Matakin Fara Karatu Da Rubutun Hausa

0
72

Muhammad Sahal Aliyu

GABATARWA
Tun a shekarun baya ne wuraren shekarar 1932 aka fara yunƙurin neman ingantacciyar hanyar da za a bi wajen yin rubutun Hausa, ba don komai ba sai don saboda irin yadda ake mu’amala da harshen kuma ake wallafe-wallafe da harshen. A yanzu harshen Hausa ya yi nisan da ba za a iya gano inda ya kai ba.

Ana amfani da harshen Hausa a makarantu tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, ana amfani da shi a gidajen rediyo da jaridu da muƙalu da talabijin da sha’anin addini da kuma lamuran siyasa.
Ba tare da tsawaita bayani ba, za mu yi ƙoƙarin fara sanin baƙaƙe da wasula.
A B C D E F G H I J K LM N O P Q R S T U V W X Y Z.

Waɗannan su ne baƙaƙen da ke amfani da su kamar yadda aka faɗa a baya cewa asalinsu daga harshen Turanci aka samo su. Sai dai kuma wani abu da aka gano a harshen Hausa shi ne: Akwai wasu baƙaƙe da harshen Hausa ya yi watsi da su ba ya amfani da su sam, ba don komai ba sai son ganin cewa ba su dace da yanayin furucin bakinsa ba. Waɗannan baƙaƙen da Hausa ta yi watsi da su, sun haɗa da:
P
Q
V

Bayan wannan kuma, akwai wasu ƙarin baƙaƙe waɗanda ake amfani da su a harshen Hausa, su waɗannan baƙaƙen babu su a cikin harshen Turanci. Su ne:
Ɓ
Ɗ
Ƙ

Baƙaƙen Hausa

Ya zama dole a fara sanin baƙaƙen Hausa, domin kuwa su ne ginshiƙin komai a harshen Hausa. Sanin kowa ne cewa waɗannan baƙaƙen an yi amfani da salon rubutun harshen Turanci ne aka samar da su, sai dai kuma an sami bambance-bambance a wurin rubuta wasu da kuma furucin su.

Manyan Baƙaƙen Hausa

B, Ɓ, C, D, Ɗ, F, FY, G, GW, GY, H, J, K, Ƙ, KW, KY, ƘW, ƘY, L, M, N, R, S, SH, T, TS, W, Y, ‘Y, Z.

Ƙananun Baƙaƙe

b, ɓ, c, d, ɗ, f, fy, g, gw, gy, h, j, k, ƙ, kw, ky, ƙw, ƙy, l, m, n, r, s, sh, t, ts, w, y, ‘y, z.
Waɗannan su ne baƙaƙen da ake amfani da su kamar yadda aka faɗa a baya cewa asalinsu daga harshen Turanci aka samo su. Sai dai kuma wani abu da aka gano a harshen Hausa shi ne, akwai wasu baƙaƙe da harshen Hausa ya yi watsi da su ba ya amfani da su sam, ba don komai ba sai son ganin cewa ba su dace da yanayin furucin bakinsa ba. Waɗannan baƙaƙen da Hausa ta yi watsi da su, sun haɗa da:
P
Q
V

A yanzu bayan mun fahimci waɗannan baƙaƙen to za mu yi ƙoƙarin kawo baƙaƙen Hausa zalla baki ɗaya domin ganin su a zahiri. Kamar yadda aka gani a sama, waɗannan su ne baƙaƙen da ake amfani da su a wurin rubutun Hausa da kuma wurin magana.

Ƙirƙirarrun Baƙaƙen Hausa

A wannan ɓangaren, za a yi bayanin wasu baƙaƙe ne waɗanda harshen Hausa ya samarwa kanshi domin dacewa da yanafin furucin bakinsa. Waɗannan ƙirƙirarrun baƙaƙen su ne:
FY, GW, GY, KW, KY, QW, QY, TS
fy, gw, gy, kw, ky, qw, qy, ts

Wasulan Hausa

Bayan mun fahimci waɗannan baƙaƙen na Hausa, sai kuma batun wasulan Hausa waɗanda su ne mahaɗin waɗancan baƙaƙen a wurin yin magana ko rubutu, domin kuwa dole sai da taimakon su ne za a sami damar yin kowane furuci da kuma yin magana.

