Littafin Mace Mutum na Rahma A. Majid na magana ne kan danne haƙƙin mata da akan yi, musamman na daga abin da ya shafi al`adar Bahaushe. Marubuciyar ta ma fara ne da shimfiɗa labarin littafin da nuna yadda talauci kan jefa mafi yawa daga cikin mata su shiga harkar barace-barace, bayan sun sha wahala ko dai ta aure, wanda ya ƙi daɗi, ko kuma wadda ake yi a gargajiya.
Ginin labarin ya fara daga ƙauye, yadda Fatima wadda aka fi sani da Godiya ke ba da labarin yadda rayuwa ke gudana a ƙauyensu, na yadda mazauna ƙauyen ke fama da rashin wayewar kai, da kuma irin yadda al’adun ƙauyen suka kasance na ko-in- kula dangane da abin da ya shafi mata gaba ɗaya, ga abin da take cewa:
‘Ta ɓangaren karatu dai mu mata babu ruwanmu, aure kawai muke jira.’
Godiya dai ta ci gaba da nuna mana cewa su dai matan wannan ƙauyen ba su da wata ƙima ko daraja da suke da ita, domin duk wani aiki mata ke yi, kuma babu ruwan su da wani karatu, kuma don duhun jahilci, ko su mazan karatun addini kawai ake tura su gabas su yi, shi kuwa karatun zamani, suna samun labarin cewa ne kawai duk wanda ya yi zurfi cikinsa, to ya fantsama ne cikin duhun kafirci.
Hasali ma, mutanen wannan ƙauyen ba su da wata alaƙa da mutanen birni, balle ma har su sami wata yarda ko aminta da wannan ilmin zamani da suke jin labarinsa, wanda na kafirci ne, sannan tsakaninsu da birnin ma tafiya ce mai tsawo, domin mota ma ba ta zuwa daga kasuwa sai kasuwa ta garin wadda ke ci mako- mako suke ganin mota. A taƙaice dai Godiya a nan tana ƙoƙarin nuna yadda jahilci, da duhun kai da kuma talauci ya yi wa mutanen ƙauyensu katutu.
A haka dai rayuwa ta ci gaba a wannan ƙauyen, ta yadda har aka yi wani baƙon malami daga Nijeriya (wannan labarin ya faro ne daga wani ƙauye a Jamhuriyar Nijar), inda babansu Godiya ya yi wa wannan malamin kyautar Lami wato yayar Godiya. Duk dai a nan wurin mun ga yadda ita Lami ke yi wa ƙanwarta huɗubar kada ta bari a yi mata irin yadda aka yi mata, domin ta nuna irin yadda mata ke rayuwar bauta yayin da aka yi masu aure, musamman wanda ba su so.
Kuma a haka Alaramma ya ɗauki amaryarsa, aka kuma ba su Godiya domin ta je ta zauna da amarya a can Nijeriya. A can Nijeriya kuma Lami ta je ta faɗa wa kishin kishiyoyi, domin Alaramma na da mata biyu, a haka kuma jininta ya shaƙu da na wadda Alaramma bai cika so a gidan ba, wannan duk sai suka taru suka sa wa Lami da `yar zamanta baƙin jini a gidan.
Bayan zaman doya da manja da ake yi, da cikin da matan malam biyu suka samu, ciki kuwa har da Lami, kwatsam sai ga malam ya ƙara yin aure, wanda wannan ya ƙara tayar da hayaniya a gidan. Su kuma masu cikin, sai aka yi ta ƙoƙarin ɗura masu rubutun sha, yayin da Lami ta nemi a kai ta asibiti kuwa, ta ji abin da ba ta yi tsammani ba, domin kuwa ta ji cewar ko matar Maigari ma sai idan haihuwar ta zo mata da gardama sannan ake kai ta wurin unguwarzoma, ita ko ga ta matar malam tana maganar asibiti.
A haka dai haihuwa ta zo wa Yaya Indo, bayan ta yi kwana huɗu tana yin naƙuda ta haihu, amma ɗan bai zo da rai ba, ita kuma wadda ta haihu jini ya ƙi tsaya mata, aka ɗauke ta aka kai wani asibitin ƙauye, an nemi jinin da za a ƙara mata, amma duk wanda aka gwada cikin waɗanda suka kai ta asibitin su ma suna neman ƙarin jini, a haka dai matar malam ta mutu.
Ita ma yayar Godiya da ta fara naƙudar, amma ta zo da gardama sai aka yi mata yankan gishiri, wanda wannan ya jefa ta cikin mawuyacin hali, wanda ya sanya dole sai an kai ta birni don yin tiyata, ta mutu a birnin, amma da suka dawo ba a gaya wa Godiya ba, sai daga baya malam ya ce su shirya a kai ta gida, bayan zuwansu ƙauyensu ne ta fahimci cewar Lami ta mutu.
A ƙauyensu ɗin ta sake ganin wannan malamar asibitin wadda ta ke zuwa ƙauyensu malam tana ba su magunguna, wato malama Zubaida, ta yi mata bayanin duk abin da ya faru, sannan ta nemi da ta tafi da ita, domin ta ji ana cewa ita za a mayar wa malam, amma ta rarrashe ta, daga ƙarshe dai da maganar auren Godiya da malam ta tsananta, sai ita Godiya ta ɗauki shawarar da yayarta mai mutuwa ta ba ta, na ta gudu ta bar ƙauyensu.
Ta gudu ɗin, kuma kamar arashi, sai direban malama Zubaida ya tsince ta ya kai ta wurin malama, wadda dama ta yi ta roƙon da ta gudu da ita. Daga ƙarshe dai ganin Godiya za ta shiga wani hali, tun da ta sha alwashi ko da malamar ba ta tafi da ita ba za ta gudu, malamar ta aminta za ta tafi da ita ɗin, amma bisa sharaɗin cewa bayan ta gama makaranta za ta dawo ƙauyensu, wato lokacin da ta san ciwon kanta, kuma lokacin da ba wata barazana da wani zai yi mata.
Rayuwar Godiya, wadda yanzu sunanta ya dawo Fati a birni ya shiga cikin wani sabon salo, domin kuwa ta san yadda rayuwa take gudana a birni, ta shiga makaranta, har ya kai ga ta yi jarabawar JAMB domin samun ci gaba da karatu, a cikin wannan halin ne malama Zubaida ta nemi haɗa auren ɗanta Bashir da Fati, saboda ta lura ɗan nata na neman shiga cikin rayuwar Fati ɗin, shi kuma ya nemi jajircewa.
A dai haka Fati ta samu shiga jami`ar Abuja, yayin da shirye-shiryen aurenta da Bashir ya kankama, amma malama ta ce sai an je ƙauyensu Godiya an bayyana musu. Sun dai je ƙauyensu Godiya ɗin an kuma iske abubuwa da dama sun faru, wasu masu daɗin ji, wasu kuma akasin haka.
Bayan dawowarsu gida Nijeriya an ɗaura auren Bashir da kuma Fati (Godiya), amma dai a tsaitsaye, domin ga alama dai Bashir ba ya son auren, ita kuma Fati ta fara karatunta a lokacin. Kuma har zuwa lokacin da ta gama bautar ƙasa abubuwa tsakaninta da mijinta ba su sauya ba, a haka dai ta haƙura.
Sun zauna tsawon lokaci har zuwa sadda malama Zubaida ta rasu, abubuwa dai ba su sauya ba, kuma saboda tsananin halin da Fati ta shiga tsakaninta da mijinta, ya sanya har ta yarda da abokin mijinta suka rinƙa tarayya a lokacin da mijin nata yake Abuja da amaryar da ya aura. Auren Bashir da Fati ya zo ƙarshe lokacin da ya gane suna yin lalata, ita da abokinsa lauya, bayan ya sake ta, ta nemi lauya ya aure ta shi kuma ya turje da nuna cewa idan ya aure ta Bashir zai samu damar nuna wa duniya cewar dama mazinata ne.
Bayan ƙin auren ta da lauya ya yi, Fati ta ƙara shiga cikin wani ƙangin na gaba-kura-baya-sayaki na yadda za ta tafiyar da rayuwarta, a haka dai ta yanke shawarar barin gidan da lauya ya kama mata, ta tafi Sakkwato wurin wata Hajiya Hassana wadda ta sani. A Sakkwato bayan jin labarinta da Hajiya ta yi, ta tausaya mata, ta kuma ba ta wurin zama, sannan kuma ta nemar mata aiki a makaranatar kwamfuta ta mata da wata tsohuwar kwamishiniya ta buɗe a garin Sakkwato, amma daga bisani aka bar koyarwar, sai dai shiga yanar gizo.
Tsaron da take yi a wurin ne ya sa ta samu wani basarake ya nemi auren ta, ta dai amince an yi auren, daga baya take ji a wurin wannan basaraken cewa wai malamin duba ne ya ce za su haɗu, kuma su yi aure saboda shi haihuwa yake nema don ya samu mai gadonsa. Bayan auren ta da basarake an yi soyayya, kuma ta ga kula har take tunanin cewa ko ramuwa ce na soyayyar da ba ta gani ba a baya, har zuwa lokacin da ta samu ciki, har ya kai ga haihuwa, amma abin da ya ɓata harkar shi ne da ta haifi mace, wannan haihuwa ta mace da ta yi kusan ita ta wargaza jin daɗinta da kuma soyayyar da ta gani a baya.
