Lallai Ne Shugaba Ya Nemi Yardar Allah Shi Kaɗai

0
11

An karɓo daga wani mutumin Madina ya ce: “Ma’awiyya ya rubutawa Aisha (Radiyallahu Anha) wasiƙa ya ce: “Ki rubuto min wata wasiyya amma a taƙaice”. Sai ta ba shi amsa da cewa: “Assalamu alaika, bayan haka haƙiƙa na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Wanda ya nemi yardar Allah da aikata abinda zai sa mutane su yi fushi da shi, Allah zai isar masa da wahalar mutane.

Kuma wanda ya nemi yardar mutane da aikata abinda zai jawo masa fushin Allah, sai Allah ya ƙyale shi da mutanen. Ka huta lafiya.

Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi da lafazin: “Wanda ya nemi yardar Allah da aikata abinda zai jawo masa fushin mutane, sai Allah ya yarda da shi, kuma ya sa mutane da su yarda da shi. Wanda ya nemi yardar mutane da aikata abinda zai jawo masa fushin Allah, Allah zai yi fushi da shi, kuma ya sa mutane su yi fushi da shi.

ƘARIN BAYANI

Ya zama wajibi a kan duk wani mai jagoranci ya zartar da hukunci na gaskiya wanda ya dace da dokokin Allah koda kuwa ɗaukar wannan matakin zai fusata mabiya ko kuma waɗansu daga cikinsu. In dai ya yi haka da kyakkyawar niyya to zai samu yardar Allah da falalarsa da taimakonsa kuma zai buɗa tunanin mabiyansa su fahimce shi su yarda da shi.

Idan kuwa ya kasance ƙoƙarin shugaba shi ne ya farantawa mabiyansa ya yi musu duk abinda suke so, koda kuwa wannan abun ya saɓawa gaskiya da dokokin Allah to haƙiƙa zai gamu da fushin Allah da azabarsa, kuma daga ƙarshe sai su waɗanda yake ƙoƙarin farantawa ɗin sun juya masa ba ya sun yi fushi da su.

Saboda haka, duk wani ƙuduri ko mataki da shugaba zai ɗauka ya kasance na gaskiya ne kuma ya yi shi da kyakkyawar niyya sannan kuma ya kasance tare da hikima da tausasawa, kada ya damu da sai ya farantawa kowa, wannan ba zai haifar masa da wani alhairi ba a wurin Allah da kuma wurin su kansu mabiyan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisai Na Ƙarya Da Raunana A Kan Ashura danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceZikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala