Lissafi Akwai Zaƙi

0
55

Fati

Assalamu alaikum yara.

Shin ko kun san cewa lissafi, wato Mathematics,  wani abu ne mai daɗin gaske?  Kuma idan ka iya za ka gane cewa yana da sauƙi. Kawai dai ɗan lokaci za ka ba da ka yi ya bita, sai ka ɗanƊani zumar lissafi.

Daɗin daɗawa lissafi ilimi ne na yau da kullum. Misali- kullum sai an raba muku abu a gida. Wannan sai da lissafi. Idan kin je yawin sallah kin dawo za ki zo ki ƙirga kuɗin da kika samu. Wannan sai da lissafi. Baban ku zai ce tela ya gwada ku domin ɗinkin kayan salla. Wannan ma sai da lissafi. Idan Abban ki zai gina muku sabon gida sai an yi gwaje-gwaje da yawa. Duka wannan sai da lissafi. Ashe ko yara kun ga ilimin Math yana da matuƙar anfani. Ba abun mu guje shi ba ne. Kawai za mu ba da ɗan lokaci ne sannan kuma mu daina tsoro.

Sai mun haɗu a gaba

Domin karanta Yunƙurin Hausantar Da Kimiyya Da fasaha danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAddu’ar Wanda Ya Ji Tsoron Zaluncin Wani Mai Iko
Labarin na GabaTarihin Kafuwar Ƙasar Qatar