Minene Fibroid? {Ƙarnin Mahaifa } Da Kuma Abubuwan Da Suke Kawosa

0
51

Kafin bayanin alamomin,mu fara da minene “fibroid”? Fibroid wata matsalace a mahaifar mace,wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa  kuma yana girma a mahaifar mace,ƙulutun naman mai cutar da lafiya  yana ɗanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam.

” Fibroid” kalmar turanci ce,domin sauƙin furuci da Hausa,zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan ,anyi ƙiyasi cewa cikin mata 100,kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid,musamman a shekarunsu na samun haihuwa – wato daga shekara 16 zuwa 50,wani ƙiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid

A lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ƙuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al’adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause),mafi yawan nau’in faibirod da ake samu bayada alaƙa da ciwon-daji {kansa} (not cancer),ƙululun ko ƙwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous),yana iya fitiwo fiye da ɗaya a mahaifa,kamar guda uku,huɗu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.

Domin karanta bayani akan Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki Danna nan

 Alamomin Matsalar Faibirod Sun Haɗa Ha:
  •  Zubar jinin al’adah mai yawa,ko na tsawon lokaci
  • Zubar jini a baƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila
  • Ciwon ƙugu,saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
  • Yawan fitsari
  • Ciwon baya daga ƙasan baya
  • Jin zafi ko ciwo lokacin yin jima’i
  • Rashin jini a jiki saboda yawan zubar jini
  • Rashin jin dadi a mara,musamman saboda girman ƙulutun a ciki
  • Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
  • Ciwon ƙafa
  • Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane,musamman idan faibirod din ya girma
  • Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani
Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Faibirod Zai Iya Haddasawa:
  • Matsala wajen haihuwa lokacin naƙuda
  • Matsala yayin fama da juna biyu
  • Matsalar rashin samun juna biyu  rashin ɗaukar ciki ga mace saboda ƙulutun ya toshe taushe ko danne wani  bangaren mahaifa
  • Yawan ɓari zubewar ciki

Yana da matuƙar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin yaje asibiti domin binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka,idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.

Menene Ke Kawo Matsalar Faibirod?

Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid,saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod,daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace.

Eestrogen daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace,wato estrogen sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace,rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima’i,a lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito,kuma shine ke saka sha’awa ko yawan sha’awa ga mace idan yayi yawa

Yana dakyau ku karanta Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za’a Magance

A lokacin balaga ƙwayayan mahaifa(ovaries)zasu fara samar da sinadarin,za’a iya kiran eestrogen da suna maƙerin ƴan mata domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma,a taƙaice,eestrogen shine sinadarin da faibirod suka dogara dashi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamasin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al’ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙanƙancewa.

Wasu Dalilai Da Ka Iya Sa Yiwuwar Mace Ta Samu Faibirod
  • Gado: Idan mahaifiyarki ko ƴar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.
  • Jinsin baƙar fata:  Mutanen Africa ko ƙasashen bakar fata,wato jinsin baƙar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod,kuma matasa mata baƙar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa,a ƙasashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu ƙasashen,ba kasafai ake samun matansu da matsalar ba.
  • Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa: (ƙwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma),ƙiba,ƙarancin sindarin vitamin D,yawan cin jan-nama,rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa,shangiya da sauransu.
Hanyoyin asibiti na magance matsalar asibiti ya ƙunshi:

Aikin tiyata (surgery) domin cire ƙulutun tare da cire wani bangaren mahaifa “uterus” [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa,sa’annan wani nau’in  aiki tiyatar [Myomectomy] wanda baya hana haihuwa a gaba,ƙwayoyin magani da wasu hanyoyin,musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar

Girman faibirod na iya zama ƙwatanƙwacin girman dutse karami ko ƙasa da haka,ko girman lemun tsami ko na zaƙi,ko girman ƙwallo,girman jariri koma fiye da girman jariri,musamman idan ba’a cire shiba ko magance saba,wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci (4 inches ko 9-10 cm) to akwai buƙatar ayi aikin tiyata domin a cire shi,idan Kuma bai kai hakan ba insha Allahu akwai maganin da zai nar kar da shi (FIBROID SHRINKER).

Domin karanta bayani akan Ciwan Hanta {Hepatitis} Danna nan

labarin da ya wuceCiwan Hanta {Hepatitis}
Labarin na GabaMutane Da Yawa Sukan Yi Tambaya Akan Aa Yaya Za a Samu Hanya Mafi Sauki Ta Yin Tazarar Haihuwa Ba Tare Da Shan Ƙwayoyi Ba