Manyan Wasulan Hausa
A, E, I, O, U
Ƙananun Wasulan Hausa
a, i, o, u, e, ai, au,

Bayan mun fahimci waɗannan baƙaƙen da kuma wasulansu, to a yanzu za mu yi duba da misalai na kowanne baƙi domin ƙara fahimtar abin yadda ya kamata. Misali:

BAƘAƘE KALMOMI
B Baba, Bindiga, Bahaushe.
Ɓ Ɓarawo, Ɓera, Ɓawo
C Caca, Carbi, Cokali
D Dankali, Damisa, Doki
Ɗ Ɗaki, Ɗoki, Ɗawisu.
F Fatanya, Faranti, Famfo.
FY Fyace, Fyaɗe, Fyaɗa.
G Ganga, Gangami, Gado.
GW Gwanda, Gwangwani, Gwaiba
GY Gyangyaɗi, Gyaɗa, Gyara
H Harshe, Hausa, Hutu
J Jimina, Jagora, Jarabawa
K Katifa, Kaifi, Kaji
Ƙ Ƙarfi, Ƙato, Ƙofa
KW Kwakwa, Kwando, Kwalta
KY Kyankyaso, Kyauro, Kyau
ƘW Ƙwai, Ƙwallo, Ƙwarangwal.
ƘY Ƙyalle, Ƙyaure, Ƙyashi
L Lemu, Laushi, Loma
M Masara, Mahauci, Madara
N Nama, Noma, Nema
R Rami, Rijiya, Rigakafi
S Sauro, Sauri, Sata
SH Shanu , Shuka, Sheƙa
T Taliya, Tafiya, Takalmi
TS Tsuntsu , Tsamiya, Tsalle
W Wanka, Wanki, Waƙa
Y Yaƙi, Yaji, Yatsa
‘Y ‘Yanci, ‘Ya’ya,
Z Zaki, Zagi, Zango

Misalan Furucin Baƙaƙe Da Wasula

A nan za a yi magana ne a kan yadda ake furucin baƙaƙe haɗe da wasulansu:
A I O U E
Ba Bi Bo Bu Be
Ca Ci Co Cu Ce
Da Di Do Du De
Ɗa Ɗi Ɗo Ɗu Ɗe
Fa Fi Fo Fu Fe
Ga Gi Go Gu Ge
Ha Hi Ho Hu He
Ja Ji Jo Ju Je
Ka Ki Ko Ku Ke
La Li Lo Lu Le
Ma Mi Mo Mu Me
Na Ni No Nu Ne
Ra Ri Ro Ru Re
Sa Si So Su Se
Ta Ti To Tu Te
Wa Wi Wo Wu We
Ya Yi Yo Yu Ye
Za Zi Zo Zu Ze
Sha Shi Sho Shu She

Idan aka yi la’akari da wannan jadawalin da ya gabata a sama, to za a fahimci cewa lallai an biyo hanyar da za a fara gina kalma ko kalmomi da ake son yin amfani da su a cikin zantukanmu da ma rubutunmu.
Tattaunawa Tare Da Ɗalibai Don Fara Gina Kalmomi.

GAƁA

Mece ce gaɓa?
Gaɓa yanki ce na faɗar kalma mai tsarin baƙi (B) da wasali (W) a jere. Sani (1999). Wato baƙi da wasali su ne tubalan ginin gaɓa. A sanadiyyar samuwar gaɓa ne ake iya samar da kalma. Sannan kuma ita gaɓa tana samuwa ne gwargwadon tsawon kalma. Akwai kalma mai gaɓa ɗaya da mai gaɓa biyu da mai gaɓa uku da mai gaɓa huɗu da biyar har ma zuwa shida.

Kafin mu shiga cikin bayanin adadin yawan gaɓa, ya kamata mu fara sanin menene tsarin gaɓa? Tsarin gaɓa dai ya kasu zuwa gida uku ne, akwai:
BW
BWW
BWB
Misali:
Makaranta = BW-BW-BWB-BW
Mafarauta = BW-BW-BWW-BW
Tambaya = BWB-BW-BW
Ruwa = BW-BW
Zaurawa = BWW-BW-BW
Maƙwabci = BW-BWB-BW
Zalunci = BW-BWB-BW
Mayaudari = BW-BWW-BW-BW
Tausayi = BWW-BW-BW

Idan aka kalli waɗannan misalan, za a ga cewa gaba ɗaya waɗannan tsarin gaɓar da aka ambata a baya duk sun bayyana a cikin misalan kalmomin da suka gabata, wannan ya tabbatar mana da cewa kowace kalma ta Hausa ba ta wuce irin wannan tsarin in dai an ɗora ta a bisa wannan ma’aunin.

