Labari Mai Taken Ina Za Mu Je!

0
21

Ina za mu je, ina ake so mu je? Gidajenmu sun zama tamkar ƙaburbura, Makarantunmu sun zama wuraren da ake farautar rayukanmu. Ya ke uwa Najeriyarmu, ina za mu je? Don samun mafaka wanda ta wuce bayan ki.

Bayan mun ci abinci mun sha ruwa, muna latse-latsen waya, kwatsam! Sai ga Laure ta shigo cikin falo a firgice, tana cewa: “Anti, zuciyata ta kasa samun sukuni, a lokacin da na ji labarin da ya faru da ni, ya sake faruwa da wasu ‘yan mata har ashirin da biyar (25) a Jihar Kebbi. A lokacin da labarin ya iske ni, sai na ji komai ya dawo min sabo, na shiga ɗimuwa, hankalina ya ɗugunzuma.

Innalillahi wa’inna Ilaihi raji’un! Shin rayuwar da muka yi a sansanin da a ka kai mu, lokacin da aka sace mu, irin ta waɗannan ‘yan mata za su yi?” Da labarin fitowar su ya riske ni, na yaba da ƙoƙarin masu juya sitiyarin mulkin ƙasar mu, sai dai ya kamata a ce, an mayar da hankali a kan matsala tun kafin afkuwarta, a yi tsayin daka wajen daƙile matsala kafin faruwarta.

A samar da tsaro mai ɗorewa, don ina gudun kar abin da ya faru da Laure, ya sake maimaituwa ga ‘yan mata masu ƙananun shekaru irin ta. Wacece ke, me ya faru da ke? Tambayar da na yi wa Laure kenan don jin ƙarshen labarinta. Ta kada baki ta ce:

“Anti, na kasance ɗaya daga cikin ‘yan matan Chibok, waɗanda ‘yan bindiga suka raba su da ahalinsu, suka rusa duk wani buri na rayuwarsu, suka mayar da gonakinmu mafakarsu, ta gudanar da dukkan tsiya da wasali.

An killace mu a wani sansani, wadda ake gudanar da rayuwa tamkar rayuwar dabbobi, babu tausayi ko imani a zuƙatansu. An min fyaɗe a wannan waje, wanda ya kasance na samu juna ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Kaico! na yi ɓarin ciki har sau uku.

A karo na ƙarshe ne na haifi yarinya ta, wanda ni kaina ban san haƙiƙanin wanene mahaifinta ba, domin a rana na kan samu zaratan maza da suke keta min haddi sama da mutum uku. A lokacin da nake renon cikinta, na haɗu da ibtila’i iri-iri, daga ni har jaririyar cikina mun sha uƙuba, sai dai alƙawarin Allah tabbatacce ne, to wannan ne ya sa yarinyar ta rayu.

A lokacin da nake naƙuda, na yi matuƙar tausayawa kaina da abin dake cikina domin irin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da mu ka tsinci kai ciki daga ni har jaririyar. Na yi doguwar naƙuda, wanda har wani ya ɗana bindigarsa zai harbe ni, don haka suke yi idan irina ta kasa haihuwa da wuri, sai su harbe ta su cilla ta cikin daji abin su.

Shugaban runduna ne ya ba da umarnin a ƙyale ni, wanda ban san dalilin hakan ba, sai dai na fi tunanin kwana na ne kawai bai ƙare ba. Haka na yi ta fama, jini ya ɓalle min, a haka har Allah ya yi ikonsa na haihu. Babban tashin hankali na shi ne, yadda na haɗu da ciwon yoyan fitsari.

Innalillahi wa’inna Ilaihi raji’un! Haka na yi ta fama, wadda ta kai har sauran ‘yan uwana waɗanda aka sato mu tare, sun fara ƙyama ta, saboda yadda nake zarni ga ƙarnin jego, har ta kai ga na fara wani irin wari, tsutsa ta fara bayyana a gefanni na, wanda ni kaina abin ya fara damuna, har na fara burin mutuwa.

Yarinyar da na haifa ciwon shawarar yara ya kama ta, idonta ya mata rawaya-rawaya (yalo shar), ga ba ishashen ruwan nono, domin ni ma ban samu isashshen abincin da zan kai baki na ba bare na samu ruwan nonon da zan shayar da ita, har ta kai na fara addu’a Allah ya sa mu mutu, domin ina ganin da wannan rayuwar ai gara mutuwa, wataƙila ita ce hutu a gare mu.

Anti kina ji na, a cikin ‘yan uwana da aka sato mu tare, akwai wata wadda ɗaya daga cikin ‘yan ta’adar yake ji da ita, to, da taimakon ta ne, nake samun ruwan zafin da nake gasa jikina, da wani magani wanda ban tantance sunansa ba, sai kuma ɗan abincin da nake sawa a bakin salati. Cikin ikon Allah sai yoyon fitsarin ya tsaya daga nan ne na fara jin ɗan dama-dama wanda har yanzu ina fama da ciwon sanyi, kuma har yanzu ban warke ba.

A cikin wannan tashin hankali muka ci gaba da rayuwa, wasu an kashe su, wasu kuma an gurɓata musu rayuwa. Ni yanzu babban tashin hankalina shi ne, idan yarinyata ta kai munzalin girma, wane jawabi zan mata har ta gamsu, a kan wanene mahaifinta? Saboda yanzu na cire ƙauna da yin wata kyakkyawar rayuwa don an gurɓata min ita gaba ɗaya.

Anti, kin san me, dukkan abubuwan nan da suka faru da ni, a lokacin ban wuce yar shekara goma sha huɗu zuwa biyar ba (14-15), a yanzu haka ban san ina ne makomar rayuwata ba.”

Na yi kasaƙe, ina sauraronta, ban san lokacin da ƙwalla ke fita daga idanuwa na ba. Ke duniya, ina za mu je, ina ake so mu je! Ya ku al’umma ku gane!

Dukkan al’ummar da ta tozartar da rayuwar ‘ya’ya mata, wannan al’umma ta kama hanyar tozarci da ƙasƙanci a rayuwa ta gaba.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken INA ZA MU JE! wadda Na’ima Sulaiman Dakayyawa (Oum Fatayat) ta wallafa, wadda aka gabatar a Taron Ranar Marubuta Ta Duniya na ranar (31/12/2025) a Dutsen Jihar Jigawa.

Danna nan don karanta Ya Ake Sanin Kai?

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceLabari Mai Taken Tsatsar Zuciya
Labarin na GabaRawar Da Ƙirƙirarrar Basira Ke Takawa Wajen Ƙarfafa Tsaro Da Bunkasa Tattalin Arziki
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.