Wannan muƙalar za ta yi duba ne akan matsalolin auratayya, saboda idan mutum ya yi duba na tsanaki sosai akan sha’anin aure, zai ga ana ta samun mace-macen aure a wannan yanayin da muke ciki. Saboda haka, aure shi ne jigo na rayuwar mutum, sannan aure shi ne yake samar da nutsuwa da kwanciyar hankali a tsakanin mutane, shi ne abin da yake ƙulla alaƙa mai ɗorewa a tsakanin mutane.
GABATARWA
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah (Subhanahu wata’ala), wanda ya yi sama da ƙasa ba tare da an yi musu tokara ba, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam).
Bayan haka, abubuwan da suke kawo matsaloli akan mace-macen aure suna da alaƙa da sauka daga kan tafarkin tsarin addinin musulunci da kuma abubuwan da al’adar mu take kai, wanda addininmu ya amince mana da sauran su.
MUTUWAR AURE
Bismillah rahmanin rahim, akwai abubuwa da yawa, waɗanda suke kawo akan mutuwar aure a tsakanin ma’aurata da yawa kamar su, auran ƙarya, aikin gwamnati, rashin iya girki, rashin iya kwanciya, auran dole, rashin iya kulawa, rashin iya gina alaƙar soyayya, rashin iya kalaman soyayyya, rashin iya kwalliya da tsafta, rashin wasa da juna, rashin shawara ga juna, sai wasu cututtuka wanda suke faru a tsakanin ma’aurata, wasa da abokan miji, wasa da ƙannan miji da buri kamar yadda ya zo a cikin littafi na biyar (Kambun Ma’aurata 5). Haka kuma, a cikin litttafi mun kawo ƙarin wasu daga ciki, kamar haka:-
1. Auran ƙarya: Yana kawo mutuwar aure, saboda gina aure akan ƙarya da facaka da dukiya, sannan da nuna mata mutum ɗan wajan wani ne ko nuna mata motoci har da gidaje masu alfarma, bugu da ƙari ma har da ‘yan uwa masu alfarma. Sannan da yi mata hidima ta kece alfarma, ta kayayyaki ko anko na bukukuwa na alfarma, musamman a watan ramadan da sallar idin ƙaramar sallah da babbar sallah ko yawan turo mata kati a waya da dai sauransu.
2. Aikin gwamnati:– yana ɗaya daga cikin abin da ke kawo mutuwar aure ga wasu mazajan, saboda yana iya samun rashin iya kulawa da fahimtar junansu, sannan ana iya mu’amala da wasu mazajan a wajen aiki har ma da wasa da dariya har da goya ta a motarsa ko mashin ɗinsa wanda haka yana kawo zargi a tsakanin ma’aurata da dai sauransu.
3. Rashin iya girki:- rashin iya abinci yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo rabuwar aure, saboda yana ɗaya daga cikin abubuwan da maza suka fi so a wajen matayensu, domin macen da ta iya abinci daban take a wajan mijinta, saboda haka ya zama tilas ga wacce take so ta mallake mijinta ta iya girki, girkin ma ta yi da hannunta, saboda idan girki ya yi zai yaba mata sosai sannan za su yi so da shaƙuwar junansu.
4. Auren dole:- auren dole yana kawo rabuwar aure da raba kan al’umma ta kowanne irin hali, saboda an gina auran ne akan dole, ba a a kan soyayya ba. Saboda wata alfarma da yake da ita a wajen iyayenta ko ‘yan uwanta. Haka kuma ‘ya’yaye yana da matuƙar kyau sosai idan sun samu kan su a cikin hali, kada su yi gaggawar rabuwa, su fahimci dalilan da yasa aka yi musu wannan aure, saboda idan ma sun bi zaɓin zuciyar su, to su iya haɗuwa da waɗansu matsaloli na rayuwa, saboda kaucewa umarnin iyayensu.
5. Rashin iya kulawa:- rashin iya kulawa da suna yana iya kawo mutuwar aure, saboda wasu mata suna barin mazajensu a wulaƙance ko maza su ma suna barin matarsu a wulaƙance, yin hakan bai dace ba ga addinin musulunci, saboda haka barin mace ko miji babu wata kulawa mai kyau yana kawo mutuwar aure, musammamma a karkara, za ka ga miji ya bar matarsa da wankau har da sirfau don ta nemi abin da za ta sa a baka da rana. Saboda shi mijinta abin da wai ya sani a kansa shi ne ciyarwan safe da yamma, yin hakan bai dace ga musulmi ba sannan bidi’a ce kai tsaye. Ya Allah ka ba mu yadda za mu yi mu sahayar da matayanmu har da ‘ya’yanmu.
6. Rashin iya gina aure a kan soyayya:- yana kawo mutuwar aure, saboda duk abin da aka gina shi akan soyayya komai daren daɗewa yana nan, misali kalli uwa da ‘yarta, kalli mahaifi da ‘ya’yansa, saboda duk irin yanayin da ma’aurata suka tsinci kansu a ciki za su iya haƙuri da junansu su zauna lafiya komai tsanani ko talauci ba za su iya rabuwa ba, ya Allah ka haɗa mu da masu so da ƙaunar mu don Allah, ameen summa ameen.
7. Rashin iya kalamai na soyayya:- rashin iya kalamai masu tafiyar da zukatan mijinki shi ma yana iya kawo rabuwar aure, saboda rashin magana mai daɗi, amma fa ku lura idan sun je siyan sarƙa da awarwaro da kayan kwalliya iri-iri, za ka gan su suna raunar da muryarsu, haka ma ida za su yi magana da abokannan miji ko ƙannan miji, a cikin sassanyar murya za ka ji su suna yi.
Amma wata macen idan za ta kira ka ko magana da mijinta sai ka ji tana cewa, Salman, Salman, Salman, ko Farisi, Farisi, Farisi, babu wasu kalamai masu daɗin sauraro kamar su , “ya angona, ya mijina, ya maigidana , ya abin taƙamata, ya shugabana, ya yayana, ya dalin-ɗina, ya jinin jikina, ya rayuwata, ya ranka shi dade, ya honarable, ya honi je, ya habibina, ya sahibina, ya hasken rayuwata, ya abban ameer, ya jigon rayuwata, ya annurin zuciyata, ya farin cikin rayuwata, my dear, ya abban ameerah, ya abin alfaharina, ya abban dadi, ya baban Salman ko Salma ko Yasir da dai sauransu.
Mene ne so?
So wata tsoka ce ko jijiya ce a cikin zuciya, wanda Allah yake halittar bayinsa ko ɗan Adam da ita, don haka so wata ƙaramar tsoka ce, wadda kowane ɗan-Adam yake da ita, sa’annnan shi so ba a ganinsa, saboda sirri ne wanda Allah ya ɓoye a zuciyar kowane mutum, sai dai kawai alamoninsa ne za ka iya ganewa da zarar wani ko wata ta kamu da son wani. Saboda haka, shi so daga ƙarami yake farawa sai ya cigaba da girma da faɗaɗa, saboda yawan tunanin abin da kake so ko kike so.
Saboda haka, a lokacin da mutun ya shiga cikin soyayyar abokinsa, sai kuma ya kasance suna ƙaunar juna, to idan hakan ta faru, so ya haɗu a nan, sannan sai su fahimci abubuwan da ke dauwamar da ƙauna guda goma sha biyu (12) kamar su:-
a. Tausayawa juna: Idan wani abu ya samu ɗayansu na musiba da dai sauransu, sai a nuna damuwa akan haka.
b. Kulawa da juna: Kamar yadda muka yi bayaninsa a darasin da ya wuce.
c. Yarda da juna: Yana ga samari da ‘yan mata har da ma’aurata, su yarda da junansu, ma’ana su fahimci abin da kowannansu zai iya aikatawa saboda mahassada.
