Hiv/Aids Cutar Kanjamau (Sida)

0
66

MA’ANAR CIWON SIDA: Cutar Kanjamau wanda a turance ake kira da Acquired Immunodeficiency syndrome (AIDS) cuta ce me hadari ga rayuwar dan adam wacce kwayar cuta me karya garkuwar jiki da ake kira a turance  da Human Immunodeficiency Virus(HIV) ke kawo ta.

Ita wannan kwayar cuta ta (HIV) na ruguza kariya da jiki ke samarwa daga cututtuka wanda hakan ke ba wa wasu cututtukan daman yi wa jiki illa da wuri.

HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR KANJAMAU

  1. Ana iya kamuwa ta hanyar saduwar da ba’a yi amfani da kwarkwaron roba ba ga Wanda yake dauke da wannan ciwo.
  2. Amfani da abubuwan masu kaifi kamar reza da wuka, kibiya, allura da mai cutar ke amfani dasu.
  3. Bayar da jini mai dauke da cutar sida ga mai buqata.
  4. Ta nonon uwa ga ya/yaro wajen shayarwa.
  5. Haduwar jinin uwa  mai dauke da cutar, dana jariri ko jaririya lokacin haihuwa (transplacental).

Domin karanta Physiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa) Danna nan

ALAMOMIN TA:

Daga alamomin ta akwai

  1. Zazzabi Mara yankewa.
  2. Ciwon kai Mara yankewa.
  3. Ciwon jiki akai-akai.
  4. Kuraje.
  5. Ciwon gabobi.
  6. Zawo.
  7. Gyanbon baki ko na al’aura.
  8. Zufa da daddare.
  9. Ciwon makogwaro.
  10. Kaluluwa mafi akasari a wuya.
  11. Tari Mara yankewa.
  12. Ramewa akai-akai.
  13. Rawar dari Mara yankewa.

Ganin alamomin ta ba ya tabbatar da samuwar ta har sai an tabbatar da hakan ta hanyar gwajin jini.

Yana dakyau ku karanta Physiology da Hausa Kashi na Takwas: Gastrointestinal System(Sashin Sarrafa Abinci)

HANYOYIN KARE KAI
  1. Amfanin da kwarkwaron roba lokacin saduwa.
  2. Kin yin amfani da abubuwa masu kaifi kamar reza ko allura ko jinin da wanda ke dauke da cutar yayi amfani da su.
  3. Kara karfin garkuwar jiki.
  4. Yin gwajin cutar lokaci bayan lokaci.
  5. Takaita abokan saduwa.
  6. Shan magani ga wanda ke dauke da cuta.
  7. Gwajin jini kafin sanyawa mai bukata.
MAGANIN TA

Har yanzu babu wani magani da bincike ya tabbatar da warkewa daga cutar, amma akwai magunna da dama da ke dakusar da haihuwar kwayar cutar.

Hadi da shan magani, cin abinci mai kara karfin garkuwar jiki na da amfani matuka.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Sannan matuqar zaku Sha magani tareda da kiyaye dokoki to tabbas zakuyi rayuwa tamkar kowa.

WASU ABUBUWA NE ZAKA IYAYI TAREDA MAI CUTAR:

Zaku iyayin abubuwa Kar harka ba tareda kasamu wanna cuta ba:-

– Cin abin tare a kwano daya.

– wanka tare

– Wasa tare

– Kwanciya tare da Mai cutar

– Gaisuwa tareda Mai cutar

– Zama guri daya da Mai cutar

– Amfani da cokali daya da Mai. Cutar.

– Amfani da Kofi daya da Mai cutar

TUNATARWA:

Kira ga al’umma duk Wanda/Wadda akasamu da wannan cuta to kar a kyamaceshi, ajashi ajiki, abashi kariya da kulawa sannan kuma da Shawarwari, tareda da kiyaye yaduwar cutar ga al’umma.

SHAWARA:

Aduk lokachi da bawa ya tsinci Kansa da irin wadannan alamomi to Kar yai qasa agwiwa ya ziyarchi asibiti mafi kusa Don yin gwaje-gwaje da Kuma samun gamsasshen bayani dangane da cutar.

Domin karanta bayani akan Matsala Ta Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Daya Danna nan

labarin da ya wuceMatsala Ta Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Daya
Labarin na GabaShin Mutum Na Da Buƙatar Gyara Don Zai Aure