Zama bai ga Fati ba domin an yi zargin cewa ma cikin ba na Ciroma ba ne, domin dai bai nan ya yi tafiya, bayan ya dawo aka ce tana da ciki, wannan shi ya sanya ta sake yin hijira ta bar Sakkwato, ta nufi Kano bisa hanyarta ta zuwa Legas. Ta isa Legas cikin jirgin ƙasa, kuma ta faɗa hannun innar ‘yan Arewa wato Inna Yaya mai sai da abinci, inda ta kasance mai ba da tikiti idan an ci abinci, amma zama bai yi tsawo ba, domin da uwar ɗakinta ta haɗa ta da wani don ya zama farkanta, ita kuma ta ƙi, sai ta fatattake ta.
Ita kuma ta koma Zango, gidan wata Mai alkubus, inda ta zauna kuma har daga baya ma ta buɗe wurin karantar da yara, amma nan ma ba da daɗewa ba ta wargaje, sai daga baya aka samar mata tuƙa tuwo a wani gidan sai da abinci, kuma daga fara aikinta a wannan gidan tuwon ba da daɗewa ba wani ciwo ya taso mata a gabanta, wanda likitoci suka ce sai an yi mata tiyata, su kuma ba su da waɗannan kuɗin, wannan ciwon dai shi ne ya yi ajalin Godiya, ta rasu ta bar ɗiyarta guda ɗaya Amina.
Ɗiyar da Fati ta bari wato Amina ta ci gaba da rayuwa a hannun Mai alkubus, har zuwa lokacin da rikicin ƙabilanci ya kaure, Aminar na makaranta yayin da ta dawo gida sai ta iske an fasa gidan nasu, wannan shi ya yi sanadiyar komawarta hannun wata wai ita yaya Bilki, ita ta ci gaba da rainon ta a Legas ɗin har zuwa lokacin da ta gama makaranta. Ta bar wurin mama Bilki saboda ta ƙi yi mata tallar ruwa, daga baya ta haɗu da wasu matasan `yan jami`a, mace da namiji waɗanda suka tafi da ita gidansu na gado suka ci gaba da zama.
Daga baya dai Amina ta sake haɗuwa da Mai alkubus, kuma ta samu gurbin karatu a jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Amina dai ta gama jami`ar Ahmadu Bello, bayan abubuwa da dama da suka faru. A ciki ta yi karatu tuƙuru, ta kuma ƙi jinin da ƙaunar duk wani ɗa namiji bisa dalilinta na rashin tausai da riƙon amana. Ta yi ƙawaye `yan birni daga ciki har da Ummi, wadda daga baya saurayin Ummin ya dawo wa Amina bisa dalilinsa na cewa Ummin ba `yar goyo ba ce, wannan kuma ya haifar da rigingimu, iri-iri, amma dai duk da haka ta gama karatunta na likitanci da sakamako mai kyau. Sannan daga ƙarshe ta auri Abbas, wanda shi ne tsohon saurayin Ummi.
A dunƙule, dai bayan auren Amina da Abbas rayuwa ta yi daɗi, kuma Amina ta ƙaddamar da shirinta na neman `yancin mata wanda shi ne ƙashin bayan littafin.
Jigo A Littafin Mace Mutum
Kai tsaye duk wanda ya fara karanta wannan littafin zai san jigonsa neman haƙƙin mata ne. Duk da akwai ƙananan jigogi, amma dai wannan jigon shi ne kan gaba. A farkon buɗe littafin maganar babban jigon ce ta fara fitowa fili inda wata `yar kare haƙƙin mata ta rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga wata ƙungiya mai iƙirarin kare matan mai suna HATTARA! CI DA GUMIN MATA !
Sannan idan muka kalli irin wahalhalun da marubuciyar ta ce Godiya (wato mahaifiyar Amina) ta sha, a wurare da dama, an nuna yadda maza ke tauye haƙƙin mata ne. Dubi rayuwarta ta farko a ƙauyensu, sannan lokacin da ta dawo birni irin yadda Bashir ya yi faman neman ɓata rayuwarta kafin daga baya mahaifiyarsa ta tilasta masa auren Fatimar.
Haka ma ko bayan auren an nuna irin azabar da ta yi ta sha, har zuwa lokacin da ta auri basarake a Sakkwato, nan ma duk an nuna yadda aka danne haƙƙinta, kai a cikin littafin, a rayuwar Godiya kaf, an nuna cewa ta rayu cikin bautar maza, har zuwa lokacin da ta mutu, ɗiyarta ta karɓa.