d. Amincewa juna: Yana ga samari da yan mata har da ma’aurata su amincewa junansu, saboda zargi yana iya kawo matsala a tsakanin masoya.
e. Fahimtar juna: Ya zama wajibi akan masoya su fahimci junansu, saboda munafikai ko magulmata.
f. Haƙuri da juna: Yin haƙuri da juna, idan wani ya yi laifi, sai a danne a zuciya, yana ƙara ƙauna a cikin zukatan masoya mai ɗorewa.
g. Kau da kai da juna: Kau da kai ga juna, yana ƙara soyayya a cikin zukatan masoya, saboda yawan zargi ko sa ido yana kawo rashin fahimtar juna.
h. Kyauta: Yawan yin kyauta, yana ƙara danƙon soyayya da ƙauna a cikin zukatan masoya.
i. Shawara da juna: Yawan shawara ga juna, yana kawo shaƙuwa da juna.
j. Danne zuciya: Kamar haƙuri ne, idan wani ya yi laifi ko ya ɓata muku rai ko fushi, sai a danne abin a cikin zuciya, ka yi kamar ba ka damu ba.
k. Rangwame ga juna: Yin afuwa ko uzuri, yana ƙara so da soyayya mai danƙo.
9. Kwalliya da tsafta: Suna ɗaya daga cikin abubuwan dake dauwamar da ƙauna, saboda ita tsafta ko kwalliya tana fito da ɗan Adam. Sannan ya zama dole a kansu, su guji baza sirrinsu da ɗaukar jita-jita har da zargin junansu. Sannan su guji zargi a cikin soyayyarsu, bugu da ƙari ma su lura da maƙiyansu har da mahassadansu da dai sauransu.
10. Rashin iya kwalliya da tsafta: Na iya kawo rabuwar ma’aurata, saboda ita tsafta cikon addinin musulunci ce, sannan ku san su ne abin da mai gida yake lura da shi ga matarsa har ma ‘yan uwansa. Saboda haka, ya zama wajibi akan matan aure su iya kwalliya da tsafta, saboda Allah (subhanahu wata’ala) yana san masu tsarki, ma’ana masu tsafta.
Har ila yau, kada matan aure su zauna ba tare da tsafta ba, musamman a dai-dai lokacin da miji yake dawowa gida, wata mace za ka ji hammatarta tana wari har da jikinta baki ɗaya, saboda ta bar hammatarta da gashi ba ta cisgewa (ko askewa), wata ma ɗakinta za ka ji yana wari kamar mai sayar da daddawa ko wacce ɓera ya mutu a cikin ɗakinta.
11. Rashin wasa da juna: Shi ma yana iya kawo rabuwar ma’aurata, saboda rashin zolaya da juna yana iya kawo rashin shaƙuwa da juna, babu laifi wata rana mai gida zai iya shan kwalliyarsa mai kyau ya fesa turaransa mai kamshi, ya fito bakin ƙofar ɗakin matarsa ya tsaya ya aika ko ya yi sallama ya kira ta, idan ta tambaya wane ne? Sai ya ce, “da ita honije ɗinki ne ke kira, bayan ta fito, sai ku tayin zantukanku na soyayya. Sannan babu laifi ku yi tseran gudu har da langa, amma idan babu kowa a gidan, sai ku kaɗai da dai sauransu.
12. Rashin shawara da juna: Yana iya kawo mutuwar aure, saboda yin wani abu ba tare da shawara ba, yana iya kawo saɓanin fahimta a tsakanin ma’aurata.
