khairatu.shehu
Kowacce cuta tana da magani, kuma kowace matsala tana da mafita, don haka mafita ga wannan mummunan hali da muka shiga ya zama wajibi a kanmu mu yi tunanin samar da hanyoyin da za a iya bi don rage ko ma kawar da wannan matsala baki daya, tunda illolin shaye-shayen kayan maye yana shafar al’umma ne baki ɗaya.
Don haka yaƙi da su wani alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, wato sai an yi taron dangi, kowa sai ya ba da tasa gudummawar daga kan gwamnati da hukumomin suke kula da hana fatauci da kuma shan miyagun ƙwayoyi da ƙungiyoyi da kafafen yaɗa labarai da malaman makarantu na addini da na boko da iyaye da mariƙa da yayye da ‘yan uwa da abokan arziƙi da su kansu matasa maza da mata da kuma sauran jama’ar gari.
Ya zama wajibi a yi duk abin da za a yi wajen tabbatar da ganin an yi nasarar shawo kan wannan mummunar ɗabi’a, don abin ya fi ƙarfin mutum ɗaya ko hukuma ita kaɗai, abin ya zama tamkar kan ɗaki sai an taru. A nan, za a yi bayanin ire-iren matakai da gudummuwoyin da kowa zai iya bayarwa kamar haka:
Matasa Maza da Mata
1. Matasa su lura sosai da ire-iren abokan da za su yi abota ko ƙawance da su.
2. Ya kamata ko ma ya zama wajibi matasa su lura da ire- iren masoyan da za su yi soyayya da su, domin shiga soyayya da mashayi ko mashayiya yana iya haifar da koyon wannan mummanar harka ta shan ƙwayoyi da abubuwan masu sa maye, musamma tun da soyayya tana da matuƙar tasiri a rayuwar matasa musamman mata, waɗanda suke da raunin zuciya, yanzu-yanzun nan sai a juya musu tunani a sanya su a wata hanya marar kyau.
3. In ba ki fara ko ba ka fara shan kayan maye ba to kada ki soma ko kada ka soma shan su. In kana sha ko kina sha, ka yi ƙoƙari ko ki yi ƙoƙari ki daina shi ne mafi alfanu ga rayuwar kowane matashi ko matashiya; Iyaye su bi hanyoyin lura da irin ƙawaye ko abokai da kuma samarin da ‘ya’yansu suke yin hulɗa da su.
Don a makaranta ana samun miyagun’ abokai maza da mata, kuma in suna yin irin waɗannan shaye-shayen ƙwayoyi sukan koya wa ƙawaye ko abokai ko kuma masoyansu. Saboda haka iyaye su dinga bibiyar lamuran ƙawayen ‘ya’yansu a makaranta ko a gida ko kuma masoyan (samari) da suke tare da su. Yin hakan yana da matuƙar muhimmanci.
Iyaye da Mariƙa
4. Iyaye lallai su ɗauki matakin sanya ido wajen tarbiyyar yara.
5. Su lura wajen sanin halayen matan aure ko zaurawa da ‘ya’yansu suke shiga gidajen su suna yin hulɗa da su. Domin ana samun wasu gidajen matan ko zawarawan suna zama matattarar waɗannan matasa masu irin halayen na shaye-shayen magunguna don su koyi maye, kuma wasu a nan suke koya wa wasu matan ko ‘yan matan; kai har da yara matasa masu shiga gidajen sukan koyi irin wannan harka ta shaye-shaye.
6. Duk lokacin da iyaye suka ga ‘ya’yansu da wani magani na ƙwaya ko na ruwa ne lallai su matsa da tambayar su da bibiyar sanin ko na menene.
7. Iyaye su dinga kai ziyarar ba zata cikin dakunan ‘ya’yansu kuma su dinga bincika jakunkuna da akwatunansu da sauran wuraren da ake tunanin yarinya za ta dinga ɓoye wasu abubuwa da ba ta so a gani.
8. Iyaye su dinga sanya ido a kan lokutan da ‘ya’yansu suke fita daga gida da kuma lokacin da suke dawowa, kada a bar wa yarinya damar ta dinga kulle gida da kanta, domin wannan wata wawakekiyar ƙofa ce ta yarinya ta yi abin da ta ga dama iyaye ba su sani ba.