Adadin Yawan Gaɓa A Kalma

Bayan kuma mun fahimci waɗannan tsare-tsaren na gaɓa, to yanzu kuma za mu waiwaya kan batun yawan adadin gaɓoɓi da ake da su na kalma. Kalmomin da muke amfani da su a harshen Hausawa na yau da kullum ana samun wasu adadi na gaɓa da suke ɗauke da su. Daga cikin waɗannan adadin, akwai kalma mai gaɓa ɗaya da mai gaɓa biyu da mai uku da mai huɗu da mai biyar har ma akwai kalmar da take ɗauke da gaɓoɓi shida. Ga misalansu kamar haka:

Mai gaɓa ɗaya :
Ɗa
Rai
Kai
Ja
Ci
Ji
Yau
Kyau

Mai gaɓa biyu :
Fada
Uba
Alli
Kuka
Lemu
Ƙwarya

Mai gaɓa uku:
Tausayi
Alama
Kalmomi
Alewa
Tsintsiya
Masana
Makami

Mai gaɓa huɗu :
Makaranta
Majalisa
Rarrabewa
Tattarawa
Tattaunawa
Masarauta

Mai gaɓa biyar :
Masana’anta

Mai gaɓa shida:
Almubazzaranci

ALAMOMIN RUBUTU/ALAMOMIN AJIYE MAGANA

Akwai alamomi daban-daban da ake amfani da su wajen yin magana ko kuma rubutu. Wannan ya danganta da yanayin mai rubutu ko kuma mai magana. Akwai waɗannan alamomi guda goma. Ga su kamar haka:

Aya (.) wato inda magana ta ƙare aka tsaya.
Ruwa biyu/aya ruwa biyu (:) mai nuna alamar cewa wata maganar tana nan zuwa.
Waƙafi (,) don nuna hutawa a lokacin magana.
Waƙafi mai ruwa (;) don nuna magana mai cin gashin kanta. Ya yi kama da aya a wajen aiki.

Alamar tambaya (?) tana zuwa ne a lokacin da aka yi tambaya.
Alamar motsin rai (!) tana zuwa ne a lokacin da aka yi wani furuci mai sosa rai, kamar tsoro ko mamaki ko kuma ɓacin rai.
Karan ɗori (-) ana amfani da shi ne wajan haɗa harɗaɗɗiyar kalma.

Alamar zancen wani ( “ ” ) ana amfani da ita ne wajan tsakuro maganar wani kai tsaye kamar yadda ya furta zancensa.
Baka biyu ( ) ana amfani da ita ne don ƙara fayyace ma’anar wata kalma ko zance, ko kuma ƙarin bayani a kan wata magana.  Alamar zarcewa (……) ana amfani da ita ne don nuna cewa maganar da ake yi ba ta ƙare ba, wato maganar ba ta cika ba.

SUNA

Kalma suna idan aka kalle ta za a ga cewa kalma ce Bahaushiya wacce Hausawa suke amfani da ita. A nan za a iya bayyana suna da cewa:
“Duk wani abu mai rai ko maras rai, wanda ake iya gani da ido da wanda ba a iyawa, wanda ake iya taɓawa da hannu da wanda ba a iyawa.” (Sani, M.A.Z 1999)
Kenan za a iya cewa komai ma suna ne a bisa ma’anar da Sani. M.A.Z 1999 ya bayyana mana. Suna zai kasance duk wani abu da ake kiran mutum ko dabba ko kuma wani abu mai rai ko mara rai da wanda ake gani da kuma wanda ba a iya gani.

IRE-IREN SUNA

Akwai ire-iren suna da harshen Hausa ya kasafta su, akwai:
Sunan yanka
Suna Gama-gari
Gagara Ƙirga
Tattarau
Ɗan Aikatau

Sunan Yanka

Sunan yanka shi ne suna fitacce, keɓantacce ga mai shi. Misali:
Aliyu
Abdullahi
Aminatu
Zainab

Suna Gama-gari

Shi wannan akasin na yanka ne, wato kishiya. Suna ne na tarayya wanda kowa na iya shiga ciki ko amfani da shi. Misali:
Mutum
Ƙwaro
Jaririya
Littafi

Suna Gagara Ƙirga

Wannan yana nufin duk sunan wani abu wanda ba za a iya ƙirgawa ba. Misali:
Ruwa
Gishiri
Taki
Yaji
Gari

Suna Tattarau

Kamar yadda aka ji sunan wato tattarau, suna ne wanda ya tattara abu fiye da guda ɗaya. Misali:
Garke
Gungu
Ayari
Runduna
Bataliya

Ɗan Aikatau

Shi wannan sunan ya bambanta da sauran, domin kuwa suna ne wanda ya samu daga jikin “aikatau/aiki”. Misali:
Shara
Wanki
Girke-girke
Rayuwa

