Menene Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?

0
19

Zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne burin dukkan ɗan Adam maza da mata, manya da yara musulmi da wanda ba musulmi ba. Za mu iya cewa, yanayin nutsuwa da jin daɗi da farin ciki, annashuwa da samun gamsuwa a zuci, ba tare da wani tsoro ko fargaba ko damuwa ba, a kan abin da ya wuce ko tsoron abin da zai zo. 

Waɗannan abubuwa in sun haɗu, a iya kiran su zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan an ɗan kusanto da ma’ana ne kawai amma a gaskiya sanin haƙiƙanin zaman lafiya da kwanciyar hankali sai wanda yake cikinsa. Larabawa suna kiran sa “Sa’adah” kuma suna fassara shi da cewa kishiyar sa wato “tsiya”. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Rukunan zaman lafiya da kwanciyar hankali guda uku ne: 

  1. Ingantacciyar zuciya da jiki. 
  2. ingantacciyar rayuwa. 
  3. Kyakkyawar makoma. 

Duk mutumin da zuciyarsa ta gurɓata da kafirci, bidi’a, zalunci, sha’awa da sauran su ko jikinsa ya yarda da lalaci da son hutu a kowane lokaci, da karɓa ba bayarwa, haƙiƙa wannan mutum ba shi ba zaman lafiya, ballantana kwanciyar hankali. 

Haka kuma duk mutumin da ya ɗauki rayuwa ta ƙarya mara tabbas mai cike da ruɗani da hauma-hauma, wacce ba ta da wani tushe ballantana makama shi ma ba zai shiga cikin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. 

Domin Karanta Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe Danna Nan

Sanin kyakkyawar makoma da tabbacin inda aka dosa yana da muhimmanci wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Yanzu a haɗa musulmi da ya yarda da Allah da ranar Lahira da wuta da Aljanna, da kafiri wanda shi kawai duniya ita ce farko ita ce ƙarshe a wurinsa? 

To amma wace hanya ce mafificiya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? To mai karatu sai in ce maka nan fa ake yin ta, saboda duk mutumin da ka yi wa wannan tambaya, zai ba ka amsa saɓanin ta ɗan uwansa. 

Mutane da yawa suna cikin ruɗani game da wannan amsa, kowa kuma aiki yake yi tuƙuru domin tabbatar da ita a kan kansa. Amma fa kashi casa’in bisa ɗari sun yi hannun riga da hanyar ba da amsa ingantacciya. Kafin a bayar da amsa, bari mu yi nazarin kaɗan daga cikin ruɗu da mutane da dama suke ciki, game da hanyoyın samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHakkin Zaman Gidan Miji
Labarin na GabaYin Afuwa Da Kyautatawa Wanda Ya Ɓata Maka