9. Idan iyaye suka ga ‘ya’yansu ko maza suka ga matansu suna yawan barci babu gaira babu dalili, nan ma su matsa su gano menene yake jawo hakan.
10. Iyaye ko mazaje su dinga yawan kula da kan harshen ‘ya’yansu da kuma matan aurensu. Lokuta da dama masu tsotsar wata ƙwayar kan harshensu yana nuna launin kore ko shuɗi saboda yawan tsotsar ƙwayar da suke yi.
11. Iyaye su guji sanya ‘ya’yansu yin aikin ƙarfi wanda ya fi ƙarfin ‘ya’yan don hakan yana sa su sha ƙwayoyin da za su ji ƙarfin da zai sa su yi aikin da ya fi ƙarfinsu, wanda daga nan in ba a yi saʼa ba sai shan ire-iren waɗannan ƙwayoyin ya zama jiki ga ‘ya’yan.
12. Iyaye su guji cusawa ‘ya’yansu dogon burin da zai sa su neman duniya ido rufe.
13. Su taimaka wa hukuma wajen yaƙi da taʼammali da miyagun ƙwayoyi ta duk hanyar da Allah Ya huwace musu.
14. Ya zama wajibi iyaye su dinga koya wa ‘ya’yansu yadda ake zaɓin miji na gari da zaman aure da kula da miji da abinci da kula da yara da sauransu.
Gwamnati da Hukumomi
15. Gwamnati ta samar wa da matasa aikin yi wanda zai hana su zaman banza da zai shigar da su wasu tunane- tunane da kuma faɗawa cikin wannan harka ta shaye- shaye.
16. Ta dinga shirya tarukan ƙara wa juna sani da yaƙi da wannan harka ta shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
17. Ya kamata hukumomin da suke kula da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA da hukamar kula da ingancin magunguna da abin ci da sha wato NAFDAC su ci gaba da sa ido sosai a kan wannan matsala, sannan kuma su matsa kaimi a kan kantunan sayar da magunguna don a sami raguwar sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma magunguna marasa inganci.
18. Su ci gaba da taimakawa wajen faɗakar da matasan da shan ƙwaya ya zamar musu jiki, ta hanyar kawwame su ɗaɗɗora su a kan tafarki mai kyau.
19. Waɗannan hukumomi in sun kama masu sayar da miyagun ƙwayoyi masu sa maye a daina sakin su a tabbatar an zartar musu da hukunci mai tsanani don wasu nan gaba kada su yi.
20. Masu sayar da miyagun ƙwayoyi su ji tsoron Allah su daina, su sani duk abin da suka aikata akwai ranar sakamako. Ba kawai duniya da abin da za su samu za su duba ba, su dubi Allah da ranar lahira.
21. Gwamnati da hukumomi kowane lokaci a kai a kai su dinga shirya bitoci da kwasa-kwasai ga hukumomin tsaro da kula da shige da fice da hana fatauci da sayar da miyagun kƙwayoyi kuma a samar musu da wadatattun kayan alki kuma na zamani kamar yadda ƙasashen da suka ci gaba suke yi.
Masu Sarautun Gargajiya
22. A matsayin masu riƙe da sarautun gargajiya waɗanda ake girmamawa, kuma suke kusa da al’umma, ya zama wajibi a gare su su riƙe abubuwan da suka saba yi tun da na sa ido da tattara bayanai wanda masu unguwanni da dagatai da hakimai da sarakuna suke yi a cikin al’ummarsu, kuma su isar da shi ga gwamnati.
‘Yan Majalusun Jiha Da Na Tarayya
23. ‘Yan majalisun dokoki na jiha da na tarayya ya zama wajibi gare su su dubi wannan al’amari su samar da dokoki masu tsauri ga mutanen da suke yaɗawa da kuma tallata miyagun ƙwayoyi ga jama’ar su.
