MAGANIN DAMUWA
Wani bincike da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar a farkon wannan shekarar 2020, ya tabbatar da cewa kimanin mutane miliyan 264 a duniya suna fama da cutar damuwa. Kuma kusan mutane dubu 800 ne suke mutuwa ko su kashe kansu a kowace shekara saboda damuwa.
Damuwa cuta ce ta ƙwaƙwalwa, wacce take haifar da matsanancin baƙin ciki da ɓacin rai da fargaba da rashin jin daɗin rayuwa da amincewa kowa.
Wanda ya kamu da wannan cuta sai ya rasa abin da zai yi, ya ji daɗin rayuwarsa, wannan ne ya sa wasu suke kashe kansu wai don su huta.
Babban abin da yake haifar da damuwa shi ne, baƙin ciki kan abin da ya wuce da wanda ake ciki da kuma fargaba da tsoron abin da ake zaton zai faru nan gaba. Wato In mutum ya tara wa kansa ɓacin ran jiya ya haɗa da na yau, ga kuma tunanin gobe ma haka za a tashi, to dukkanin rukunan cutar damuwa sun tabbata ga mutum.
A Musulunci babu wata cuta da ba ta magani, sai mutuwa. Kuma maganin Musulumci kan kowane irin ciwo shi ne kat kuma kaifiyya.
Musulunci zai ba ka riga-kafi,ya bayyana maka dalilan da suke jawo ciwo da maganinsa da kuma yadda za a yi amfani da shi a warke da iznin Allah.
Ga waɗansu taƙaitattun bayanai da za su taimaka wajen magance damuwa da ɓacin rai Insha Allahu.
DALILAN DAMUWA DA MAGANINTA
1.RASHIN GODIYAR ALLAH TA’ALA DA WADATAR ZUCI
Sau da yawa In mutum ya rasa wani abu da yake da shi, ko kuma bai samu abin da yake so ba, sai ya mance da duk wata ni’ima da Allah ya yi masa, ya rinka jin shi rayuwarsa ba ta wani amfani. Wani ma abin da yake so ɗin ba ya cikin lalurar rayuwa, kuma babu rufin asirin da bai samu ba, amma duk da haka, sai ya damu kansa da ƙunci saboda bai samu yadda ransa yake so ba.
Maganin wannan shi ne, mutum ya gode wa Allah bisa ni’imomin da ya yi masa waɗanda ba za su ƙirgu ba, ya rinka duban na ƙasa da shi, kada ya rinƙa hangen na sama da shi.
Wannan zai haifar wa mutum wadatar zuci da samun gamsuwa da yanayin da ake ciki
.
2.RASHIN YARDA DA HUKUNCIN ALLAH TA’ALA
Allah Ta’ala shi ne mai iko a kan komai, shi ne mai yin yadda ya so, a lokacin da ya so ga wanda ya so,ta yadda ya so. Rashin yarda da haka yakan jefa mutum cikin damuwa marar iyaka.
Maganin wannan shi ne cikakkiyar yarda da amincewa da dukkanin hukuncin da Allah ya ƙaddara kanka ko ga waninka koda kuwa ba haka kai kake so ba, saboda shi Allah Taala ba a sa shi, ba a hana shi, ba a ce masa ga yadda zai yi, kuma ba a tashin hukuncinsa.
3.KANGAREWA KA’IDOJIN RAYUWA
Allah Ta’ala ya tsara rayuwar duniya kan waɗansu dokoki da tsare-tsare waɗanda a kansu take tafiya.
Duk wanda ya bi wadannan dokoki zai zauna lafiya ya ji daɗin rayuwarsa, wanda kuwa ya ƙi bin su, zai gamu da damuwa da tsaki a rayuwarsa.
Misalin waɗannan ka’idoji sun haɗa:
_Allah ba ya kawo canji sai mutum/mutane sun canja salon rayuwarsu.
_Duk abin da ka aikata sakamakonsa zai dawo maka.
_Wanda ya dage ya yi ƙoƙari, shi ne zai samu nasara.
_Zalunci sama da ƙasa shi ne yake ruguza al’umma.
