Hukuncin Kiɗa A Musulunci

0
46

Bukhari ya ruwaito hadisi daga Malik cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce…. “Za a yi wasu mutane daga al’ummata da za su riƙa halatta zina da alharini da giya da kiɗa.”

Lokaci a rayuwar musulmi….. 

An ruwaito sayyidina Abubakar (R.A) na cewa kiɗa na tsirar da munafunci a cikin zuciya. 

Abdullahi bn Mas’ud ya fassara faɗin Ubangiji Maɗaukaki… … “Daga cikin mutane akwai masu sayen yasasshen zance don ya ɓatar a barin hanyar Allah (Madaukaki) da cewa shi ne kiɗa. 

KARTA DA LUDO DA DARA 

Da yawan mutane na buɗe wuraren hira da majalisai musamman bayan dawowa daga kasuwa ko wuraren aiki da yamma. Babbar hanyar ɗebe kewarsu ita ce wassan karta ko ludo ko dara. 

Irin waɗannan mutane kan kwashe awowi masu yawa suna sakaci ana hayaniya, kai ka ce yara ne ƙanana da ba su san lissafin numfashinsu kullum ƙasa yake yi ba. 

Ƴan karta ko `ƴan dara kan cinye dare ba tare da sun ƙosa ba. Kuma mafi yawansu ba sa ware ko minti talatin domin sanin yadda za su bauta wa mahaliccinsu. 

YAWAN HIRA DA ZANTUKA BARKATAI 

Galibin mutane a yau kan yi hirar awowi masu yawa ko musu kan siyasa a majalisai ba tare da fa’ida ba. Yadda wannan na gadarwa da mutum asarar da ba za ta lissafu ba. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHukuncin Kallon Talabijin Da Fina-Finai
Labarin na GabaYin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce