Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana kuka a cikin sallah don tsoron Allah, kuma yana kuka yayin sauraron karatun Alkur’ani daga waninsa, kamar Abdullahi dan Mas’ud, Allah ya yarda da shi.
Kuma Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kuka domin tausayin wani abu, kamar yadda ya yi kuka don tausayin rasa ɗansa Ibrahim da rasa jikarsa wacce ‘yarsa Zainab ta Haifa.
haka zalika, kukan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne, idanuwansa su yi hawaye, su kuma zubar da hawayen, idan kuwa kukansa ya tsananta sai aji yana shassheƙa kamar yanayin tafasar tukunya, kuma Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya kwarma ihu a dalilin kuka.
Domin karanta cikakken bayani a kan Dariyar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi, wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.