Babban abinda Ɗan Adam ya kamata ya fahimta a cikin wannan rayuwa ta duniya shi ne, dukkanin samun nasarar mutum duniyarsa da lahirarsa, ya dogara ne akan fahimtarsa da abubuwan guda shida(6) idan ya fahimce su kuma ya yi aiki da su yadda ya dace, haƙiƙa ya yi nasara, kuma ya samu dukkanin arziƙin duniya da lahira baki ɗaya.Waɗannan abubuwa guda shida(6) su ne uku na ɓangaren ubangijinsa, mahalicci sauran ukun kuma sun shafi ɓangaren Iblis wato Sheɗan, maƙiyinsa.
1. Ɓangaren ubangijinka mahalicci su ne, ka yi iyakar ƙoƙarinka ka san Allah ubangijinka, ka ba shi matsayinsa na ubangiji maɗaukaki, ka sani ba shi da abokin tarayya, ya fi kowa ƙarfi, ya fi kowa sanin ka, ya fi kowa sonka, ya fi kowa ƙaunarka, kuma ya fi kowa sanin halin da kake ciki, kuma babu abinda yake gagarar sa. Kada ka shiga cikin waɗanda ba su ƙaddara ubangiji gwargwadon matsayinsa ba.
2. Ka nemi sanin yadda ya tsara yake so ka tafi a cikin rayuwarka domin ka bi wannan hanyar, domin ita wannan hanyar ita ce za ka bi ka samu ribar wannan rayuwa ta duniya da kuma samun tukwuici na shiga gidan aljanna ranar gobe alƙiyama.
3. Ka nemi sanin abubuwan alkhairi da arziki wanda ya tanada a cikin aljanna domin waɗanda suka bi shi, suka yi masa biyayya suka bi umarninsa a nan duniya. Haƙiƙa duk wanda Allah ya taimake shi ya fahimci waɗannan abubuwa, kuma ya yi imani, da aiki da su, to haƙiƙa ya sami dukkan nasara ta rayuwar duniya da lahira, ya kuma samu haƙiƙanin Imani da Allah ubangiji mahalicci.
Waɗannan da su ne ake samun dukkan nasara a nan duniya da kuma babban rabo a ranar gobe alƙiyama.
Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane da Iblis Wato Sheɗan
1. Ka san waye Sheɗan Iblis, ka san menene matsayinsa a wurinka, menene matsayinka a wurinsa.
2. Ka san waɗanne hanyoyi ne Sheɗan Iblis ya tsara waɗanda zai bi domin ya halakar da kai domin ya sa ka bijirewa Allah ubangijinka mahalicci domin ya haɗa ka da shi a cikin wutar jahannama ranar alƙiyama.
3. Ka san wace irin azaba da uƙuba Allah ya tanada ga Sheɗan Iblis da waɗanda suka bi shi a nan duniya. Duk yawan karatun da ka yi a duniya, waɗannan abubuwa guda shida(6) kawai ake so ka fahimta, komai tarin karatunka waɗannan su ne abubuwan da ake so ka sani domin saduwa da Allah lafiya, da kuma samun rahamarsa.
Duk wanda Allah ya taimake shi ya gane waɗannan abubuwa guda shida, kuma ya rayu a kansu, tabbas ya gama arziƙin duniya da lahira. Alhamdulillah.
Za Mu Ɗora A Mako Mai Zuwa, Insha Allah.
Danna nan don karanta nauye-nauyen rayuwar aure
Edita; Rumasa’u M. Kallamu