Kakannin Manzon Allah (Saw)

0
59

Nasabar manzon Allah sallahu Alaihi wa sallama tana tiƙewa har zuwa ga Annabi Ibrahim Hikimar Ubangiji ta ƙaddara cewa shi Annabi Ibrahim wanda  shi ne kakan Annabawan Bani Isra’ila, kuma shi ne dai zai zama kakan Annabi Muhammadu Balarabe daga tsatson Annabi Isma’il.

Haka kuma duk da cewa Annabi Ibrahim ya girma ya tashi a Lardin Iraqi amma sai bisa hikimarsa ya kimsa wa Annabi Ibrahim ɗin ya yi ƙaura zuwa Falasɗin a can ya ajiye matarsa Sara sannan kuma ya tafi da Hajara tare da jaririnta Isma’il zuwa gurin da a yau ake cewa da shi garin Makkah.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Ruku’u danna nan.

A lokacin da Annabi Ibrahim ya ke tafiya da su (Hajara da jaririnta) bai san takamaimai inda zai zaunar da su ba, tafiya kawai yake yi a bisa umarnin Allah, har sai da ya zo bigire wanda babu ruwa, babu tsiro a nan Allah ya yi wa Annabi Ibrahim wahayi cewa a nan ne inda zai ajiye matarsa da jaririnta.

Babu shakka a nan akwai jarrabawa ta ubangiji ga Annabi Ibrahim wadda ta nuna mana juriya da haƙuri da kuma biyyaya na Annabi Ibrahim ga Mahaliccinsa Allah (swt) saboda ya sami haihuwa a lokacin da ya girma don haka ya yi matuƙar murna da samun wannna haihuwa amma a lokacin kuma aka umarce shi da ɗauke su (iyalansa) ya kai su can wani guri mai nisa ya ajiye a gurin da babu kowa ya koma Falasɗinu ya bar su a nan!

Ita ma Hajara ta nuna biyayya ga mijinta kuma ta miƙa wuya ga umarnin Allah mahiliccinta, saboda a lokacin da Annabi Ibrahim ya ajiye ta tare da jaririnta ya juya zai bar su sai Nana Hajara ta ce da shi, “Yaya za ka bar mu a nan wajen mu mu kadai kuma ka tafi kabar mu? Shin ubangiji ne ya umarce ka da aikata haka?” Sai Annabi Ibrahim ya ce,  “Haka ne”.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

Sai Nana Hajara ta ce, “To je ka, tunda Allah ne ya umarce ka, haƙiƙa ba zai taɓar da mu ba”. Nana Hajara a nan ta nuna tsantsar biyayya da miƙa wuya.

Annabi Ibrahim bai bar su haka ba sai ya yi addu’a ta musamman:-

ربنا إنى أسكنت من ذريتى بواد غير ذى زرع عند بيتك المحرم، ربنا ليقيموا الصلاة فاجعل أفئدة من الناس تهوي إليهم وارزقهم من الثمرات لعلهم يشكرون

“Ya Ubangijinmu ga shi na ajiye zuri’ata a wani kwari wanda babu wata shuka a cikinsa a inda ɗakinka mai alfarma yake, (nayi haka ne) ya Allah domin su tsayar da sallah, to (ina roƙon ka) ka karkato da zukatan mutane i zuwa gare su, kuma ka arzurta su da kayan abinci (ɗiyan itatuwa) domin su zama masu yin godiya”. Daga nan ne asalin samuwar garin Makka ya faro.

Larabawan Yaman sun yi hijira daga lardinsu sai suka zo inda Nana Hajara take a tare da jaririnta Annabi Isma’il sai suka nemi izininta domin su maƙotance ta saboda sun ga akwai ruwa (zam-zam) a inda take. Waɗannan Larabawa na Yaman, ana cewa da su ƙabilar Jurhum, su ne suka assasa garin makkah, kuma a cikinsu Annabi Isma’il ya tashi har daga bisani ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴansu kuma daga gare su ne, aka haifar da kakannin Manzon Allah (SAW)

Dukkanin kakannin Manzon Allah (SAW) inganttun mutane ne masu martaba da karamci da yin alheri ga mutane.

Wani muhimmin abin lura game da nagarta da Allah ya dasa a tsatson Manzon Allah, shi ne kakansa Annabi Ibrahim wanda ya tabbata mai nagarta, da ƙarfin Imani, tare da saurin miƙa wuya, ga umarnin Allah, haka shima ɗansa Annabi Isama’il wanda ya ci jarabawa a lokacin da mahaifinsa Annabi Ibrahim ya yi mafarki yana yanka shi, nan take Annabi Isma’il ya miƙa wuya ga umarnin Allah, ya yi biyayya ga mahaifinsa, ya ce, “Ya yarda a yanka shi”. A lokacin ne kuma Allah ya kuɓutar da shi daga yanka, to, haka kuma sauran kakannin Manzon Allah har zuwa mahaifinsa Abdullahi dukkansu Allah ya sanya su managarta ne su.

Wani abin lura kuma game da hikimar Ubangiji a tarihin Annabi Ibrahim shi ne, yadda Allah ya kimsa masa ɗauke Hajara da jaririnta zuwa yankin Makka, sai gashi wannan ne sanadin a haifi Manzon Allah a cikin Larabawa, daga jinin Annabi Ibrahim wanda sauran ƴaƴansu kuma su ne Annabawan Bani Isra’ila.

Haka kuma ya faru ne saboda matar Annabi Ibrahim ta farko Nana Sara ita a yankin Falasɗinu ta zauna, kuma ita ce ta haifi Annabi Ishaq shi kuma ya haifi Yakubu, wanda shi ne kakan Banu Israila saboda haka Annabi Ibrahim ya zama shi ne kakan Annabawan Bani isra’ila kuma shi ne kakan Annabi Muhammad wanda shi kuma Balarabe ne (saw).

Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin “Bita A Cikin Tarihin Shugaban Halitta” Domin karanta cikakken littafin ko daukoshi  danna nan.

labarin da ya wuceYadda Namiji Zai Bi Wajen Zaɓen Mace Tagari
Labarin na GabaHaihuwar Manzon Allah (Saw)