An ƙaddamar da fassarar Sahihul Bukhari daga harshen Larabci zuwa Hausa a mujalladi shida, wani gagarumin aiki da Alƙali Imam Ahmad Zaruqu Idris Kabara, ɗan asalin Jihar Kano, ya gudanar.
An gudanar da taron ƙaddamar da littafin a ranar Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, a Jami’ar Bayero, Kano.
Wannan aiki na da matuƙar muhimmanci ga harshen Hausa da duniyar ilimin Musulunci, kasancewarsa fassarar Sahihul Bukhari zuwa Hausa da aka bayyana a matsayin ta farko a duniya da mutum guda ya gudanar da ita gaba ɗaya.
GAME DA MARUBUCIN
Alƙali Imam Ahmad Zaruqu Idris Kabara an haife shi a magaribar jinjirin watan Ramadan na shekarar 1375H, wato 1956, a unguwar Kurna Maɗatai, Kano, Najeriya.
Mahaifinsa shi ne Sheikh Idris ɗan Almustapha, wanda nasabarsa ta kai ga Sheikh Abdur-Rahman Zaiti, wanda aka bayyana cewa ya kafa Shari’ar Musulunci a Kano a tsakanin shekarun 1349–1385 Miladiyya.
Mahaifiyarsa kuwa ita ce Faɗimatul Alawiyya, ‘yar Sheikh Muhammadu Nasir, wadda nasabarta ta kai ga Nana Faɗimatuz Zahra’u (RA), ‘yar Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).
KARATUNSA DA NEMAN ILIMI
Alƙali Imam Ahmad Zaruqu Idris Kabara ya fara neman ilimi a hannun mahaifiyarsa. Daga bisani ya karanci Alƙur’ani, Ashamawiy, Arba’una Hadith da Muwadda Malik a hannun mahaifinsa da kakansa, Sheikh Dr. Muhammad Nasir Kabara.
Ya kuma yi karatu a Jami’atul Rasuuli daga 1992 zuwa 1996, tare da samun ilimin zamani a Ma’ahadud Diyani Gwale da Shahuci Judicial School, sannan ya samu Diploma in Shari’a and Civil Law.
A fannin Hadisi, ya bayyana cewa ya samu karatun Sahihul Bukhari daga Sheikh Muhammad Nasir Kabara, kuma isnadin karatun daga Imam Bukhari zuwa gare shi ya ƙunshi malamai 23.
AIKINSA DA HIDIMARSA
Ya shafe shekaru yana hidima a fannin ilimi da shari’a. Ya fara aikin koyarwa daga 1974 zuwa 1976, sannan ya yi aiki a matsayin Maga Takarda daga 1979 zuwa 1985.
Daga 1985 zuwa 1993 ya yi aiki a matsayin Alƙali, sannan daga 1993 zuwa 2000 ya zama Babban Alƙali.
Daga 2001 zuwa 2008, ya yi aiki a matsayin Babban Shugaban Masu Duba Alƙalai na Jihar Kano, sannan daga 2008 zuwa 2009 ya zama Mataimakin Darakta a Ma’aikatar Shari’a.
GUDUMMAWARSA GA ILIMI
Alƙali Imam Ahmad Zaruqu Idris Kabara ya rubuta littattafai sama da goma, ciki har da wannan gagarumar fassarar Sahihul Bukhari zuwa harshen Hausa a mujalladi shida.
A shekarar 2012, ya kafa Makarantar Daru Ilimil Hadith da ke Kurna Maɗatai, Kano.
Tun shekarar 1992, ya kasance Halifan Sheikh Muhammad Nasir Kabara a karatun Sahihul Bukhari a gidan Qadiriyya Kabara, sannan ya zama Limamin Juma’a a shekarar 2012.
ABIN DA AKA CE A WAJEN ƘADDAMARWA
A wajen taron ƙaddamar da littafin, Farfesa Matabuli Shehu Kabara ya yi bayani kan tarihin aikin fassarar da yadda aka gaji wannan tafarki daga marigayi Sheikh Muhammad Nasir Kabara.
Mai bitar littafin, Dr. Shehu Kabara, ya yaba da ƙwarewar marubucin, musamman yadda ya fassara wurare masu sarƙaƙiya ta hanyar amfani da tsohuwar Hausa da sabuwar Hausa, domin kiyaye armashi da asalin harshen Hausa.
Haka kuma, Farfesa Haruna Musa da Farfesa Umar Sani Fagge sun yaba tare da taya marubucin murnar wannan gagarumin aiki.
Uban taron kuma Shugaban Ɗarikar Qadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara, ya yaba da aikin, tare da jan hankalin malamai kan muhimmancin kasancewa kusa da al’umma domin bunƙasa addini, ilimi da tarbiyya.
ZURIYYARSA
Alƙali Imam Ahmad Zaruqu Idris Kabara yana da ‘ya’ya 19 — maza 9 da mata 10.
Mazansa su ne: Nasir, Mujtaba (Allah ya jikansa), Idris, Muslim, Mukhtarul Kunti, Aliyul Hauwwas, Bukhari, Shehil Fatih da Usman.
Matan kuma su ne: Asiya, Hauwa’u, Shema’u, Rabi’atu, Atika, Batulu, Lalla Rahama, Sa’adatu, Ummu Aimana da Faɗima.
Kammala fassarar Sahihul Bukhari zuwa harshen Hausa a mujalladi shida babban abin alfahari ne ga Kano, Hausawa da harshen Hausa, tare da ƙara samar da wata muhimmiyar kafa ga masu karatu domin fahimtar Hadisan Manzon Allah (SAW) cikin harshensu.
Wannan aiki ya haɗa hidimar addini, bunƙasa ilimi da adana martabar harshen Hausa, kuma zai iya zama wata muhimmiyar taska ga al’ummomi masu zuwa.
Masha Allah, Tabarakallah.
Allah Ya saka wa Alƙali Imam Ahmad Zaruqu Idris Kabara da alkhairi, Ya sanya wannan aiki cikin ma’aunin kyawawan ayyukansa, Ya ƙara masa lafiya, ilimi da albarka, Ya kuma albarkaci zuriyarsa.
Amin.