Alƙalan Kotunan Jihohi Da Na Yanki Da Kuma Na Tarayya
24. Ya kamata alƙalan kotunan jihohi da na yanki da na tarayyar Nijeriya su daina jan ƙafa wajen zartar wa da masu safara da fatauci da sayar da miyagun ƙwayoyi kai har ma da dillalai da masu jirage na ruwa da na sama da motocin dakon kaya da masu manyan ma’ajiyun kayayyaki wato sito, kotu ta dinga hukunta su ba sani ba sabo.
Kantunan Sayar Da Magunguna
25. Kantunan sayar da magunguna su yi taka tsantsan wajen sayarwa da matasa magunguna barkatai, su dinga bibbiyar dalilan da ya sa matasa suke zuwa sayen magani domin ta yiwu ba an zo saya saboda ba a da lafiya ba ne, sai don a sha a yi maye, a yi mankas. Yin haka zai taimaka mana ƙwarai da gaske wajen rage waɗannan masifu da suke bibiyar mu.
Masu Sayar Da Magunguna A Cikin Baka (Kan Faranti Ko Kwali)
26. Ya zama wajibi masu kantafi da rayukan jama’a a kan baka ko farantai ko kwalaye ko masu baje shi kamar ana sayar da gyaɗa a cikin kasuwa waɗanda ake kira (kyamis ba ƙyaure), su lura da wannan sana’a tasu da yadda take jefa rayuwar al’umma a ciki haɗari marar iyaka, wanda dama gwamnatocin Afrika da duniya baki ɗaya ba su yi naʼam da tsarin wannan sayar da magani a kan titi ba, su dubi Allah su sami matsuguni kuma su sami horo da izini daga hukuma don su yi wannan san’a cikin doka da tsari, kuma su tsira daga fushin Ubangiji.
Masu Magungunan Gargajiya
27. Masu magungunan gargajiya da suke amfani da amsa kuwa (lasifika) su dinga zuga magungunan da suke sayarwa suna maganganum batsa a cikin tallace tallacensu, suna kira ga matasa, kuma matasan suna saya suna amfani da shi ba bisa ƙa’ida ba, ya kamata su daina su kuma sani yin hakan yana tunzura maza da mata suna affakawa ga wata rayuwa da ba ta dace ba musamman ta shaye-shaye, zai fi kyau su sami waje su zauna suna sayar da magungunansu cikin tsari da doka.
28. Haka su ma ‘yan masu ganye, mata masu bin gidajen matan aure, musamman ma masu sayar da magungunan mata, su sani suna haifar da illoli ga matan, domin wasu mata in sun yi amfani da ire-iren waɗannan magunguna yana cutar da rayuwarsu, daga cikin jikinsu da wajen jikinsu da kuma ƙwaƙwalwarsu, tunda an sami misalai da dama na irin ɓarnar da waɗannan magunguna suka yi ga mata, na aure da zawarawa da ‘yan mata, kuma sayar da ire-iren waɗannan magunguna yana haifar da zinace-zinace tsakanin matasa.
Ƙungiyoyi
29. Ƙungiyoyi waɗanda ba na gwamnati ba, wato masu zaman kansu su dinga shirya tarukan ƙarawa juna sani da wayar da kai da kuma yaƙi da waɗannan abubuwa da suka addabe mu, wato shaye-shayen ƙwayoyi masu sa maye, musamman ga mata.
30. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam su daina ɗaure wa masu fatauci da sayar da miyagun ƙwayoyi gindi na cewa an tauye musu haƙƙi ko an ci zarafinsu, domin illolin da suke haifarwa ga al’umma suna da yawa ƙwarai.
31. Ƙungiyoyin sanya ido tsakanin al’umma su dinga nemo matasan da suka faɗa wannan yanayi na shaye-shaye don a kauwame su a saita musu tunani da tafiyar da rayuwarsu, domin gwamnati kawai ba za ta iya yin wannan aiki ita kaɗai ba, sai an yi taron dangi.
Malaman Makarantun Addini
32. Malaman makarantu na addini su ne za su yi jagoranci wajen yaƙi da shaye-shaye ta hanyar yin bayanai a wajen koyarwarsu da wa’azi da nuna illar shan duk wani abu da zai jirkita hankali da kuma irin matsalolin da shaye-shaye suke haddasa wa mutum a rayuwarsa da kuma irin abin da zai haɗu da shi a wajen Ubangiji ranar ƙiyama.
