Hanyoyin Ta’ammali Da Kayan Maye

0
7

khairatu.shehu

Hanyoyin sun haɗa da hanyar sha da zuƙa ta baki (smoking) da zuƙa ta hanci (inhalation/sniffing) da yin allura ta jijiya (intravenous/iv injection). Kowaɗanne an ware su gida-gida daki-daki kamar haka:
WAƊANDA AKE SHA TA BAKI

ƙwayoyi na sha ko shan ruwan magani: Ire-iren waɗannan magunguna idan an sha su ba ta hanyar da ya kamata ba, wato aka yi amfani da su ba yadda likita ya ce ba, in dai suna da wasu sinadarai to suna iya bugar da waɗanda suka sha su.

Magungunan Mura Da Tari

Duk wani maganin mura da tari da yake ɗauke da wasu sinadarai da za mu kawo su a nan gaba, in dai aka sha su da yawa yadda ya wuce ƙa’idar da likita ya bayyana, to za a bugu. Waɗannan magunguna mura da tari suna ƙunshe da waɗannan sinadarai: Diphenhydramine da Chlorpheniramine Maleate da kuma Codeine. Akwai kuma shayin gadagi, shi ma ana haɗa shi da wasu ƙwayoyi, bayan itatuwan da ka haɗa aka dafa shayin da su.

Magunguna masu rage zafin ciwo da raɗaɗi irin su codeine da morphine da tramadol da phibine suna iya bugarwa inda suka wuce ƙa’ida.

Misali masu shan waɗannan magunguna na buguwa suna haɗa waɗannan maganguna na mura ko tari da waɗanda suke ƙunshe da sinadarin Chlorampheniramine Maleate sannan su haɗa da wasu ƙwayoyi da ruwan lemo. Sannan suna shan:

  • Kashin Ƙadangare
  • Kashin ɓera
  • Ashana
  • Bula
  • Dagwalon Masana’antu

Giya ta gargajiya ita kuma ta haɗa da: Kokino da Burkutu da Bammi. Sannan akwai Fura mai tsami. Akwai Giya ta zamani wadda kamfanoni suke yin ta, yawanci duk giyar da take ɗauke da sinadarin alcohol in aka sha ta da yawa tana bugarwa. Ana kuma shan ruwan (dafin) kwaɗo bayan an kashe shi.

WAƊANDA AKE ZUƘAR HAYAƘIN TA BAKI (smoking)

  • Tabar wiwi.
  • Kuma ana amfani da kyankyaso a dinga zuƙar hayaƙinsa
  • Shisha da sauransu.

Waɗanda Ake Shaƙa ta Hanci ko Tarbar Warinsu Don a Bugu (inhalation/sniffing)

  • Hodar Iblis (cocaine)
  • Garin tiya gas (tear gas)
  • Garin fankon harsashin bingida
  • Man fetur (petrol)
  • Inhela (inhaler)
  • Sholisho (solvent solution)
  • Madarar sukudayen
  • Ruwan kwatami
  • Tururin masai
  • Ƙasar wajen fitsarin turken doki
  • Ƙasar wajen da mutane suke yin fitsari.

ALLURA TA JIJIYAR JINI (intravenous/iv injection)

  • Allurar hodar Iblis (cocaine)
  • Allurar Pertozocine
  • Allurar Fortwine.

A taƙaice, ƙwayoyin magungunan da akan sha domin sa maye sun ƙunshi ayarin magunguna masu ɗauke da sinadaran Tramadol da Dazapham da Promethazine da Chlorampheniramine da sauransu. Waɗannan sinadarai bayan taimakon da suke da shi a cikin magungunan da suke ɗauke da su, suna da illoli wato, (side effect) na sanya hajijiya ko barci da mutuwar jiki da kasala domin tasirin da suke da shi a bisa ƙwaƙwalwa.

Don haka akan yi amfani da su a cikin waɗannan magunguna gwargwadon adadin da amfaninsu ya zarce illar da suke da su, matuƙar an sha su yadda likita ya ba da umarni. To, a nan ‘yan maye sukan yi amfani da su ta hanyar zarce ƙa’idar yadda ya kamata a yi amfani da su, ta yadda tasirin illarsu za ta bayyana fiye da amfaninsu a jiki.

Misali a yayin da likita ya yi umarni da a sha ƙwayar magani mai ɗauke da waɗannan sinadarai, ƙwaya ɗaya ko ƙwaya biyu rak a rana guda, to ‘yan maye sukan haɗa guda goma ko fiye da haka a lokaci guda. Saboda haka sai waɗannan illoli na sanya hajijiya ko barci da mutuwar jiki da kasala su riɓanya ainun har su kai ga sa maye da gushewar hankali da abubuwan da ke da alaƙa da shi.

Haka nan magunguna na ruwa da akan sha domin sa maye sun ƙunshi ayarin magunguna, musamman na tari, ɗauke da sinadaran Diphenhydramine da Chlorampheniramine Maleate da Promethazine da sauransu.

Waɗannan sinadarai bayan taimakon da suke da shi a cikin magungunan da suke ɗauke da su, suna da illa wato (side effect) ta sanya hajijiya ko barci da wata mutuwar jiki da kasala domin tasirin da suke da shi a bisa ƙwaƙwalwa. Don haka akan yi amfani da su a cikin waɗannan magunguna gwargwadon adadin da amfaninsu ya zarce illar da suka da ita, matuƙar an sha su yadda likita ya ba da umarni.

To a nan ma ‘yan maye sukan yi amfani da su ta hanyar zarce ƙa’idar yadda ya kamata a yi amfani da su ta yadda tasirin illarsu za ta bayyana fiye da amfaninsu a jiki. Misali a yayin da likita ya yi umarni da a sha ruwan magani mai ɗauke da waɗannan sinadarai cikin cokali biyu sau uku a rana guda, ‘yan maye sukan shanye kwalba guda mai ɗauke da cokali kimanin ashirin ko fiye da haka a lokaci guda.

Saboda haka sai waɗannan illoli na sanya hajijiya ko barci da mutuwar jiki da kasala su riɓanya ainun har su kai ga sa maye da gushewar hankali da abubuwan da ke da alaƙa da shi. Har ila yau, duk wani sinadari da za a yi amfani da shi a jikin ɗan Adam ko da ruwa ne, yana da amfani ne kaɗai in an yi amfani da shi bisa ƙa’ida, amma in ya zarce ƙa’ida, hatta ruwa, to zai iya zama illa ga jiki.

Saboda haka masana suke kiran shan duk wani abu mai jirkita hankali ba tare da ƙa’ida ba da suna SUBSTANCE ABUSE! Don haka duk nau’in abubuwan da ake amfani da su don maye za su iya zamowa masu amfani ta wani ɓangaren.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

Domin karanta Wasu Abubuwa Masu Sa Maye danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWasu Abubuwa Masu Sa Maye
Ado Ahmad Gidan Dabino
Shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Najeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni sannan ɗan wasa ne a shirin finafinan Hausa kuma ɗan jarida. Tare da shi aka kafa wasu ƙungoyoyi na marubuta da masu shirya finafinai. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama'a da yake yi a cikin ayyukansa.