Jigon dai ya fara fitowa fili ne lokacin da Abbas ya nemi ta amince su yi aure, wato lokacin da take labarta masa irin wahalar da mahaifiyarta ta sha a hannun maza, ta ce:
‘… don haka ba na son maza, don ba sa son mu. Ba su son mata, amma sun ƙi fitowa fili su nuna mana ba sa son mu, ba don komi ba sai don imaninsu da cewa mu ba mutane ba ne, don haka ba za mu fahimci ƙiyayya ba. Yaudarar mu nishaɗi ce… ? Yaudararmu sana’a ce, mai riba. Yaudararmu kamar halaccin lallashin dabbar da ake son a kama ne domin a yanka a ci namanta…. Suna zuba mana kayan kwaɗayi, sai mun shagala, muna ci kamar dabbobi, sai mu ji harbi.
Wasu sun mayar da mu karnukan farauta. Mu suke tasawa a gaba wajen kamo `yan uwanmu a gabanmu su wulaƙanta. Su auri mai mutunci, ba don su yi mutunci ba, sai domin ta renar masu mutuncin gidansu, su suna waje suna yaga mutuncin `yar uwarta. Wasu suna mana wayo, sun ce sun sakar mana wuya, mu sha ruwa, bayan sun sakar mana tarko a ƙafa, suna talla da mu, mu ne sana`ar da ke ciyar da su, ta shayar da su, amma ba mu sani ba, muna zaton su ke ba mu abin da muke ba su. Muna zaton mu ke dogara da su, ashe su ke dogara da mu. Sun sanya mu mun fi dabba dabbanci’.
A nan wurin duk abin da Amina take nunawa bai wuce irin abin nan da Bahaushe ke cewa na an ci moriyar ganga, an ya da kwaurenta ba, domin duk abin da take cewa bai wuce rashin nuna yarda da namiji ba, ko kuma irin yadda maza ke amfana da mata, amma a koma a rinƙa cewa mata ba su da amfani, ko kuma a yaudare su, ko wani abu makamancin haka.
Jigon littafin bai fito fili sosai ba sai lokacin da Amina ta zama cikakkiyar mace, lokacin da ta gogu da boko, lokacin da suka kafa ƙungiyarsu ta fitattun mata a arewa, kuma lokacin da suka tashi tsaye don neman `yancin mata, ga abin da suke cewa:
‘… Ba gasa muke ba… Ba hassada muke ba. Haƙƙinmu muke nema. Amma ba za mu samu ba, sai mafi akasarin mata sun san suna da haƙƙin da aka danne masu. To ta yaya za mu yi haka in ba da ilmi da ilimantarwa ba ? Ke nan ashe ilmi ne kan gaba a harkarmu.’
Kai tsaye mun fahimci cewar `yancin mata kawai suke son ƙwatowa daga danne shi da ake yi. Kamar yadda muka ce akwai ƙananan jigogin da suka tallafa wa fitowar babban jigon, kamar jigon soyayya da jigon haƙuri da sauran su.
Salo A Littafin Mace Mutum
Salon littafin duk da cewar mai sauƙi ne, amma yana da ɗan ruɗarwa, domin kuwa an yi amfani da wani salon kwan-gaba-kwan-baya daga farkon littafin domin fara nuna inda aka dosa, da yake dama so ake a yaƙi danne haƙƙin mata, sai aka ɗauko salon buɗe littafin da yadda mata da sauran mabarata suka cika garuruwan ƙasar Hausa. Sannan Hausar da aka yi amfani da ita mai sauƙin ganewa ce, ga karin maganganu da aka yi amfani da su bila haddin.
Wani salon kuma da ya bambanta wannan littafin da wasu littatafai shi ne yadda a sashi na biyu na littafin sai aka nuna cewa kamar Amina ta gama karanta labarin mahaifiyarta ne ga mai karatu, ba shakka wannan wani salo ne wanda ba duka marubuta ke amfani da shi. Haka kuma an yi amfani da kalamai da lafuzza masu sauƙi da daɗin fahimta. Kuma an yi amfani da salon fara rayuwa daga ƙauye zuwa birni.
Naɗewa
A wannan babin an yi nazarin littattafai guda huɗu; Rabin Raina da So Jinin Jiki da Ina Son Sa Haka da kuma littafin Mace Mutum ta fuskar jigo da salo domin fito da wancan fasalin na adabin Kasuwar Kano da muka gani.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Domin karanta Sharhin Littafin Ina Son Sa Haka danna nan
Edita@rumasau-kallamu