Hadisi Na Huɗu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

0
4

An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba ya tare da mu wanda ba ya tausayawa ƙaraminmu, kuma ba ya girmama babbanmu, kuma ba ya umarni da kyakkyawan aiki, ba ya hani ga mummuna.

Tirmizi ne ya rawaito shi.

ƘARIN BAYANI

Waɗannan hadisai guda biyar suna bayyana falalar tausayawa mabiya da jinƙan su da sauran masu rauni da haramcin gallaza musu, suna nuna cewa duk wanda yake da jinƙai da tausayi Allah zai tausaya masa, kuma rashin tausayi alama ce ta rashin imani da rashin rabo a lahira, har ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Ba ruwansa da maƙetaci mugu maras imani da tausayi da kuma wanda ba ya girmama na gaba da shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Biyar A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)
Labarin na GabaHadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musa