Domin karanta Rabe-Raben Aure Hausawa danna nan

WAKILIN SUNA

Bayan kuma mun gani kuma mun fahimci abin da ake kira suna, to yanzu kuma za mu leƙa mu ga batun da ake kira da suna “Wakilin suna”.
Sani, M.A.Z (1999) ya bayyana abin da ake kira da wakilin suna, inda ya ce:
“Wakilin suna nau’i ne na kalma da ake wakiltar suna a lokacin magana.”
Kenan duk wata kalma da za a yi amfani da ita wajen nuni zuwa ga suna, to ita ake nufi da wakilin suna. Misalan wakilin suna:
Ni
Kai
Ku
Su
Shi
Ita
Ke.  Waɗannan su ake kira da wakili/wakilan suna a lokacin magana.

ƘIRGA/ƘIDAYA A HAUSA

Ida nana batun ƙirga ana magana ne a kan ƙidaya da ake amfani da su domin nuna adadi ko yawa na wani abu. Akwai ƙidaya da harshen Hausa yake amfani da su, kaɗan daga cikin misalan ƙirga:
Sifili = 0
Ɗaya = 1
Biyu = 2
Uku = 3
Huɗu = 4
Biyar = 5
Shida = 6
Bakwai = 7
Takwas = 8
Tara = 9
Goma = 10
Goma sha ɗaya = 11
Goma sha biyu = 12
Goma sha uku = 13
Goma sha huɗu = 14
Goma sha biyar =15
Goma sha shida = 16
Goma sha = 17
Goma sha takwas =18
Goma sha tara =19
Ashirin = 20
Talatin = 30
Arba’in = 40
Hamsin = 50
Sittin = 60
Saba’in = 70
Tamanin = 80
Casa’in = 90
Ɗari = 100
Dubu ɗaya = 1,000
Miliyan = 1,000,000

GAISUWA

Gaisuwa na ɗaya daga cikin hanyar da take ƙara kawo soyayya da zumunci wacce take nuna halin dattaku da girmamawa. Saboda haka za a iya cewa gaisuwa na nufin:
“Gaishe da shugaba ko aboki” Qamusun Hausa (2006)

A wani ɓangaren kuma nuna girmamawa tare da nuna halin tarbiyya da kuma mutuntawa.
Gaisuwa a harshen Hausa ta rabu zuwa kashi uku, akwai:
Safe ko safiya. Irin wannan gaisuwa ana yin ta ne da safe a lokacin da aka wayi gari bayan an tashi daga baccin dare an wanke fuska (sallah). Ana fara wannan gaisuwar ce daga waye gari zuwa ƙarfe sha biyu na rana. Ana irin wannan gaisuwar ce kamar haka:
Ina kwana?
Mun kwana lafiya?
Barka da safiya.

Ta Rana. Ita wannan gaisuwa ana yin ta ne da rana, wato daga ƙarfe sha biyu na rana zuwa faɗuwar rana. Ga yadda ake yin gaisuwar:
Ina wuni?
Mun wuni lafiya?
Bar da rana.
Barka da yamma.

Ta Dare. Ita wannan gaisuwa tana farawa ne daga lokacin da rana ta faɗi zuwa lokacin kwanciya bacci. Ga yadda ake yin gaisuwar:
Barka da dare.

BAMBANCE JINSI

A cikin harshen Hausa ana rana halittu zuwa gida biyu idan aka zo ɓangaren jinsi, wato jinsin mata (mace) da kuma jinsin maza (namiji).
“Wannan yana nufin bambancewa tsakanin jinsin mutum ko na wani abu.” Jinju, M.H (1980).

Da wannan ma’anar kuma, za mu wuce kai tsaye wajan nuna abubuwan da suke bambance mana jinsin namiji da kuma jinsin mace. Daga cikin alamomin da ake gane kalma jinsin namji ne akwai:
Duk wasu kalmomi waxanda qarshensu ya qare da waxannan wasulan: i, o, u, e, to wannan Kalmar namji ne. misali: Jinsin Namiji
Jemage gari dutse jiki haƙuri ƙarshe
Babe raino rogo kasko lemu bugu
Baƙo rumbu gemu tuwo gurgu kuturu

Jinsin Mace
Kamar yadda aka yi bayanin alamomin jinsin namiji, a nan za a bayyana alamar da take nuna kalma mai nuni a kan jinsin mace. Duk wata kalma da ta ƙare da wasalin a to wannan kalmar mace ce. Misali:
Abarba rowa gwanja jaka loma
Zakanya mara riga ayaba agwagwa

Sai dai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba, akwai wasu keɓaɓɓun kalmomi waɗanda suka saɓa, wato sun kauce ma ƙa’idar da aka shimfiɗa wajen bambance jinsi. Akwai wasu kalmomi da suke ƙarewa da wasali masu nuni da alamar namiji amman kuma suna ɗauke da jinsin mace. Misali:
Kande Mairo Abu Asabe Jummai

Saboda haka wasu lokutan akan sami irin waɗannan kalmomi da suka saɓa ma ƙa’ida, amman hakan ba yana nuna ba daidai ba ne kuma ba zai haifar da wata matsala ba.
Sai dai kuma akwai wata ƙa’aida da Jinju, M.H (1980) ya ƙara bayyanawa, inda ya ce:
“Sunayen ranaku da na shekaru da na kusurwoyin duniya da na unguwanni da na garuruwa da na ƙasashe da kusurwoyi da kuma na adadi/ƙirga duk jinsin mace ne.

Sunayen Ranaku
Litinin Talata Laraba Alhamis Juma’a Asabar Lahadi

Sunayen Shekaru na Hausa
Su ma waɗannan sunayen duk jinsin mata ne. misali:
Bara Bana Baɗi
Kusurwoyi
Gabas Yamma Kudu Arewa Ƙasa Sama
Dama Hagu

Nahiyoyi
Afirka Asiya Amirka Turai Ostireliya
Adadi/ƙirga
Ƙirga da muke da su, su ma ɗin jinsin mace ce. Misali:
Ɗaya 1
Biyu 2
Uku 3
Ɗari 100

Shi kuwa Sani, M.A.Z (1999), ya ƙara yin bayani ne a kan yadda za a ƙara tantance kalma mai ɗauke da jinsin mace ko jinsin namiji, inda ya ce za a iya amfani da wani abu da ake kira madanganci wato (n da r). A lokacin da ake son ƙara tabbar da matsayin kalma na mazaunin jinsinta, sai a yi amfani da waɗannan ma’aunan guda biyu. Madangancin n yana wakiltar jinsin namiji inda ita kuma r tana wakiltar jinsin mace. Ana amfani da su ne a ƙarshen kalmar domin tabbatar da hakan.

Togiyra Jinsin Mace
Akwai waɗansu sunayen ƙarshensu a ne amman duk da haka jinsinsu namji ne, kamar:
Baka bawa ruwa zakara boka wata

LOKUTAN HAUSA

A wannan muhallin kuma za a yi ƙoƙarin yin bayani ne dangane da abin da ya shafi lokutan Hausa. A harshen Hausawa kwai lokuta guda bakwai. Sani, M.A.Z (1999).
Waɗannan lokutan su ne:
Shuɗaɗɗen na ɗaya mai alamar (a da n)
Shuɗaɗɗen lokaci na biyu mai alamar ( ´ )
Lokaci na yanzu na ɗaya mai alamar (na)
Lokaci na yanzu na biyu mai alamar (ke)
Lokaci mai zuwa/na gaba na ɗaya mai alamar (za)
Lokaci mai zuwa/na gaba na biyu mai alamar (a)
Lokaci sababben mai alamar (kan)

KAMMALAWA

Kamar yadda bayanai suka gabata dangane da baƙaƙen Hausa da wasulansu, za a fahimci cewa wannan wata ‘yar shimfiɗa ce aka soma yi kafin a fara shiga cikin batun ilimin harshen Hausa. An ga bayanai tare da masalai na kowane baƙi da aka ambata a baya. An kawo batun gaɓa da tsarinta da kuma adadin yawan gaɓoɓin da ake samu a cikin kalma. Sannan kuma an kawo batun gaisuwa da wakilan sunaye da batun jinsi da ƙirga da alamomin rubutu da kuma lokutan Hausa.

MANAZARTA

Bello, A. (2014) Sabon Nahawun Hausa. Ahmadu Bello University Press: Zaria Kaduna.
Bello, A. (2020) Daidaitacciyar Hausa Da Kare-Karen Harshen Hausa. Ahmadu Bello University Press: Zaria Kaduna.
Ƙamusun Hausa (2006), Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Bayero: Kano.
Sa’id, B. (2004) Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero: Kano.
Sani, M.A.Z. (1999) Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press: Ibadan.
Jinju, M.H (1980) Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limite: Zaria.

Danna nan don karanta Asalin Hausawa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMecece Ƙwaya?
Labarin na GabaNazarin Sara/Yayi A Harshen Hausa (Slang)