33. A cikin huɗubobin limaman masallatai su dinga sanya wannan batu na shaye-shaye a ciki.
34. Ya kamata makarantu su dinga fito da wasu darusa waɗanda ba sa tsarin koyarwa na jiha ko na tarayya, gyaran ƙafa da farce da ƙunshi sabulu da bambita da kitso da gyaran gashi wanki da guga da ɗinkin hula da kwaɗo da linzami da dafa abinci da sauran su.
Malaman Makarantun Boko
35. A dinga yin addu’a bisa neman kariyar Allah a kan lamuran da suke damun rayuwarmu baki ɗaya, a duk lokacin da aka kammala karatun, makarantar addini.
36. Makarantun boko su dage wajen yaƙi da shaye-shaye ta hanyar sanya ido ga ɗalibansu wajen abubuwan da suke shiga da shi aji na ci ko na sha ko na shaƙawa.
37.Hukumomin makaranta su dinga kai ziyarar ba-zata a ɗakunan kwanan ɗalibai don bincikar kayan maye in akwai su.
38.Ƙungiyar iyayen yara da malamai su dinga aiki tare wajen binciken haɗin gwuiwa a ɗakunan ɗalibai, duka ɓangarorin su dinga sanar da juna ire-iren bayani da suka samu game da yaran a gida ko a makaranta, wannan zai jawo raguwar waɗannan lamura.
39.Su dinga yi wa dalibansu faɗa a game da abubuwan da za su yi amfani da su na sha, su kuma nuna musu kada su yi abota da mutanen banza, don yin abota da mutanen banza yana sa wa a koyi munanan ɗabi’u.
40.Su dinga jawo dalibansu a jikinsu su kuma nuna musu illolin shaye-shaye, ko cewa sai an sha ƙwaya za a yi karatu ko za a iya shiga aji don ɗaukar karatu, sannan su dinga shirya wasannin kwaikwayo da za a yi wani batu na illar shaye- shayen miyagun ƙwayoyi. Kuma a dinga shirya gasa tsakanin ɗalibai ta yin rubutu a kan shaye shaye da illarsu ga rayuwar al’umma.
41.Ya kamata makarantu su dinga fito da wasu darusa waɗanda ba sa tsarin koyarwa na jiha ko na tarayya ba, kamar na ƙananan sana’o’i irin su gyaran waya da ɗaukar hoto da kula da shuke-shuke da sayar da ruwa zobo da kunun zaƙi da kowane irin abubuwan sarrafawa da kuma kayan ƙwalam da maƙulashe kamar nakiya da alkaki da dubulan da fanke da acama da awara da gurasa da dai sauran kayan ciye-ciye da sauransu.
Masu Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi
42.Ya kamata masu sayar da miyagun ƙwayoyi su kwana da sanin cewa akwai hukunce-hukunce masu tsauri da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tana da ga masu wannan mummunar sana’a, don haka su guji fushin hukuma da kuma fushin Ubangiji, domin an ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, don haka kere na yawo zabo na yawo wata rana za a gamu.
Kuma su tuna da rayuwar duniya ba ita kaɗai ce ba akwai ta lahira, duk abin da suka yi na ɓata tarbiyyar al’umma don su sami kuɗi, ranar alƙiyama za su samu sakamakon duk abubuwan da suka aikata na lalata tarbiya da rayuwar jama’arsu.
Kafafen Yaɗa Labarai: Talbijin da Rediyo da kuma Yanar Gizo
43.Ya kamata kafafen yaɗa labarai su dage wajen wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shaye.
Talabijin
Ya kamata gidajen talbijin su dinga tace finafinan da suke nuna wa ta hanyar cire duk wani abu da zai nuna yin amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma tasirinsu, da kuma shirya wasannin kwaikwayo masu nuna illar shan kayan maye.
Rediyo
Zai yi kyau su ma gidajen rediyoyi su dinga sanya ido a kan waƙoƙi da kaɗe-kaɗen da suke sanyawa, musamman na waɗanda aka san sun shahara a fagen shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ko kuma masu nuna a sha kayan maye, don sanya ire-iren waɗannan waƙoƙi suna zama wata barazana ga tarbiyyar da rayuwar matasa. Kuma su dinga shirya wasannin kwaikwayo masu nuna illar shan kayan maye.
