Gulma: Shi ne ɗaukar zancen wani mutum zuwa ga wani mutum ba tare da yardar sa ba, don tayar da husuma (faɗa).
Saboda haka, addinin musulunci, addini ne na haɗin kai (zukata), addini ne na zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda yake so ya ga ya haɗa zukatan mutanensa baki ɗaya a duk inda suke a cikin duniya.
Haka kuma Allah (Subhanahu wata’ala) da manzon Sa annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) sun yi mana bayanin sharrin da gulma take iya haifarwa misali kamar su raba kawunan mutane, husuma ko jayayya, munafunci da dai sauran su.
Saboda haka ne ma Allah (Subhanahu wata’ala) ya ja kunnen mu da aikata haka ta harshen annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) kamar yadda ya faɗa;
لا يدخل الجنة نمام. Magulmaci (annamimi) ba zai shiga (gidan) Aljanna ba”.
Saboda haka, ka ga wannan hadisin ya ƙara nuna mana sharrin da gulma take iya haifarwa, saboda za ta iya hana mutum shiga gidan aljanna matuƙar ya mutu a wannan hali na gulmace-gulmace . Haka kuma gulma ko ƙarya ta wani fannin tana da ɗan amfani kaɗan, amma kuma ga wanda yake son ya ga ya haɗa kawunan wasu mutane waɗanda suke gaba da juna.
Misali idan akwai wasu mutane da ba sa jituwa da juna, to ya halatta ko kuma babu laifi akan wani mutum sai ya tashi ya samu wani mutum daga cikin su ya gaya masa magana mai daɗi haɗi da wata kyauta idan yana da hali, sai yace da shi “ga shi abin ka wane ne yace na kawo maka, sa’annan kuma yana gaishe da kai, haka kuma sai ya sake samun ɗayan shi ma ya faɗa masa haka.
Amma kuma a wannan lokacin gulma ta yi ƙaura a tsakanin mata da mata ta koma maza da maza ko maza da mata, wanda a lokutan baya da suka wuce an fi samun mata da gulmace-gulmace irin na su, amma kuma a yanzu haka wai har ma maza su ma suna yin gulmace-gulmace, kai! Hm! Wai faɗuwar girma ne ga raƙumi ya shanye ruwan ɗantsako.
Bugu da ƙari kuma, duk me yin gulma shi ne wanda ba shi da aikin yi, saboda wanda yake da abin yi a gabansa, ba shi da lokacin yin gulmar wani mutum . Saboda haka, gulma ta wani fannin tana da alaƙa da hassada.
saboda idan wani mutum suna faɗa da wani mutum ko kuma wani mutum Allah ya ɗaukaka shi, sai ka ga wani mutum yana faɗar wata magana mara kyau a gare shi, haka kuma sai ka ga yana ɗaukar maganar wani mutum yana faɗawa wani mutum, don ya ga ya haɗa su husuma ko kuma rashin jituwa a tsakanin su.
Haka kum akwai hanyoyin da za a iya magance gulmace-gulmace da dama, misali idan wani mutum ya kawo maka gulman wani mutum, sai ka ƙyale shi har sai ya gama zayyano maka dukkanin zantukan sa, bayan ya gama, sai kawai kace da shi “to ai wannan gulma ce.
Sa’annan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) haɗi da manzon Sa annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) sun hana aikata haka, saboda haka daga yau kada ka sake kawo min irin wannan maganar, sa’annan kuma ka tuba ka daina aikata haka tun kafin ka haɗu da fushin Allah”, da dai sauran su.
Danna nan don karanta hani akan yin gori
Edita; Rumasa’u M. Kallamu