13. Rashin iya magana: Yana raba aure, saboda wata macen idan mijinta ya yi mata magana, sai ka ji tana cewa gani ko mene ne, wata ma macen idan mijinta yai kiranta tana ji sai ta yi shiru. Saboda haka, dole ne akan ma’aurata su iya kalaman da za su samar da nishaɗi, kamar su “idanuwana sun kasa rufewa, saboda rashin ganinka ko jin muryarka ya angona na wasu ɗan lokuta, kunnuwa sun kasa toshewa, saboda maraicin jin lallausar sautin muryarka na wasu ɗan lokuta, bacci ya ƙauracewa idanuwana, saboda rashin kallon fuskarka ya sahibina, a yanzu haka, babu komai a cikin zuciyata sai tunanin ganinka ya jigon rayuwata” haka shi ma mijinta zai yi mata, idan yana so ya ƙara samun so da shaƙuwa a wajan matarsa, kusha shagalin ku lafiya.
14. Rashin iya ado: Yana iya kawo rabuwar aure ko kishiya, saboda haka da zarar mijinta ya fita waje ya ga wata santaleliyar zugegiyar yarinya, sai ya ji yana sha’awar auranta, saboda ita kwalliya ko ado tana ƙarawa mutane kyau sosai.
Saboda duk mutanen da ka gani duk ma’abota kyau ne, sai dai rashin ado ya gusar da kyawunsu, ka duba ka gani ranar sallar idi ƙarama da babbar salla yaya? Saboda haka, ya zama wajibi akan ma’aurata su iya kwalliya da neman magunguna da za su iya gyara jikinsu, don neman ƙarin bayani ko magani za a iya nemana, Allah yasa mu dace.
15. Rashin iya tafiya: Tana iya kawo matsalar aure ga wasu mazan, saboda wasu mazan tafiyar mace suke fara kalla, da zarar matarsa ba ta iya tafiya ba, sai ya ji ta fara fita daga zuciyarsa, da zarar ya fita waje ya samu macen da ta iya tafiya ya aura. Saboda haka, mace ta iya tafiya sosai kamar yadda mu yi bayani a babin mallakar miji.
Haka kuma, lallai yana da matuƙar kyau sosai akan ma’aurata, su yi hattara sosai,saboda su sani fa shi aure ana gina shi akan ibada, domin samun dacewa a wajen Allah ranar lahira.
Har ila yau, duk wanda ya yi aure, sai ya yi haƙuri sosai a cikin rayuwarsu da matar sa, saboda sai ya samu wajen shekara ashirin ko kuma sama da haka, sa’annan zai fara jin daɗin zaman aurar su da ita.
Saboda daga kan shekara ɗaya zuwa huɗu(1-4), za su kwashi soyayyar su ne ,saboda babu wani nauyi sosai akan su mai yawa(`ya`ya), haka kuma daga kuma shekara huɗu zuwa takwas(4-8), wata rana zai iya samu cikin gidan kaca-kaca, idan ya yi mata magana akan haka, sai ta yi haƙuri ta gyara ko da ko abin ya ɓata mata rai.
Har ila yau, daga kan shekara takwas zuwa goma sha biyu (8-12) idan matar sa ta yi masa wani abu mara kyau ko kuma ya samu cikin gidan kaca-kaca, sai ya tambaye ta meye dalilin da yasa ta bar gidan kaca-kaca, to a wannan lokaci za ta iya mayar masa da saƙo kamar haka” toh! ka ba ni kuɗn da za’a siyo sabulun da za’a wanken kayan ne”?
Sa’annan kuma, daga kan shekara goma sha biyu zuwa goma sha shida(12-16), a wannan lokacin sun tara ‘ya’ya da yawa, haka kuma ba su da wani lokaci da za su zauna su yi wa kan su kwalliya, domin su ji daɗin tattaunawarsu, saboda neman abin da yaran su za su ci haɗi da abin da za a dafa musu har izuwa shekara ashirin da biyar da bakwai, to a wannan lokacin ne suke damar jin daɗin auran su, saboda ‘ya’yan su girma, sa’annan kuma matar sa ta kusa daina haihuwa.
Akwai abubuwa da dama, waɗanda su ke kawo mutuwar aure da yawa wanda In Sha Allah a littafin mun na uku za mu ji bayanin su da yardar Allah.
Don karanta fa’idojin da suke cikin yin aure danna nan
Domin karanta fa’idojin wadatar zuci danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu