso a kansa, da shi yake cikawa,sai dai kuma, ba kasafai wanda ya taso kan alhairi yake cikawa da sharri ba, amma kuma hakan tana faruwa,wato mutum ya yi ƙarkon kifi, Allah ya kiyaye.
Dukkanin bayin Allah nagari suna cike da jin tsoron yadda ƙarshensu zai kasance, shi yasa suke yin iya yinsu, su kasance cikin ayyukan alhairi a kowane lokaci, saboda ba su san lokacin da ta Allah za ta kasance ba a kansu, duk da haka suna ta addu’ar Allah ya ba su kyakkyawar cikawa, ba sa sakin jiki ballantana su ruɗu da ayyukansu.
Mummunan ƙarshe shi ne mutum ya mutu a kan kafirci, ko shakka da kokonto ko musu da jayayya kan Musulunci ko wani abu da yake tabbatacce sananne a Musulunci.
Haka kuma, wanda ya mutu yana aikata wani aiki na saɓon Allah Ta’ala, ko wata sha’awa ta haram.
Kamar yadda wanda ya mutu yana cikin wata ibada sahihiya ko yana kan wani aikin alhairi za a ce ya yi kyakkyawar cikawa.
ABUBUWAN DA SUKE JAWO MUMMUNAN ƘARSHE
Allah Ta’ala cikin rahamarsa ga bayinsa, ya bayyana musu alhairi da sakamakonsa da kuma sharri da abin da yake jawowa, sannan kuma ya bayyana hanyoyin su, don a bi hanyar da take ta alhairi kuma a kaucewa hanyar sharri.
Wasu daga cikin abubuwan da suke jawo mummuna ƙarshe su ne:
1.Rayuwa a kan munanan aƙidu waɗanda suka sabawa koyarwar Alkur’ani da sunnar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
2.Rayuwa a kan ibadu na bidi’a waɗanda manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bai yi ba, bai koyar ba ,kuma ba a yi ba a zamaninsa.
3.MUNAFUNCI
Ya haɗa da ɓoye kafirci a zuciya da bayyana Musulumci, da riya da girman kai da jin kai da jin isa, amma yana nuna wa mutane, shi mai ikhlasi ne da tawali’u da sauran munanan halaye na zuciya da mutum zai rinƙa nuna wa mutane saɓanin su, alhali suna danƙare a cikin zuciyarsa.
4.NACEWA A KAN SAƁON ALLAH TA’ALA
A yi a yi mutum ya tuba ya ƙi, har mutuwa ta zo masa yana tsakiyar wannan sabon, kamar wanda zai mutu a wurin sata ko fashi ko ta’addanci,ko zina ko madigo ko luwaɗi ko shaye-shaye da sauransu. Kamar yadda wani da zai mutu aka laƙanta masa kalmar shahada sai ya kasa faɗa, ya kama waƙe-waƙe har ya mutu, wani kuma ya yi ihun yan ball, wani ya yi maganganun ‘yan caca, haka dai.
Allah Ta’ala ya kiyaye mu.
5.TSANANIN SON ABIN DUNIYA
Wanda zai mamaye zuciya, har ya kai ga mutum ya mance da lahirarsa ta yadda zai iya aikata komai in dai zai samu abin duniya. Wannan yana jawo mummunan ƙarshe.
6.YIN ADDINI RABI DA RABI
Da yawa waɗansu mutane sukan rinƙa sako-sako da addininsu, saboda da’awar wayewar kai ko kuma don kada a ce su masu tsattsauran ra’ayi Musulunci ne, sai ka ga har kunyar nuna cewa su Musulmi ne suke a wani wurin, kuma In ta kama har taya kafirai kafirci suke yi, ko su taya fajirai fajirci, don dai kada a bar su a baya, ko a ce su gidadawa ne.
Wajibi a duk inda musulmi ya tsinci kansa ya bi Musulunci gwargwadon ikonsa.
7.JINKIRIN TUBA DA JINKIRIN AIKI MANAGARCI
Jinkirin tuba da sa rana da jan ƙafa wajen aikata ayyukan alhairi, alhali mutum yana da ikon yi, yana jawo mummunan ƙarshe, saboda rai ba a hannun mutum yake ba, mutuwa za ta iya zuwa kowane lokaci ba notis.
Ya Allah Ta’ala ka kiyaye mu da mummunan karshe.
ABUBUWAN DA SUKE JAWO KYAKYAWAN ƘARSHEN
1.TSORON ALLAH TA’ALA
Rayuwa cikin bin dokokin Allah Ta’ala da bin sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da kaucewa abubuwan da suka hana, gwargwadon iko, yana sa a samu kyakkyawar cikawa da izinin Allah Ta’ala.
2. TSAYUWA A KAN MUSULUNCI
Ba raba ƙafa ba munafunci ba wani biye-biye ko kame-kame.
3.GASKIYA
Gaskiya a zuci,da harshe da hali da mu’amala, ba ƙarya ba yaudara ba ha’inci ba zamba ba cin amana.
4. YAWAN TUNANIN MUTUWA DA ZIYARTAR MAƘABARTA
Yawan tuna mutuwa, yana yi wa mutum linzami kan munanan ayyuka, yana kuma zaburar da mutum kan aikata kyawawan ayyuka da komawa ga Allah Ta’ala, haka ma ZIYARTAR MAKABARTA, ziyara irin wacce sunna ta koyar.
5.KYAUTATA ZATO GA ALLAH TA’ALA
Lallai ne a koda yaushe mutum ya kasance mai kyatata zatonsa ga Allah Ta’ala, tare da tsoron azabarsa da kuma aikata ayyukan alhairi. A yayin da alamun mutuwa suka bayyana an fi so zaton samun rahamar Allah Ta’ala ya fi rinjaye a zuciyar mutum a kan tsoron azabarsa, wannan yana sawa a samu kyakkyawar cikawa.
6.TUBA DA MAYAR DA KAYAN ZALUNCI KO NEMAN YAFIYAR WAƊANDA AKA ZALUNTA
7.GUJEWA ABUBUWAN DA SUKE JAWO MUMMUNAR CIKAWA WAƊANDA AKA YI BAYANI SU A FARKO.
Ya kamata kowa ya yi wa kansa hisabi tun kafin a yi masa. Mu gaya wa kanmu gaskiya, mu ɗora kawunanmu a kan sikeli na gaskiya. Mu daina kallon laifukan wasu, mu shagala da kawunanmu. Mu sani a kowane sakan mutuwa na iya cimma na.! Laa ilaaha illalah.
Ya Allah Ta’ala ka azurta mu da kyakkyawan ƙarshe ka sa kalmar mu ta karshe a duniya ta kasance “LAA ILAAHA ILLALAH MUHAMMADUR RASULULLAH”.
labarin da ya wuceMaganin Damuwa
Labarin na GabaInganta Rayuwar Ma’aurata Ta Hanyar Karin Magana