Kafin bayanin alamomin,mu fara da menene “fibroid”? Fibroid wata matsalace a mahaifar mace,wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace, ƙullutun naman mai cutar da lafiya yana ɗanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam.
” Fibroid” kalmar turanci ce,domin sauƙin furuci da Hausa, za mu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu a nan, an yi ƙiyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid,musamman a shekarunsu na samun haihuwa – wato daga shekara 16 zuwa 50, wani ƙiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid.
A lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ƙuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al’adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause), mafi yawan nau’in faibirod da ake samu ba shi da alaƙa da ciwon-daji {kansa} (not cancer), ƙululun ko ƙwallon irin wanda ba ya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous), yana iya fitowa fiye da ɗaya a mahaifa, kamar guda uku, huɗu ko ma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahaifa.
Domin karanta bayani akan Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki Danna nan
Alamomin Matsalar Faibirod Sun Haɗa Da:
- Zubar jinin al’ada mai yawa, ko na tsawon lokaci
- Zubar jini a baƙin lokuta ko tsakanin lokutan haila
- Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
- Yawan fitsari
- Ciwon baya daga ƙasan baya
- Jin zafi ko ciwo lokacin yin jima’i
- Rashin jini a jiki saboda yawan zubar jini
- Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙullutun a ciki
- Basur mai sa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
- Ciwon ƙafa
- Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu ba ne, musamman idan faibirod ɗin ya girma
- Ko ma rashin ganin wasu ko ɗaya daga cikin alamamomin da muka yi bayani
Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Faibirod Zai Iya Haddasawa:
- Matsala wajen haihuwa lokacin naƙuda
- Matsala yayin fama da juna biyu
- Matsalar rashin samun juna biyu rashin ɗaukar ciki ga mace saboda ƙullutun ya toshe ko danne wani ɓangaren mahaifa
- Yawan ɓari (zubewar ciki)
Yana da matuƙar muhimmanci mai jin ɗaya ko fiye daga cikin waɗannan matsalolin ya je asibiti domin bincike ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka, idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.
Menene Ke Kawo Matsalar Faibirod?
Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin da ya sa ake samun fibroid, sai dai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod, daga shekara 16 zuwa 50 shi ne lokacin da sinadarin ya fi yawa a cikin jinin mace.
Eestrogen ɗaya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato estrogen sinadari ne na jinsin mace da ke tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta da ya shafi jima’i, a lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shi ne ke saka sha’awa ko yawan sha’awa ga mace idan ya yi yawa
Yana da kyau ku karanta Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za a Magance
A lokacin balaga ƙwayayen mahaifa (ovaries) za su fara samar da sinadarin, za a iya kiran eestrogen da suna maƙerin ‘ƴan mata domin kuwa shi ne ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayin da take girma, a taƙaice, estrogen shi ne sinadarin da faibirod suka dogara da shi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamashin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacin da mace ta bar yin al’ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙanƙancewa.
Wasu Dalilai Da Ka Iya Sa Yiwuwar Mace Ta Samu Faibirod
- Gado: Idan mahaifiyarki ko ‘ƴar uwarki ta taɓa samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.
- Jinsin baƙar fata: Mutanen Africa ko ƙasashen baƙar fata, wato jinsin baƙar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod, kuma matasa mata baƙar fata su ne suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa, a ƙasashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu ƙasashen, ba kasafai ake samun matansu da matsalar ba.
- Amfani da hanyoyin tsai da haihuwa: (ƙwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin za su iya sa faibirod ya girma), ƙiba, ƙarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa, shan giya da sauransu.
Hanyoyin asibiti na magance matsalar ya ƙunshi:
Aikin tiyata (surgery) domin cire ƙullutun tare da cire wani ɓangaren mahaifa “uterus” [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa’annan wani nau’in aiki tiyatar [Myomectomy] wanda ba ya hana haihuwa a gaba, ƙwayoyin magani da wasu hanyoyin, musamman idan ya girma aikin tiyata ne aka fi yi domin rabuwa da matsalar
Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse ƙarami ko ƙasa da haka, ko girman lemun tsami ko na zaƙi, ko girman ƙwallo, girman jariri ko ma fiye da girman jariri, musamman idan ba a cire shi ba ko magance shi ba, wasu likutan ana ganin idan faibirod ya kai girman inci (4 inches ko 9-10 cm) to akwai buƙatar a yi aikin tiyata domin a cire shi, idan Kuma bai kai hakan ba insha Allahu akwai maganin da zai narkar da shi (FIBROID SHRINKER).
Domin karanta bayani akan Ciwan Hanta {Hepatitis} Danna nan