_Allah bai yi mutane iri ɗaya ba, kowa da halinsa da yanayinsa, sai kowa ya tsaya iya matsayinsa.
_Kowane wuri akwai hanyar shigarsa.
Rashin fahimtar waɗannan ka’idoji da aiki da su, yana haifar da matsananciyar damuwa da ci baya a rayuwa.
4.SABON ALLAH TA’ALA
Sabo ko zunubi shi ne karya dokokin Allah Ta’ala wanda ya haɗa da shiga haƙƙoƙin Allah da na bayinsa.
Ƙin bin umarnin Allah da bauta masa kamar yadda ya yi umarni, da aikata abubuwan da ya hana ,da zaluntar mutane da tauye musu hakkokinsu, shi ne babban abin da yake haifar da ɓacin rai da damuwa. Saboda duk wanda ya hana wani barci, tabbas shi ma ba zai yi barci ba, ko ya yi sai dai da ido ɗaya.
Saboda bin Allah Ta’ala da bai wa kowa haƙƙinsa shi ne babban maganin damuwa.
5.CIN HARAM DA ALMUBAZZARANCI
Bin hanyoyin ya ki halal ya ki haram, da son tara abin duniya ta kowane hali, da shirme da almubazzaranci da dukiya koda ta halal ce, shi ne musabbabin faɗawar mutane da dama cikin damuwa da baƙin ciki da ɓacin rai.
Maganin wannan shi ne mutum ya zage damtse ya nemi halal kuma a yi amfani da abinda aka samu ta hanyar da dace ba kauro ba ɓarna.
6.FIDDA RAI
Fidda rai daga samun sauƙi da canji daga Allah Ta’ala, babban zunubi ne kuma yana jawo matsananciyar damuwa da ɓacin rai.
Ya wajaba ga duk wanda yake cikin wani hali na damuwa, ya cika zuciyarsa da kyakkyawan fata da zaton samun sauƙi da yayewar duk wani ƙunci da tashin hankali. Kuma mutum ya rabu da tsoro da fargabar abin da bai zo ba, saboda mai tsoron rashin lafiya ya fi kamuwa da ita, haka mai tsoron talauci yakan zama abokin kut da kut ga talauci.
7.CAMFI
Canji yana jefa mutane cikin damuwa. Misali camfa wata sana’a ko mace ko wurin zama wannan zunubi ne babba, kuma yana jawo damuwa da.gurɓata rayuwa.
In dai mutum yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to lallai ne ya dogara ga Allah Ta’ala ya yi fatali da camfe-camfe da shashanci.
8.SHA’AWAR HARAM
Sha’awar lalata ta maza ko mata tana jefa mai yinta cikin damuwa, musamman idan bai samu damar cimma burinsa ba, In kuma ya samu, ba zai taɓa gamsuwa ba, saboda jini ba ya maganin ƙishirwa, haka dai za a yi ta rayuwa cikin damuwa da ɓacin rai.
maganin wannan shi ne jin tsoron Allah da kaucewa duk wani kallo da tunani da abota da ƙawance na haram.
9.TSANANIN SON ABIN DUNIYA DA DOGON BURI
Wannan ma yana haifar da damuwa da sanya a bi kowacce hanya domin samun wannan ba kuma lallai ne a samu ba.
Maganin wannan shi ne taƙaita buri da baya-baya da duniya.
10.HASSADA
Hassada ciwo ne babba kuma zunubi ne mai girma, wanda yake hana mai yinta sakat a rayuwa.
Maganin wannan shi ne a guji hassada a wanke zuciya.
11.ZALUNCI
Mutum ya yi zalunci, ko a zalunce shi yana haifar da damuwa.
Maganin wannan adalci da hakuri.
12.TALAUCI
Yana jawo babbar damuwa, kamar yadda kowa ya sani.
babban maganin sa shi ne haƙuri da dagewa wajen neman halal da wadatar zuci.
Insha Allahu a rubutu na gaba zan kawo hanyoyin samun sauƙin musibu.
Allah Ta’ala ya yaye mana dukkan damuwar duniya da lahira. AMEEN