Yanar gizo
Ya kamata gwamnati ta sa ido, kuma ta kafa wata hukuma da za ta dinga kula da kafafen sadarwa na yanar Gizo, duk waɗanda aka samu suna yaɗa harkar shaye-shaye, to a toshe su a daina samun su a Nijeriya.
Masu Shirya Finafinai
25 Masu shirya finafinai suna da abubuwan da za su yi a cikin finafinansu masu taimakawa wajen koyar da tarbiyyar matasa ta hanyar sanya wasu abubuwa waɗanda za su yi yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi. Tunda matasan nan, musamma mata suna kallon waɗannan finafinan sosai.
44.Marubuta za su zama a sahun gaba wajen kawo gyara a cikin al’umma ta fuskar rubuce-rubucensu da sanya illoli dan matsaloli da haɗuran da ke cikin shaye-shayen ƙwayoyi masu sa maye.
Sauran Jama’ar Gari
45.Kowane mutum mai hankali da sanin ya kamata zai ƙyamaci wannan mummunar hanya ta shaye-shaye: Don haka sauran jama’ar gari su ma suna da tasu rawa da za su taka ta ƙoƙarin hana wannan sabgar, ta hanyar yin nasiha ko faɗakarwa ga duk wanda suka lura yana son jefa kansa cikin wannan hanya.
46.Ya zama wajibi ga sauran jama’ar gari su ba da tasu gudummawa wajen yaƙi da wannan annoba da ta shigo cikin jama’armu, wato shaye-shayen kayan maye, ta hanyar kafa ƙungiyoyin da za su dinga nusar da matasa su guji wannan abubuwa, sannan kuma su dinga sanar da hukumomi don a dinga kama masu sayar da waɗannan kaya masu sa maye, tun da dama daga cikin masu sayarwar an san su, ‘yan unguwa ne, dole ne a kawar da sani ko sabo don a magance wannan matsala. In ba haka ba kuwa, in an ƙi sharar masallaci za a yi ta rumfar kasuwa. Sannan su kafa ƙungiyoyin tsaro da sa ido a unguwanninsu.
Mawaƙa
47.Mawaƙa ma suna da muhimmiyar rawa da za su taka wajen wannan fafutuka ta yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tun da waƙoƙi suna da matuƙar tasiri ga rayuwar al’umma, musamman ma matasa, tun da suna sauraron waƙoƙin sosai, kuma suna tasiri sosai ga rayuwar su matasan.
Idan muka ɗauki misalin wata waƙa da Ahmad Tijjani Gandu ya yi mai taken ‘Yar Maye, ta yi matuƙar tasiri ga matasa musamman mata yan shaye-shaye, tun da ta sanadiyyar sauraron wannan waƙa wasu sun bar shaye- shayen har abada. A duba rataye na 1 za a ga kaɗan daga cikin abin da wasu baitukan waƙar suke cewa.
Har ila yau akwai wani shahararren mawakin Hausa, marigayi Malam Abdullahi Sani Makarantar Lungu ya taɓa yin wata waƙa ta hani da wannan harka ta shaye-shayen ƙwayoyi masu sa maye, tun ma lamarin bai ɓaci haka ba, domin wannan waƙa an fi shekara goma da yin ta amma ta yi daidai da wannan lokaci da muke ciki. A duba rataye na 2 za a ga baitukan waƙar da kuma abubuwan da ta ƙunsa.
Shi ma shahararren makaɗin kuntigin Alhaji Dr. Danmaraya Jos ya yi waƙa game da hani a kan shan ƙwaya, in an duba a rataye na 3 za a ga abubuwan da ya bayyana.
Fatanmu dai Allah ya tsare mu daga waɗannan munanan ayyuka, ya shiryi zuriyarmu baki ɗaya, amin.
Wassalamun ala manittaba’al huda..
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Don karanta Wasu Alamomin Da Ake Iya Gane Mai Shan Kayan Maye danna nan
Edita@rumasau-kallamu