Manufofin Waƙafi

0
341

Ana yin waƙafi saboda cimma manufofin ne guda biyu, waɗanda kuma suka yi rassa masu ɗumbin yawa, waɗannnan manufofi guda biyu su ne:

1. Manufofi na addini

Waƙafi babbar alama ce na ƙarfin imanin wanda ya yi shi; da kwaɗayin da yake da shi na aikata alheri da kyautatawa ‘yan’uwansa.

Ta hanyar waƙafi musulmi zai sami damar riskar abubuwan da zai iya rasawa na ladan aikata alheri, bayan ya bar duniya.

Samun ladan bin umarnin Ma’ aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi; wanda wannan ba shakka manufa ce babba.

A cikin waƙafi da mutum ya yi wa ‘yan uwansa, akwai ladan sadar da zumunci.

Haka kuma, a cikin waƙafi akwai ladan taimako bisa aikin alheri da kyautatawa; kamar yadda Allah maɗaukakin Sarki ya yi umarni a cikin Alƙur’ ani mai girma.

2. Manufofin Kyautata Zamantakewa A Tsakanin Mutane:

Amfanar da al’ umma tare da magance matsalolinsu ta hanyar sadaukar da wani abin amfani a gare su.

Magance matsalar nan ta taskace dukiya a hannun waɗansu ‘yan tsirari daga cikin al’umma da faɗaɗa amfaninta.

Magance matsalar ajiye kadara tsawon lokaci ba tare da an amfana da ita ba.

Haka nan waƙafi hanya ce ta samar da ayyukan yi ga mutane masu yawa; waɗanda za a ɗauka aiki don yin hidima ga ayyukan waƙafin da sauransu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Rukunan Waƙafi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tattalin Arziki A Nijeriya danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceDangogin Waƙafi
Labarin na GabaTaƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci