Akwai hanyoyi da yawa wajen rabuwa da irin waɗannan aljanu da ma wasu ba irin wannan ba. Ya zama duk inda aljani yake ajikin mutum sai ya gudu ya bar shi.
Matakan Rabuwa Da Jinnu:
Matakin farko akan so mara lafiya ta cire duk wani hoto a ɗakin da take kwana sannan ta kiyayi yawan kalle-kalle. Sannan ta sabarwa kanta kwanciya da alwala, idan za ta iya yi wa kanta ta yi da kanta, in kuma za ta sa ne a yi mata shi kenan, abinda dai ake so a yi shi yadda ya kamata.
Duk lokacin da za ta kwanta bacci bayan ta yi alwala sai ta karanta waɗannan ayoyin kamar haka;
1. Aya ta ɗaya zuwa goma cikin suratul Kahf
2. Sai kuma ƙarshen suratul Mu’minun
3. Aya ta 54 zuwa ta 56 a cikin suratul A’araf
Sannan ta karanta wannan addu’ar kamar haka;
“Allahumma inni auzhubika min su’i ahlami, wa’astajiruka min talaubish shaidan fil yaƙzati wal manami”
In kika karantata shi kenan sai ki yi baccinki. In Sha Allah muddin za ki kikayi wannan shawarar ba ki da matsala.
Haɗin Turare
Wannan turare aljani ba ya sonsa, duk inda ka turara aljani ba zai so wajenba In Sha Allah.
Hannit
Lubazzakar
Habbatussaud
Tafarnuwa
Kajiji
Waɗannan su ne za a haɗa su guri ɗaya sai a rinƙa turarawa. In kika yi haka ba ke ba aljanu In Sha Allah.
Daddawar batso
Habbatus sauda
Kajiji
Kustul hindi
Al-mum
Su ma turarawa za ayi da yardar Allah aljani zai bar jikin mutum da kuma gida.
Sannan za a samu ruwa mai kyau, an fi son na zam-zam in ba a samu ba sai a yi amfani da ruwan rijiya ko kuma ruwan sama, ya zamo dai ruwan mai tsafta ne. Sai a yi alwala a nemi za’afaran mansa ko kuma garinsa sannan a samu ma’ul wardi sai kuma jan muski kaɗan sai kuma a samu ganyen magarya a niƙa shi a zuba kaɗan a ciki sannan a karanta wannan ayoyin kamar haka kowacce ƙafa bakwai ana yi ana tofawa cikin ruwa ko kuma numfashin na sauka cikin ruwan.
Ga ayoyin kamar haka;
Suratul Fatiha
Suratul Baƙarah aya ta 1-5
Suratul Baƙarah aya ta 101-102
Suratul Baƙarah aya ta 255-256
Ƙarshen Suratul Baƙarah aya ta 273-277
Suratul A’araf aya ta 54-56
Suratul Yunus aya ta 90-92
Suratul Isra’i aya ta 109-111
Suratul Mu’minun aya ta 113-118
Suratul Kahfi aya ta 1-10
Suratul Saffat aya ta 1-11
Suratul Mulk
Suratul Jinn
Suratul buruj aya ta 1-3
Suratul Kafirun
Suratul Ikhlas
Suratul Falaƙ
Suratul Nas
Waɗannan ayoyin su za a karanta a tofa a cikin ruwan sai a ba wa mara lafiya tasha da safe kafin ta ce komai, ta shafe kanta da ruwan kaɗan, sai kuma da daddare kafin ta kwanta bacci ya zama shi ne ƙarshen abin da za ta sha ta kuma shafe jikinta gaba ɗaya.
Sannan waɗannan ayoyin za a karanta su kamar yadda suke, a samo mayuka kamar haka;
Man habba
Man kwakwa
Man alayyadi
Man zaitun
Jan Muski (ɗan kaɗan)
Man ridi
A haɗe su wuri guda a karanta waɗannan ayoyin a tofa a ciki ta rinƙa shafawa a jikinta musamman in za ta kwanta bacci. Duk irin taurin kai da aljani yake da shi to zai bar jikinsa da yardar Allah.
Domin karanta cikakken bayani akan
Hanyar Ƙona Aljani Ajikin Mutum danna koren rubutu.
Domin karanta bayani akan
Addu’a A Lokacin Da Mutum Ya Fitinu Da Wasuwasi A Cikin Sallah danna koren rubutu.
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu